Sashe 96
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Lokacin da muka dawo Niamey, na samu Siyamah tazo don haka na kwantar da hankalina, na sha barcina da na farka na samu tayiwa Amirah wanka da kome, har Amaan yazo ya kaita makaranta. Sai da na kwashe sati biyu kafin na shirya cikin natsuwa da kamala na nufi hanyar office,sai dai koda naje na samu ana ta bata kashi na bala'i akan me yasa Hajiya munafurce shi ta bawa wata aiki. Nan aka yi ta bala'i, Ni kan office din Aryan na wuce na zauna domin sun san da zuwa na. Ina shiga na samu Jamilah sama -sama muka gaisa, na cigaba da wasa da wayata ina temper running.
A fusace Majid ya shigo office din, ya kura min idanu. "me kika zo yi?" Ganin Jamilah a Office din na mike cikin girmamawa, na ce mishi. "Ni ce zan fara aiki a matsayin sakatariyarka." Kura min idanu yayi kafin ya tako gabana. "Nayi miki alkawarin sakawa ki gudu da kafarki." "Allah ya nuna mana." Na fada cikin girmamawa. A fusace ya fita, kallona Jamilah tayi tana faɗin. "Kiyi hakuri, sannan kiyi aikin da Hajiya zata yi alfahari dake, ki tsaya ki cikawa Amaan yardar da yayi dake. Don Allah kada ki bawa wani damar cutar da ahalin da suka yarda dake."
"In sha Allah!" Na fada ina kokarin sunkuyar da kai na, "Hamma Abdul Majid yana da kirki, yana da hakuri idan kika gane kanshi zaku zauna lafiya, rashin kirkin da yake yi na dan lokaci ne, idan aka kwana biyu zai sauko da kanshi."
Jin ta nake, ita ce hala bata san halin shi ba, amma ni nasan wannan dan bala'in ba zai sauko nan kusa ba, mutum kamar wani muzuru, sai yayi ta niman jaraba kamar akan shi aka fara jidali, ai wannan sunan shi dan balaja'u.
Haka tayi ta bani hakuri, har su Amaan da Aryan suka shigo. "Wow kin yi kyau muje na kaiki Office dinki." mikewa nayi muka fito, har Office ɗin Chairman ina bakin kofar office din shi, ina iya hango shi Hajiya tana shafa kanshi, ya lumshe idanunshi, murmushi Aryan yayi yana faɗin. "Kai wannan gayen babu asalin dan takife irinshi, kalli yadda yake wani mashar mashar kaman jikakken zakara." Ai kuwa suka kwashe da dariya.
Haka suka gama shakiyancinsu, sannan suka fita da zasu fita ne Amaan yake gaya min. "Zan turo miki dan larai, bai da matsala amma ki kula domin idan yaji haushi yana faɗin zai daku da mutum ne."
Murmusa mishi nayi tare da faɗin. "In sha Allah ba zamu samu matsala da shi ba." Ya saka kai ya fita, ina murmushi. Can Hajiya ta fito, mikewa nayi tare da gaida ta. "Ina kwana Hajiya." "Lafiya lau Daughter, ina yar jikata." "Tana lafiya." Na fito daga wurin Kujerar na amshi jakarta. "Allah ya miki albarka, ga Majid nan na bar miki amana, sannan ke mace ce tunda kika iya tarbiyyar Yarinya irin Amirah sugrah, har kowa yana son ɗaukarta. Nasan zaki iya tarbiyyarta min da wancan kasungurmin tuzurgwauro....(Anya babu lauje cikin nad'i a Maganar Hajiya......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400 0813269641
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB251
Jikina ne ya dauki rawa, tare da kallonta baki sake. "Zaki iya na sani zaki iya, shi ysa nake jin ki a raina."
"Idan kuma ban iya ba fa? Idan na kasa na fadi fa?"
