Sashe 112
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kwana biyu da zuwana, muna cin abinci Nura dan kawun mu Musa ya shigo yana kallona ya ce min. "Zahra balarabenki yana kiranki a waje." Tsame hannuna nayi. "Yanzu Zahra haka xaki auri balaraben nan ga dan uwanki." Juyawa nayi na bankawa Anisah kallo. "Karuwarce zata auri dan uwanki? Karuwarce zata zauna da dan uwanki. Ko kin manta kwadayin kudi ya kawo ni kamfaninku?"
Ina fadar haka na wuce abuna, na fita ban kuma shiga dakin ba, na je na same shi ya gaya min cewa. "Yana son ya tafi, ana niman shi ne!"
"Sai yaushe zaka dawo?"
"Zan dawo in sha Allah, ni dai ki kula min da kanki. Zahrah ina son na roke ki wata alfarma." Ya faɗa yana kallon yadda nake murmushi na ce mishi. "Allah yasa zan iya maka alfarmar nan!"
"Idan ban dawo ba, kada ki jira ni." A hargitse na zuba mishi idanu. "Me kake nufi?" "Ina nufin idan ban dawo ba, kada ki jira ni?"
"Me yasa nayi maka wani laifi ne?" Na tambaye shi. "Ko daya, sai dai ina sonki ne.!"
Ya faɗa yana murmushi, kafin ya cigaba da cewa. "Kin tambaye ni akan abin da kika yiwa Zulaihah akwai rashin adalci a ciki ko?" Idanuna da suka kad'a jajjur, na zuba mishi.."Tabbas akwai son zuciya a cikinshi. Shakuwa gaskiya ce amma dauko mata Y'a da kika yi kin so kanki. Ita tafi ki son zuciya, ta fiki sonkai a duk inda gaskiya take mu gayawa juna shine cikon zaman lafiya, idan Zuzu tazo ki hakura da Aamirah ki bata yarta, ba zata kuma cutar dake ba sannan kuma tare da mahaifiyarki kada ki ce zaki saka arai a kan wadancan yan uwanki, ki zauna da mahaifiyarki zaki samu nutsuwa, zata zo zata biyo yarta kada ki sake ki saka yarinyar a ranki har ta fahimci ita ce matsalarki, ki basu yarsu wani lokaci muna hakura da abubuwan da muke so ne sai a zauna lafiya, kada ki ce zaki ajiye kome don Amira, idan kika yi hakuri zaki haifi kamar Amina zaki haifa zaki haifa abinki."
"Da alamu idan ka tafi ba zaka dawo ba?" Dariya yayi min yana faɗin zan dawo mana, idan ban dawo ba kada ki jira ni."
"Zan jiraka har karshen rayuwata." Rufe min baki yayi da hannun shi, "Zan dawo. Sannan ki dauke ni a matsayin Yayanki dan uwanki, me share miki kuka?"
"A'a ban yarda ba!" Na fada da ƙarfi, juyawa yayi ya bar zauren, zama nayi a wurin na fáshe da kuka, ta asalin babban kofa ya shiga gidan yayi musu sallama, sannan ya fita kamar ance na leka. Na gansu tare da Majid suna tafawa har da hira. Abin su har da dariya. Ban ji me suke fada ba sai gani nayi Majid ya rike kunnen shi. Lallai wato ni zasu yi wa dan waken zagaye. Juyawa nayi rai a b'ace. "Me yasa ba zaki hakura da shi ba?"
Kallon Mamana nayi, kafin na fashe da kuka. "Yayi min halacci." "Duk da haka zuciyarki bata samu wanda kike so ba ne, Yazid yayi miki halacci, domin har abada ba zaki samu na biyun shi ba, adali me adalci da tausayi. Ba banza ya zama Sultan ba."
"Mama ina sonshi." Riko hannuna tayi, ta ja ni zuwa waje sannan ta bude mota ta saka ni, muka bar gidan a idanun Majid. "Muje waje ki sha iska, nayi kewarki."
Haka muka ta zaga gari kafin ta kawo ni, wani lambu. "Kyautata miki da Yazid yayi babu wanda ya isa ya ce bai cancanci aurenki ba, domin yayi miki abin da muma bamu miki ba. Abisa ala'adar mahaifinmu idan mace ta haɗa maza biyu, kuma suna sonta yana iya basu addu'a duk wanda yayi addu'ar aka dace zai zo mishi da zancen aurenki ne, Lokacin da muka hadu da mahaifinku ina da wanda nake son zan aura.
