← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 138

Sashe 73

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
036
Tuntube Nana ta yi zata fad'i, Majid ya tare ta . "Innalillahi kaga ni ba? Ka ga ni ba tun ban bar asibitin ba ya fara ƙoƙarin ganin bayana." Shi dai bai ce mata uffan ba, har suka isa wurin Motarshi. Bude mata yayi ta shiga. Don jaraba glass ɗinta ma sai da ya kusa faɗuwa ta riko ta saka a juye, da wutsiyar idanu Majid ya kalle ta. Yana tab'e baki har suka bar Asibitin. "Hajiya!" Ya kira sunanta, bayan ya zare glass ɗinta ya saka mata shi. "Na'am Alhajin Allah." Murmushi yayi cike da takaici, domin tun fil azal ya dace su samu wannan soyayyar amma basu samu ba, sai rana tsaka. "Ka kira sunana kuma kayi shiru, ni bana son haka idan ka san ba magana zaka yi ba ka daina min haka, sai a kira mutum ya dauka wani abin arziki zai samu amma ayi shiru, ai wannan wulakanci ne." Bai ce mata cikanki ba har suka iso gida, zata fita taji kofar motar a rufe. Fito da yar karamar bindiga yayi ya ajiye, zare idanu tayi waje. "Hmm Alhaji me zaka yi da bindigarka haka?" Gyara zama yayi yana faɗin. "Duk wanda ya gaya miki labarin abin da ya faru, tow ki kirani ki tambaye ni kinji ko? Kada na kuma jin kina zargin wani kina jina?"
"Alhajin Allah, da akan wannan zaka min kashedi ai ba sai ka rike bindigarka ba, kawai ce min Nana kada na kuma jin kin zargi kowa, zan ce maka Allah ya huci zuciyarka bawan Allah ba zan kuma ba."
A ranshi yana jin dadin yadda take saurin razana, da hawa hanya. Idan da wata ne hayaniya zata mishi. "Kin ga dai ni ban ce kome ba, kawai abin da nake so zan saka miki lambata kawai ki gaya min kome ya faru zan baki amsa." Ya dauko wayarshi ya kunna mata videon abinda yake faruwa na hatsarin, taga dai ba Aryan din bane ma yake tukin Jamilah take tukin.
"Hmmm! Amma fauziya tsinanniya ce, ita ta kawo min labarin Aryan ya tafi ya watsa min jikoki a titi mota tabi ta kansu."
Lumshe idanun yayi ya ce mata. "Je ki kinji Matar ƙarfen daga ke ba ƙari."
"Alhajin Allah ka maida bindigar nan."
"Tow matar ƙarfe." Ya ajiye shi a asusun motarshi. "Hmmmm. Alhajin Allah yaushe zaka saya min nama." "Jeki za a kawo miki." "Alhajin Allah baka saka min wayarka a wayata ba." Ya karbi wayarta da yake makale a wuyarta har da igiya domin cire mishi tayi, yayi abinda zai yi ya mika mata. Layin sai tarin bashi.
"Taya kika ci bashi haka?"
"Ina zan sani tunda Yar gidan Hafiza ɗaukar wayar take, ba dare ba rana matukar na ajiye zata ɗauka." Hafiza stepsister ɗinshi ce, yarta tazo hutu. Ciro kuɗi yayi ya mika mata, "Ga Barka da sallah ɗinki." "Allah ya kara bud'i, na gode sosai." Ya bude mata motar ta fita, ya juya ya bar gidan bata shiga gida ba, sai da ta daina hango Motarshi ta shiga gida.
"Nana Oyoyo ya masu jikin?" Kuru tayiwa Hajiya Fauziya, kafin ta ce mata. "Ke dai Allah ya tsine gulma da munafurci da yake kokon ranki, munafuka Annamimiya. Kika saka ni zargin dan marayan Allah da yake kwance cikin jinya, kai fauziya ke tsinanniya ce wutar munafukai ya tabbata akanki. Munafuka makira. Allah ya isa min shi yasa Rabi take burge ni bata shiga harkar kowa amma ke kullum munafurci yana cin gindinki."
Tass ta wanke Hajiya Fauziya da kanta a kasa, ai Nana ta iya tozarci idan ka sake ka takaleta a gaban uban Kowa zata wanke ka kai din banza ina ruwanta tunda kai ka tab'ata.
Asibiti kuwa sai yamma can Amaan ya farka, Jamilah ce dai sai du'a'i domin hankalin kowa ya tashi ya dace ace ta farka amma al'amarin ya ci tura. Haka yasa likitoci suke kanta ba dare ba rana.