"Ba zan tab'a zarginki ba, don nasan kin yi ƙoƙari kuma kin yi iya bakin ƙoƙarinki." Hawaye ne ya ciko min,"Kada ki sare ta hanyar zubda hawaye, nasan zaki iya fa." Gyada kai nayi har na rakata, na dawo na zauna ina kallonshi ya juya kujerar shi. Bakiɗaya sai naji na muzanta, haka na zauna yinin ranar babu abinda aka yi, har aka tashi.
Washe gari.
Da wuri na iso aikin, inda na samu ayyuka da uban yawa. Haka na nasa kaina a gaba da taimakon Aryan na rage aikin, sannan da aka tashi ya ga na ciro yar karamar flaks da cooler abinci na fara ci. "Babu tayi ne?" Diba nayi na bashi sauran, muna cikin ci Hamma Amaan ya kawo wasu files zai shiga office din ya hango Aryan yana cin abinci cikin takaici ya ce mishi. "Kai dai kayi girman banza, ajiye mata abincinta." "Sai kayi kuma!" Haka ya lullube Aryan da faɗa, ganinsu tsaye bakiɗaya yasa shi lekowa yana haɗe rai. "Meye haka?" Mikewa nayi ina goge bakina. "Kayi hakuri sir, kana bukatar wani abu ne?" Zuba min idanu yayi kafin ya ce. "Aikin zama ki tara maza kika zo yi?" Fitowa nayi daga inda nake na tafi bakin kofar na tsaya. "Kayi hakuri Sir!" Tsaki yayi ya shige ciki sake baki suka yi, suna kallon na shiga office ɗin, tunda na shiga nake tsaye, bai ce min ga aiki ba, shi bai kore ni ba.
A fusace Amaan ya nufi Office din, "idan baka son tayi aiki da kai yayi kyau, amma batun ka shanyata ai ita mace ce mai rauni. Zaka iya shanya Jamilah ko Anisah, har tsawon mintuna?"
"Ka bar kiran Yan uwana masu kamun kai. Hira tazo yi da maza ko aiki?"
"Ok idan na fahimta mune baka son mu kulata ok that's fine, amma ka sani idan kasan yadda rana ta fito kasan inda zata fadi ne? Kayi kokarin ganin mu'amalar ka da kowa tayi kyau akwai ranar da kana bin kowa don muradinka zasu juya maka baya. Muje Zahra." Girgiza mishi kai nayi tare fa faɗin. "Na gode!" Haka ya ajiye takardun ya fita, shima Aryan ya shigo cikin Yarensu na buzaye yayi mishi magana, banza yayi mishi.
Haka ya fita bai kula ni ba, bai kula kowa ba har aka tashi. Na d'aga kafata na kasa, zama nayi a wurin ina nishi.
B'acin rai da tsanarshi suka kara cika ni, haka ya fita ya bar ni a Office din, Dan Larai ne ya shigo office din kawo abu ya ganni ina kokarin tashi. "Zahra'u lafiya?" Haɗiye yawu nayi nace mishi. "Babu kome taimaka min na tashi." Haka ya riko hannuna na tashi, har na fita na kira driven da yake zirga-zirga da ni, a hankali na isa har wurin shi na shiga. Kuka ne yake taso min, amma naki yi har sai da na isa gida, ina shiga dakina na fada ban daki na fashe da kuka, haka nayita kuka karshe hada sallah nayi bayan na fito, tsanar shi ba zai amfane ni da kome ba. Amma don tsana a duniya babu wanda na tsana irinshi.
A wurin da nayi sallah a wurin nayi barci, sai dare na farka nayi sallar Magariba da Isha, sannan nasha magani da tea na kwanta, Siyamah tana tare da Amira. Haka muka yi ta gwagwarmaya da Majid, cutarwa irinta bakin mugu babu wanda bai sani ba, har ta kai yana iya saka ni nayi ta yawo a kamfanin wai na kai wasu takardu, sai da takai kafafuwa na har wani irin ciwo suke ban tab'a fushi ba, amma ina yawan kuka domin a gaban kowa disgani yake.