← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 138

Sashe 69

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wani irin dauke wuta Hajiya tayi, bakiɗaya kanta ya shiga juya mata, wani irin lumshe idanu tayi tana ganin duhu yana mamaye mata ilahirin ganinta, kamar daga sama ta tsinci bakinta da faɗin."Alhamdulillahi innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Alhamdulillahi." Ta shiga faɗa da sauri da sauri, amadadin gigita da tashin hankali sai Allah ya saukar mata nutsuwa. Kwalla ne suka cika mata idanu, kafin ta shanye su ta hanyar sakin murmushin da yafi kama da yaƙe. Bata ce musu cikanku ba, ta nufi dakin Maman Maisarah ta ce mata. "Allah ya ƙara miki hakuri, nima yanzu na samu labarin hatsarinsu Amaan." Tana fadar haka ta juya ta bar kofar dakin, a falon kuwa ganin yadda lokaci guda nutsuwa ya dawo mata, ya b'ata ran Tani domin ita so take lallai sai ta ga kukan Sa'adatu, bata kaunar yadda take wani nunawa kamar babu abinda yake damunta. Bayan tasan cikin ranta tana cikin tashin hankali, cikin takaici da bakinciki ta ce mata. "Ikon Allah, ko shima Amaan din ba d'an Mamman Ba'are ba ne?" "Tassss!" Hajiya ta dauke ta da mari, wanda yasa kowa na wurin shiga hankalinshi hatta Nana da take zaune. "Akul ki lalata min nasabar Yarana da Mamman Ba'are, nayi shiru tsawon shekaru talatin da wani abu, ba wai ban iya magana ba ne ko tsayawa kai na ne ba zan iya ba, na zab'i shiru shine mafi alkhairi. Tare da saka ran wata rana zaki gane kuskurenki." Murmushi Hajiya tayi tana faɗin. "Kamar yadda kika san kome akan kowa, nima haka na hana idanuna barci domin nasan wacece ke." Matsawa sosai Hajiya tayi tana mai kasa da murya ta ce mata. "Idanun duniya yana kanki, domin na samu asalin waye Sajjid Mamman Ba'are, tare da labarin kawar da ta kashe kawar.." dabas Tani tayi tana kallon Hajiya baki sake, murmushi Hajiya tayi tana me juyawa bata kuma magana ba, don dama karfin hali take kawai, don ita kaɗai tasan yanayin da take ciki, zuciyarta tayi mata wani nauyi, ji take kamar zata mutu. Salati da taslimi take, tana fita a gigice ta faɗa cikin motar da take jiranta, tana shiga ta dafe goshinta, "wani asibiti suke?" Ta fada da wata irin marayar murya, wanda yake gab da sakin kuka, haka suka nufi asibitin Ba'are hospital. Tunda Hajiya ta shiga asibitin, niman wuri tayi ta zauna tana kallon yadda mutane ke kaiwa da komowa, bakiɗaya basirarta ta tsaya cak, a zahirin gaskiya inda suke ya dace ta nima, amma kuma sai gashi tana kallon kome da idanun zuci, lokaci guda jin ta da ganinta suka tsaya cak.

A can emergency room kuwa, ana ta ƙoƙarin a ceto rayuwar Jamilah Mamman Ba'are, tare da Aryan Mamman Ba'are. Wanda yake kansu kuwa Majid ne, aikin yake da zuciyarshi da rayuwarshi bakiɗaya, wani irin narkewa zuciyarshi take, musamman da yayi ido biyu da yan uwanshi, akwai wani abun da ya bashi mamaki ya aka yi hakan ya faru? Ace Aryan da Amaan da Jamilah sun yi hatsari a lokaci guda, ya aka yi haka ya kasance? Yana gama aikin tare da taimakon wasu likitocin da Nurse, ya fito daga dakin yana zare safar hannunshi, Hajiya ya hango a can gefe zaune. Da sauri ya cire facemask, ya nufe ta da sauri, yana tab'a kafadarta tana tafiya bakiɗaya ta kwanta, "Hajiya!" Ya kira sunanta da karfi, abinda ya ja hankalin mutanen cikin wurin kansu kenan, wasu daga cikin nurse na asibitin da suka san Hajiya, sune suka turo abin daukar mara lafiya ya d'aura ta akai. Kome na kan Majid ya tsaya cak, bai gama fita daga mamakin hatsarinsu Amaan ba, ya kuma katari da sumar Hajiya.
A wannan karon ya gaza taimaka mata, Dr Najib ne ya tsaya akan Hajiya. Bayan ya gama aka turata daya daga cikin dakunan VIP domin yadda jininta ya hau bata son hayaniya bata son ganin duk abinda zai sake d'aga mata hankali. Zama Majid yayi yana kallon yadda ta koma duk saboda su, shi kan bai san inda zai cusa ranshi ba, amma har ga Allah ya gaji da tashin hankalin da yake faruwa a cikin gidansu.
Chapter 69 · 0% Book details