Sashe 64
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*031*
"Ni a sanina ban ki shi ba, tunda nice na kawo shi nace ina son shi, ashe don haka ya faru uziri ya dace ayi min ba fushi da b'acin rai ba." Ta fada tana kuka sannan ta cigaba da cewa. "Na amshi kuskure na." Juyawa Zaytoonah tayi ta koma gareta, ta zauna tana me dora mata Baby Zahra a saman cinyarta."Ammy ki daina kuka, don Allah." Ta fada tana jan hancinta. "Dole nayi kuka, yar uwarki ta rasu baku gana ba, mahaifinku ma haka duk laifina ne."
"Bana jin Didi ta rasu, baffanmu kan jikina ya bani baya raye, amma Didi fa ina jinta a raina sosai da sosai."
Rungume su tayi tana faɗin, "duk inda take, tana cikin kariyar Ubangiji, Allah zai shiga lamarinta a ko ina take."
Wato idan har aka samu irin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, zai yi wahala wata fitina ta sauko ba tare da an samu warakar shi ba, tun da suka ji labarin mutuwar Baban Zaytoonah, hankalin kowa ya tashi haka yasa Zaytoonah rikice musu, tare da nisanta kanta da Mahaifinta, duk da kowa yaso mata bayani amma taki fahimta. Haka yasa taje har gaban Sheikh Aliyu Wodabbe, ta ce ita ya mata lamuni zata bar gidan ta tafi neman danginta da suka rage a duniya. Shine ya kira Aminatu da Yafendo da Sumeye, Zaytoonah tana zaune a wurin.
"Na kira ku ne, domin Zaytoon tana son ta tafi neman ahalinta."
Da sauri Ammynta ta d'ago kai tana kallonta cikin wani irin rawan jiki tace mata. "Ba dai tafiya zaki yi ki bar ni ba?" Girgiza kai tayi tana kara faɗin. "Kiyi hakuri nayi laifi wallahi nayi laifi, nasan nayi laifi tunda kike shirin gudu na, don Allah kiyi hakuri. Amma kada ki tafi kiyi hakuri na had'aki da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama."
Kwalla ne masu zafi suka shiga zubo mata, tana kallon yadda mahaifiyarta take kuka da dukkanin zuciyarta, mikewa tayi ta bar wurin, haka yasa Yafendo bin ta dakin. Kuka ta saka tana kara jin zafin Ammyn har Hamma tasa ya roke ta, duk shirin da suke da Hamma sai da ta mishi rashin mutunci, amma yanzu ta zauna tana mata wani kuka mara hujja. "Idan kin shirya ki gaya min, akwai kanwata da muke Yayan mata a Yola, tana aure a can idan kika tafi zasu tayaki niman sauran danginki. Amma kafin nan bari na gaya miki wani abu. Da ace Allah bai nufa an ga Aminatu da wuri ba, ta wuce wani wurin da lalurar gushewar hankali ga kuma cikinki, tow kuwa ba makawa bamu san abinda zai faru ba, imma da tun lokacin kin mutu ke da ita, ki godewa Allah tunda har kika taso an tab'a miki gorin yar mahaukaciya? Tow hauka tuburan Aminatu tayi, da ta warke kuwa ko da wasa bata kaunar ka tambaye ta, bayanta ki godewa Allah da mari kika sha a duk lokacin da kika tambayi bayanta. Saka ran mahaifinki zai biyo sawunta yasa Malam dakatar da ita har na tsawon shekaru Domin tsakaninki da yar Uwarki, tazarar me yawa ce. Ba zance kiyi hakuri ba domin an zalunce ki, amma a matsayina na mahaifiyar Aminatu dole na kare mutuncinta da rayuwarta, tana kuka ne don ta rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwarta, sannan tana shirin rasa ki a karo na uku. Ke baki jin tsoron kukan da take yi wata rana yarki ta saka ki?"
Da sauri ta d'ago kai tana kallon yafendo bakinta yana rawa ta ce. "Yafendo!" "Mahaifiya ce ita, bai dace a saka ta kuka har haka ba, hakan zai tab'a rayuwarta da lafiyarta."
Daga haka ta bar dakin, har ta kai bakin kofar ta ce. "Ba fata nayi miki ba, kina da damar yin fushi da kuka da fada, da ihu amma ki sani itama an mata uzuri domin ba laifinta ba ne, haka Allah ya shirya lamarinshi da ace mutum yasan abinda goben shi zata bayar da zai gyara wanda yake ganin ya dace da shi, ki yi hakuri na baki hakuri ne a matsayina na mahaifiyar Aminatu. Ba a matsayin kakarki ba ki dauka a wani wurin aka miki kuskure to ina mai kara baki hakuri." Daga haka ta bar dakin, tabbas Yafendo ta tsayawa yarta at least ta nunawa Jikarta itama tana son Yarta, ba zata sake damuwa ya cutar mata da Aminatu ba, kamar yadda tana ji tana gani aka hanata akan Yar uwar Aminatu.
Wannan abubuwan yasa Zaytoonah, hakuri da mata uzuri, amma bakiɗaya bata jin dadin rayuwarta. "Ammyn ina son tafiya Nijar na cigaba da karatu a can!" Ta fada tana kallon Ammynta. "Indai haka zai saka ki farinciki na amince, zan kira Dadah na gaya mata, sai ki tafi can Allah yasa haka shine mafi alkhairi."
