Sashe 109
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
hannunta, yadda Yazid yasan Zahrah sam baya jin zafi dayawa akan Majid yana shige mata,don billahi azim tsaf zata kunce maka kome. Haka yasa shi riko hannunta har dakin da aka kwantar da Amirah, suna tsaye. Bana ce ina cikin farin ciki ba, amma yau ganin sakon Zulaihah ya fama min ciwo dayawa, na kasa kome sai hawaye, har likita ya fito ya ke gayawa Yazid da sauki sun rage kaifin maganin, a daren barcina ragagge ne domin kuwa ina rufe idanuna zan ji kamar za a dauke ta, Allah ya taimaka Yazid na tare dani, yana rike da hannuna. "Kiyi hakuri kin ji." "Nayi wani abu da bai dace ba ko?" "A'a sai dai soyayyar yan uwanki ta rufe miki idanu." "Ya zan yi?" Na tambaye shi, "ki hukunta su haka zai saka su fahimci lallai kina da fushi." Murmusa mishi nayi, kafin na ce mishi. "Ba zan iya ba, ba zan tab'a ba idan ayi haka na zama mara hakuri, duk abinda zumunci yayi min ba zai saka na saka wuka na datse alakata dasu ba." "Ina sonki!" Yau kalmar tafi koda yaushe dukan zuciyata, na tsayar da kome nawa da wannan fitinar gara na auri Yazid. Saboda ya bani farinciki sama da kome ya saka ni dariya kma zai cigaba da saka ni dariya. "Zan tafi Marwa kan yanzu da Amirah. Kai kuma ka tafi wurin Ya Babangida kuyi magana, zaman Nijar ya kare idan kuka tsayar da magana ina marwa!" Jan hancina yayi yana faɗin. " Na jima da jiran wannan ranar. Yau gashi Allah ya kawo min." Ya faɗa yana murmushi. Nima sunkuyar da kai nayi ina wasa da yatsuna. Haka muka kwana a wurin masallaci ya wuce ni ma a dakin Amirah nayi sallah, bayan na idarwa na wuce dakina, na hada tea na sha na hadawa Amirah na kawo, tana barci har lokacin. Ina rungume da ita. Barci ya fara fisgana har nayi me nauyin, sai ji nayi ana shafa kaina. "Zahra!" Bude idanu nayi dakyar amma ina barci yaci karfina. "Na gode sosai, naga Amirah sugrah. Amma ina son Y'ata na kasa barci without aamirah, nasan ke adila ce kuma zaki bani Y'ata sannan ki gaya min nawa kika kashe zan biya amma ki bani Y'ata don Allah nima ina son naji dumin ta As a mother." So nake na bude idanuna, amma.nasaka ina son na tashi amma na kasa, abu daya na sani na k'amk'ame Amirah, a hankali barci yayi awon gaba da ni. Ina ga mafarki nake. Ban tashi ba sai dare, a lokacin hankalin Kowa ya tashi,don a gwada jinina da aka yi ne aka tabbatar akwai sinadarin bugawar a ciki,a hankali na bude idanu. "Alhamdulilahi ta farka!" "Tun yaushe nake barci?" "Tun five na safe." Kokarin tashi nayi na kasa, don har lokacin babu karfi a jikina. "Me ya faru?" Na kuma tambayarsu. "Kwantar da hankalinki babu abinda ya faru." Nifa na zata mafarkin zuzu nayi, sai da aka tabbatar min an samu abin maye a ruwan tea da nasha, ware idanu nayi tare da dafe goshina. Dakyar na tashi na shiga ban daki nayi Alola da wanka zan fito naga dan takarda a jikin allon madubin banɗakin. *Ba mafarki kike ba, da gaske ina son Y'ata nice na saka miki abin maye a ruwan tea ɗinki." A hankali na zare takardan na yi plushing dinsa.... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB259 Ina fitowa na samu an shimfida min abun sallah, sai da nayi sallah sannan nayi addu'a, abincin da Yazid ya Kawo min naci. "Babu yadda zan bar garin nan kafin nan da jibi?" "Akwai mana." "Don Allah a kai ni Marwa!" Na fada cikin tsananin kad'uwa, murmushi yayi yana faɗin. "In sha Allah daren gobe zaki bar garin nan, amma ki fara ajiye musu aikinsu." "Tow! Yanzun nan." Na fada jikina yana rawa don bakiɗaya hankalina baya jikina, rike kafada ta yayi yana faɗin. "nutsu" na fashe mishi da kuka na ce mishi. "ya zanyi? Yan uwana sune matsalata." "Kece kika mai da su matsalarki." Cikin kuka nace. "Kamar ya? Taya na mai dasu matsalata? Taya zan ." "Zaki iya mana, ki kwantar da hankali sannan ki nutsu ki saka a ranki zaki tafi kuma zuzu ba zata kuma zuwa wurinki ba." "Zata zo wurin Yarta." "Ba zata kuma ba." ... Dakyar ya rarrashe ni, sannan na rubuta takardar barin aiki. Abin da ya faru... A ranar da Nawwas ya ɗauke ta, a ranar ya ga Amirah. Kuma dama suna tab'a juna da Zuzu,akan ya nima mata inda Zahra take da Babynta. Sai gashi ya ganta don haka ya tura mata da hoton yarinyar domin kuwa ya jima yana bibiyar yarinyar da makaranta da ko ina da suke, tunda ya tura mata Zuzu ta d'aga hankalinta. A ranar da tazo a ranar Zahrah ta hadu da su Addah tana airport din, sannan ta je har asibitin tana bibiyarsu.