Sashe 74
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai dai wani abu da yake ganin zai fi mishi, zaman asibiti domin akwai abinda yake tuna mishi military section. Murmushi yayi yana jin wannan shine mafarin farincikin shi.
Sai da aka sallami Hajiya da Aryan, amma Amaan yana cigaba da jinya. Domin har zuwa lokacin ana kan zancen mishi tiyata ne, don duburarshi dole aiki za ayi mishi.
Manyan likitocin da suka kware akan tiyata, har da shi Majid a ciki suka jagoranci tiyatar farko, domin zama yana shirin gagararshi. Koda akayi aikin farko za a iya cewa an samu nasara, tunda har an samu yana iya zama tare da yin bayan gari da kanshi.
Jamilah ce dai da alamu sai yadda Ubangiji yayi da ita, a wannan yanayin Zaytoonah da Mamarta suka zo, har da Yafendo.
•
Camp.
Wato al'amarin Addah sai a hankali, domin kuwa idonta ya lalace. Duk yadda aka so a gyara amma abin ya ci tura, a duk lokacin da Addah ta kalli idanunta, ta kuma tuna cewa saboda Zahra idanunta ya lalace, tana kara jin matukar tana raye Zahrah tana raye sai ta rusota daga sama, sai tayi kaca-kaca da duk wata daukakar Zahra.
Jin za a shigo dakin tayi maza ta boye madubinta, bayan Ummi ta rigada ta gani. "Kina kallon idanunki ne?" Ummi ta tambayeta babu wani abu a ranta, amma dake tana kallon kamar izgilanci Ummi zata mata, ita kuma zuciyarta daya tayi maganar. "Kina min dariya ne don na rasa idanuna ɗaya? Ai ba ayiwa ƙaddarar wani dariya yau gare ni gobe ga wani."
"Ke dai kika sani, abin da yake zuciyarki kike faɗa, amma ya daga tambayarki kawai zaki hau surutu kamar wacce aka zaga."
"Shegiya munafika, algunguma."
"Eh na yarda amma ban kai ki ba, makashiya me sayar da Yarta domin duniya da abin cikinta"
"Ni kika zaga karuwa kawai, wacce ta zubda cikin shege."
"Kanku ake ji, farka da makaho."
"Lalatacciya mazinaciya."
"Duk abinda muka aikata ai laifinki ne, domin kece kika aika mu, bari ki ji ko jahannama zan shiga ina fatan Ubangiji yasa tare dake ne, gani ga ke. Ina kallonki kina kallona."
"Tsinanniya muguwa, in sha Allah ba zan shiga cikin jahannama ba." Addah ta faɗa tana mikewa, Ummi ta ce mata. " Kika sake hannunki ya tab'a ni sai na miki shegen duka, idan kina ganin wasa ne Bismillah." Ta fada tana mikewa a fusace tana watsawa Addah harara.
"Ni nace zan dake ki ne? Kawai don kin ga na tashi sai ki fusata." Lokaci guda tayi sanyi, domin tasan Ummi bugun kato zata mata.
•
Wata biyu da sallah, karatu yayi zafi domin kuwa, gashi bani da lokacin kaina sai na karatu zuwa yanzu babu wani da yake tare da ni sai su Maman Barakatu, a wurinsu Amira take zaune, idan na dawo haka zan huta na shiga cikin gidansu. Dake motar da ake kai ni makaranta sun bar min ita, ni kuma kunya nake ji na ja motar.
Ina kwance kamar ruwa ya cinye ni, nifa sai yanzu na gano raguwa ce ta gaske. Domin kuwa idan na dawo nayi sallah na kwashi abinci, to nan nake bajewa, habawa bana iya tabuka kome kai Allah na gode talaka bai iya samun wuri ba, sai na baje nayi ta nishi dai-dai kamar wata tsohuwar akuya.
• Duk yadda Hajiya taso danne abin, kasa rike zuciyarta tayi. Domin ganin har Yafendo a Nijar yasa zuciyarta laushi ta shiga fesar da abinda yake ranta, tana faɗa tana kuka. "Wannan sirrin Yaranki ne, ko kin gaya mana sai dai mu baki hakuri kamar yadda Abdul Majid ya gaya miki, kin bar Amaan don yana nunama Majid kiyayya kike gudun kada wani ya sani ya yi amfani da hakan ba? Tow ga shi nan yadda aka wayi gari, Wa garin ya waya? Addah na sha gaya miki duk abinda ya faru dake ba laifin kowa ba ne, laifinki ne akan Yaranki ya dace ki tsaya. Don Allah kada ki kara barin haka ya faru."
Cikin shashekar kuka ta ce mata. "Har yau baki ji labarin batula ba ko?" Murmushin karfin hali tayi tana faɗin. "Ta rasu fa, ni kan.har nayi mata addu'a Allah ya mata rahama."
Amma!"Ni kuma ina ji a jikina Batula tana raye, kamar tana kusa damu."
"Kawai kina jin haka ne don kin saka hakan a ran ki ne amma ni nasan bata raye."
"Ammi don Allah rike min, Mimi." Ta mika mata Yarta zata fita, "ina zaki?"
"Zan tafi wurin Hamma Abdul a can asibiti."
"Hmm! Ki dauki yarinyarki me shegen kukan tsiya." Inji Mamanta, "barta ba zata yi kuka ba." Da sauri ta fita bata ma tsaya ba. "Zaytoonah tana son Majid sosai."