"Amin Ammyna, in sha Allah zan binciko mana inda Didi take." Inji Zaytoonah. "A'a kada ki wahalar da kanki, in sha Allah zata zo gare mu." Cikin shashekar kuka ta ce mata. "Muma dole mu neme ta, ba zamu jira sai tazo ba." "Hmmm kin dai ce tana raye ne, amma yadda nasan rigimar su da mutanen garin nan zai yi wahala idan bata mutu ba."
"Wallahi tana raye tana raye na rantse da Allah." Haka suka yi ta kuka a tsakaninsu. Har bayan an sha ruwa Malam ya kirasu ya musu nasiha da addu'ar idan Zahra tana raye Allah ya bayyanata, idan ta mutu Allah ya mata rahama."
Haka suka yi ta addu'a, sannan suka tashi. Duk da dai zuciyoyinsu babu dad'i amma kuma haka bai hana su sakin ransu ba, domin kuwa kowa yana jin ciwon abin da ya faru. Musamman Ammyn gani take kamar da wata a kasa, haka kawai ba zata samu lalurar gushewar hankali ba, sannan daga baya, taji kamar zata mutu idan aka tambaye ta, me ya faru ko ina mijinta yake.
Wannan abin ya sakata cikin damuwa, bayan sunyi sahur, Ta kira Yayarta ta gaya mata, cikin farinciki da murna ta ce tazo tana bukatar abokiyar hira. Sannan ta gaya mata dalilin zuwan Zaytoonah karatu zata yi, Itama ta karfafa mata gwiwar haka, dake Allah ya taimaka dukkansu suna da abun yi domin itama Aminatu koyarwa take a nan Jami'ar Cameroon.
- South Africa. Sai da aka kai ruwa rana, kafin suka bashi hutu tun zuwan shi bai matsa ko nan da can ba, yana makale da aikinsa, sannan da ya nemi hutu kin bashi suka yi, sai da ya koma ya rubuta musu ajiye aiki. Da shugabansu ya gani a fusace ya yaga takardar. "kana da hankali kuwa? Kasan yadda muke alfahari da kai da zaka so ajiye aikinka?" Kusan soja da bala'i da masifa da ihu, shi dai bai ce kome ba yayi shiru yana sauraren Commander ɗinsu. Har ya gama sannan ya dauko wata takarda, ya rubuta mishi an bashi hutun sati biyu. "Sir mahaifiyata ba zata fahimce ni ba, sannan ina son a bani koda wata daya ne, nasan is too hard na samu wannan kwanakin. Amma idan na ajiye aikin zata fahimci ita din abar girmamawa ce." Dake Commander din Muslimi ne kuma dan arewancin Nijeriya, murmushi yayi ya ce mishi. "Abdul Majid Mamman Ba'are, nasan waye kai Chairman guda da yake gudun matsayinsa. Sai dai an haife ka ne domin ka zama soja, ba wai kayi aiki da sojoji ba, zan baka wata gudan amma ka sani can kujerar da kake gudu, zata bibiye ka a duk inda kake matukar kana raye. Kasa yayi da kanshi yana kallon takalminshi da bai daura igiyar ba, "mahaifiyarka tana son ka rike matsayinka ne, domin hankalinta zai fi kwanciya. Sai dai ba abu me sauki bane a wurinka. Kayi imani da hawa saman teku domin aikinka, ka dauki kamfanin a matsayin teku ne, ta gaya min kome akanka da kuma kamfanoninku."
Bai ce mishi uffan ba, yasan halin shi sarai ko abokan aikinshi ba karamin mita suke akan wannan halin nashi na rashin magana ba, har kawo ƙararshi suke amma babu abinda ya sauya, wani irin murdadden hali ne dashi, yaki sabo da kowa aikin shi kawai yake baya kula kowa baya harka da kowa baya shiga harkar kowa, ina ka fito aiki ina zaka aiki. Haka yasa ko irin yan matan nan babu me shiga sabgar shi, domin sun tabbatar da cewa shi din ba daidai ba ne, kuma bai da lokacin mace.
"Shi kenan Allah ya tsare, ka dawo lafiya."
Salute yayi sannan ya dauki takardar, ya nufi hanyar waje, yana kallon agogon hannunshi. Sam bai dauki rayuwarshi da zafi ko fadi ba, asalima ya ajiye kanshi inda yake ganin nan Allah ya ajiye shi, bai tab'a nuna fad'in rai ko kuma nuna cewa shi din wani ba ne, yasan yana da dukiya me yawan gaske, amma haka bai tab'a damunshi ba, asalima shi yafi saka kanshi a matsayin kananan mutanen da suka taso cikin talauci da wahalar rayuwa.
Wannan yasa baya jin girman kai ko wani abu, meye a rayuwar da wata rana mutuwa zaka yi, sannan magana ce babu wanda ya isa saka.shi, shi bai saka kowa lallai dole a kula shi ba, kuma baya jin lallai dole sai yayi magana duk wanda yaji haushi to ya daukarwa kanshi dala ba gammo ne.