Haka Babanku yayi ta bibiyar rayuwata, amma naki kula shi. A lokacin da yazo akwai dan Yayan Yafendo da muke soyayya. Haka Malamijo ya basu addu'ar, me haɗe da niman zabin Allah. Ina ji ina gani suka yi addu'ar, kwana biyu Abbas yazo ya ce ya janyewa Mahaifinku, shi yana da wata rayuwa na daban zai tafi domin cimma ta." Hawaye ne ya zubo mata,tayi murmushi. "Allah ya gani bana son Abubakar, amma haka suka tasani a gaba na aure shi, da fari muna zaune anan, ya ce zai koma garinsu bayan na haife ki. Kin ga yan gidan mu babu wanda bai tafi aikin hajji ba, gata na duniya na samu..amma da Allah ya ƙaddara sai gashi na auri makiyayi wanda bai san fari a zamani ba sai dai addini kan babu laifi don yana da ilimin addini sosai. Koda nazo cikin gidan sai na fahimci dangin shi basu farinciki da ni, haka na zauna idan na cire miki Mahaifinsu babu wanda ya dauke ni mutum, amma Alhamdulilahi tunda wanda ya kawo ni yana sona, haka na cigaba da zama har zuwa lokacin da na bar gidan da laluran gushewar hankali, Allah ya takaita min wahala, daga can gida na dawo a hanyar dawowa na hadu da wadanda suka san Malamijo, sai dai na sha azaba domin wata na takwas ina tafiya da kafa, ga tsohon ciki. Haka na dawo gida aka min jinya, kafin na haifi Zaytoonah. "
Hawaye ta share bayan ya cire glass ɗinta, "Bayan nan ban kuma yarda na ambaci sunan Abubakar ba, domin a gidan nasan Addah ta tsane ni, sannan ta sha alwashin sai ta ga bayanki, na jima da fahimtar bata sona ita da sauran matan gidan, amma wannan ba dalilin ba ne da zan kullace ta, domin haka ta tsani Babanku kamar me, duk da yana mata bauta amma gani take kamar aurena yasa shi juya mata baya, don ta sha cewa ya sake ni. Amma yaki ban zargi kowa da yayi min wani abu ba, Amma nasan an zalunce ni matuka gaya."
Share hawaye nayi ina wasa da mayafin hannuna. "Malamijo yana son duk wacce zai mata aure ta kasance mai biyayya." Na yarda ya zab'a min miji, amma Mama ban da Majid." Na fada ina shashekar kuka. "Shima bai ce zai zab'a miki Majid ba, idan kuma Majid yana cikin kaddararki haka zaki hakura da shi."
"Na hakura kika ce? Mutanen da basu san darajar rayuwa mutum ba, Mama har Hajiya sai da tace na rabu da Majid me zan yi da su?"
"Duk da haka me yasa kika tawo da yar da ba naki ba? Kin gagara rabuwa da mutanen da suka tsane ki sai waɗanda."
"Mama kada ki ce min kina tare da Hajiya?"
"Ba haka ba ne, ba zan tayaki faɗa don kawai an b'ata miki ba, amma zan tashe ki daga barcin da kike kuma ba zan miki dole ba. Amma ki raba kanki da su Addah don rayuwarki suke nima."
Kuka na fashe da shi tare fa faɗin. " Wasiyyar Baffana ne fa!" "Idan ma me nene ya kamata ki ajiye kiyi fama da kanki, a wannan fagen ba naki ba ne, ki barsu shi ma bai iya da dangin shi ba balle ke."
"Mama kina nufin!"
"Idan kin mutu saboda, ina da Zaytoonah. Kuma ba zan fasa farincikina saboda ke ba, idan kin so ki rungume su ai ba wani abu ba ne waye ya damu, ban san wahalarki ba abu ɗaya na sani idan wani abu ya same ki, wallahi tsakanina da ke sannu. Domin ba zan manta da azabar da na sha ba, kuma idan Zulaihah tazo ki bata yarta, Babu kira babu abin da zai ci gawayi. Kema ki wanke kanki daga kallon da ake miki, muje." Idan nace Mama itama tabi layin su Yazid ban yi mamaki ba, haka muka dawo na shiga dakin Yafendo tana zaune, Aamirah tana gefenta tana tashan zuma. Zama nayi a gefensu ban san lokacin da na fashe da kuka ba, wani irin kuka nake wanda yasa Yafendo murmushi.
"Kiyi hakuri a bata yarta don ko kin hanata, ba zaki tab'a farin ciki ba sannan alaƙarku ba zai dawo ba, amma idan kika bata zaki rayu cikin farin ciki. Allah ya sakawa Yazid da alkhairi. Jiya mun jima da shi." Dattijuwa me tarin ilimin addini da sanin rayuwa tayi ta min nasiha har Mama ta shigo, Hajiya kam ko da ta shigo kasa magana tayi. "Mama zan maida ta, amma don Allah kada ki min auren dole." Murmusa min tayi tana faɗin. "ba zan tab'a miki dole ba, har abada babu dole a cikin gidan nan domin an daina."
Da wannan naji sauki a raina.
*
Zuzu
Kamar tayi hauka, lokacin da taji labarin Zahra sun bar nijar da ita. Bata kwana a Nijar ba, ta nufi Nigeria don dama akwai nata da Addah.
Akwai wani al'amarin da sai ka gama shirinsa, sai Allah ya lalata maka kome. Zuzu tayi niyyar sai ta binciko inda Zahra take, bayan ta gama yiwa Addah tijara. Sai dai bayan ta isa Kano, daga Kano suka hau jirgi zuwa Yola, a wannan yanayin al'amarin Allah ya shigo, domin shima bai tab'a saka ranshi zai ganta ba. Yana waya da wani abokin cinikayyar shi, kawai ya ganta kamar saukar aradu.