Hajiya ta farka itama, sai dai babu wanda ya bata labarin halin da Jamilah take ciki, ko lokacin da Amaan ya shigo dakin dakatar da Majid tayi ta hanyar juya musu baya. "Ya tafi bana son ganinshi." Alama Majid yayi mishi da hannu suka fita. Ƙoƙarin danne hawayen da suke son zubo mata tayi domin bata son tayi mishi kuka, idan tayi mishi kuka, bata san wacce irin rayuwa kuma zai yi ba, sai tayi ƙoƙarin danne abin a ranta, "Kiyi kukanki amma ba da nufinmu ba, kiyi jininki zai sauka sosai. Kiyi kuka ba ragwanta bane jarumta ce, rago shi yake ihun, jarumi hawaye yake zubarwa domin ya samu sauki a zuciyarshi. Hajiya bature ya ce "courage doesn't mean you don't get afraid, courage means that you don't let fear stop you," kiyi kukanki Ummina, kiyi kuka idan baki ba zai dame ki har karshen mu, ba iya shi ba hatta mu rashin kukan zai haifar da abubuwa dayawa." Zama yayi a gabanta yana murmusa mata ya ce. "Kina nufin Allah ba zai jarabce mu bane? Idan bai jarabce ki ba, Ummina ki binciki girman alakarki da Allah, domin shi baya jarabtar kowa sai wanda yake da kusanci da shi. Hajiya Ummina, Allah baya duban marasa nima a wurinshi sai masu nima, kada ki ce Allah bai amshi addu'arki ba ne, a'a ya amsa yana son ya ga girman hakurinki ne, Ummina Allah baya waiwayar waɗanda suka manta da shi, yana waiwayar masu ambaton shi ne. Ya amshi addu'arki na neman shiriya akan Yaranki, ya tab'aki ne don yaga hakurinki idan kika yi hakuri ya kara miki alkhairi akan haka. Hajiya Ummina kiyi hakuri domin rabonmu yake wahalar dake, Allah ya nufa ta hanyar mu zaki ta haduwa da kalubalen rayuwa. A madadin Yan uwana bakiɗaya muke nimawa Amaan Mamman Ba'are, yafiyarki da albarkanki."
A hankali ta saki kuka me sauti, yau Majid ya tunatar da ita Allah, a wannan halin da take ciki. "Ki godewa Allah da aka farga da lalurar shi idan kuma da gawarsa aka samu da wannan labarin fa? Hajiya akwai abinda kai a wurinka babban al'amari ne, amma a wurin Allah karamin al'amari ne."
Dafe kirjinta tayi, tana kuka har da shasheka."Kiyi kukan ki samu sauki Hajiyata, domin da haka ne ba zan tab'a yarda hawan jini ya sake tab'a min ke ba, amma idan kika yi shiru zuciyarki zata yi sauki tunanin da zaki ta ajiyewa domin ganin ya zaki yi, zasu tafi shaidan da miyagun mutane ba zasu same ki ba, domin kin rigada kin cire."
"Ba zan iya cire abin da na gani akan Amaan ba, ji nake kamar ba zan yafewa kaina ba." Ta fada tana kuka, "Zaki iya fa, amfanin kukan kenan ya sauke min kaso me yawa na damuwarki, kuma ba gazawa ba ce, amma tabbas zaki manta idan kika tuna inda Amaan yake raye, Hajiyata har da laifinki wurin barin Amaan ya faɗa wannan halin." D'ago kai tayi tana kallonshi. "Wallahi da gaske nake gaya miki, domin amman yana bijire miki ba shi yake nufin ki kyale shi yayi yadda yakeso ba, na sani dukkanmu kece kika haife mu, amma samuwar ɗayanmu yana iya shafe halin kowannen mu da yake ciki, Hajiya tun ranar ƙari kika bar tubani, domin da kin tsaya akan Amaan da haka bai faru ba, bakiɗaya kina tunanin idan kika takura mishi zai kauce ta wata hanyar bayan kyale shi, shi ne fadawar shi halaka, Hajiya wani hanzari ba gudu ba, ni kina son nayi aure. Amma baki san me yake damuna ba, Hajiya idan xan yi auren na su macen da nake so, karshe xan iya zama me karkon kifi daga ruwa zuwa wuta. Hajiya idan har da gaske ke Uwa ce, yanzu ya dace ki tsaya akan Amaan ba kyale shi ya rayu babu wani a kusa da shi ba."
"Duk ƙoƙarina akanku dama na gaza ne?" Murmushin karfin hali yayi mata, ya ce mata. "Har kwanan gobe ba zan kiraki raguwar Uwa ba, domin duk inda ake bukatar uwa jaruma kin kai wurin, sai yan kura-kurai da ba za a rasa ba, amma ai kin yi ƙoƙari domin zaki iya lashe kambun uwa ta musamman a duniya."

Majid yayi maganar da yasa jikinta yayi sanyi, don bata taɓa kawowa gazawarta akan Amaan shi ya haifar mishi da lalacewar shi ba, yasa tayi shiru sanin ya kara mata aiki yasa shi fita ya sayo mata magani har da me saka barci, ya b'alla mata ta sha. "Tabbas nice na taimaka mishi wurin lalacewa, domin a lokacin gani nake idan ban barshi yayi yadda yake so ba, zai iya lalacewa."
"Yanzu ai mun rufe wannan chapter ɗin ko Hajiyata." Ya zauna yana kallonta, ɗaukar wayarshi yayi yana danne-danne. Shiru yayi domin yana son tayi shiru ta kwanta. Kuma hakan ce ta faru, da ta gama yan nazarinta, kafin ta kwanta barci yayi gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke ya kara karfin ac din dakin sannan ya nufi jikin windown dakin ya tsaya yana kallon waje. Dole ne a gare shi ya fuskanci kowacce matsala.
Wayarshi ce tayi kara ya dauka, "Majid Mamman Ba'are, na ga sakonka. Allah yasa haka shine mafi alkhairi, kuma ka dauki matakin da ya dace. Kasa da duniya ba zasu manta da alkhairinka ba."
"Na gode Sir" ya faɗa, haka suka yi sallama, yana jin wani sabon nutsuwa yana saukar mishi ya ajiye aikin soja ya huta. Yanzu dama biyu gare shi ya tsaya asibiti ko ya karbi kamfaninsu.
Chapter 73 · 0% Book details