"Bana jin akwai bukatar ayi wannan zancen, domin kowannensu ƙaddarar shi daban." Inji Yafendo tana shigowa. "Yafendo ko don zumuncinmu!" Inji Hajiya.
"Malam ya gaya min cewa duk yadda muke son, su had'a kansu haka ba zai yiwu ba. Domin kuwa kowa da ƙaddarar shi da rabonshi"
"Kuma ai babu adalci ace Majid ya auri bazawara da Yarinyarta a duba dai." Inji Maman Zaytoonah, "kada na kuma jin irin wannan zancen." Inji Hajiya.
Dariya Yafendo tayi domin tana jin dadin yadda suke tsayawa junansu.
A can asibitin kuwa, dama da gayya Majid yaki komawa gida, don idan ya koma suka yi idanu biyu da Zaytoon ba barin shi zata yi ya huta ba, shi yasa shima ya hana kanshi komawa gidan.....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce.
[4/19, 4:22 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*037*
*Aunty Nuratu Salihu Abba gaisuwarki ta musamman ce. 😹 Tare da Team Hajiya Tani ikon God 🤣*
A harabar gidan suka hadu da Nana, kallon uku saura kwata Nana tayi mata, kafin ta dauke kai kamar ba zata amsa gaisuwar da take mata ba, kafin ta amsa ta ce mata. "Ina zaki haka?" Tana hura hanci. Zuciyar Zaytoonah daya ta ce mata. "Wurin Hammayo zan je a asibiti." Ta mikawa Driven food flask, wani haɗe fuska. "Ce miki yayi yana jin yunwa?" Ta fada tana wani haɗe rai, "A'a kawai nayi mishi irin abincin da yake so ne." "Au ya gaya miki ba'a bashi abincin da yake so ne?" Gajiya da Jarabar Nana Zaytoonah tayi ta wuce zata shiga mota, Nana tayi bake-bake. "Wallahi bakya shiga ki je wurin shi." Fitowar Aryan tare da Nabeeha suka samu ana rigima, ita kan Zaytoonah zuba mata idanu take, sai masifa Nana take. "Kai Ariyan wannan yarinyar me kama da muciya da zanin me take nufi da Alhajin Allah?"
Juyawa yayi ya gama duba ko ina bai ga me kama da abinda ta siffanta ba ya ce mata. "Wa kenan?" Ya tambaye ta, zubura baki tayi tare da zunden Zaytoonah da idanunta suka kawo kwalla, juya fulatanci yayi ya ce mata, "shiga mota ki tafi zan ji da ita.". "Wallahi wuta balbal ko kabarin mutum yana ci da wuta ba zan yafe ba, da zagin da aka min." Wuce ta Zaytoonah tayi ta shiga motar, kafin Nana ta fahimci abinda suke nufi motar ta bar gidan, kallon Aryan tayi baƙi sake. "Idan baka yi haka ba ai ba zaka tabbata ka sha nonon Fulani ba, kuma zan kira Alhajin Allah na gaya mishi domin nayi alkawarin bani cin amanarshi."
Garin masifa har madubinta ya fadi, dauka tayi tana faɗin. "Allah ya isa Annabin Allah ya isa, kuma duk wanda ya sake ya likawa jikana bazawara ban yafe ba, Allah bai yafe ba, Annabin Allah bai yafe ba." Ta dauki madubin ta saka shi a juye. Wayarta ta lalluba ta shiga dankara kira. "Halo Alhajin Allah " "bashi bane Haladu ne Nana." Kashe kiran tayi ta kuma lallubar wani number. "Halo Alhajin Allah." "Nana Halima ce fa!"
"Yau naga tijara Alhajin Allah nake nima." Ta kuma kashe kiran, ta wuce gidanta, tana kiran Driventa"Salele!" Da sauri ya iso. "Kira min Alhajin Allah."
Tunda ta fadi Alhajin Allah yasan Majid ne, don haka.ya kira mata shi ya mika mata wayar. "Gashi nan Nana." Karba tayi wayar ma a juye ta saka a kunnenta. "Halo Alhajin Allah, kasan ba zan cuce ba kuma ba zan ci amanarka ba."
"Eh Nana!"
"Tow ga wannan doguwar yarinyar nan, me kama da fatalwa tana kawo maka abinci. Ban san me ta kawo maka ba, na dai gaya maka gaskiya a tow ba zan iya cin amana ba."
"Na gode Nana!"
.... A asibitin kuwa tun kafin su isa, Nana ta fesa mishi zuwan Zaytoonah, don haka ya shige Office ɗinshi yana shiryawa domin tana zuwa zasu fita. Bayan son wani ya san akwai wacce take bibiyar shi yanzu a fara yayata shi. Lokacin da Zaytoonah ta iso ne take raba idanu, tana nimanshi. "Yan mata!" Ya kira sunan, juyawa tayi tana tura baki, "cutie cutie pie zaka ce." "Ok muje!" Ya amshi basket din Hannunta, ya mata jagora har dakin da aka kwantar da Jamilah, "Hamma ya cikinta?"
"Lafiya lau, baby girl ce kin ga yadda take, girma kuwa." Ya nuna mata wani computer da yake kula da cikin Jamilah.
"Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah." Daga nan suka nufo wurin Amaan , anan suka sha hira kamar ba gobe, sai dare ya sakata a mota ta dawo gida.