← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 138

Sashe 45

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

--
Washe gari.
Hajiya ta hada kan Iyalanta zuwa Marad'i, har da Amaan yana Motarshi a baya, Hajiya da su Aryan suna mota daya, sai hira ake kamar yadda suka saba ana zolayar juna, Aryan ke tuka motar, shi yana zaune a gefen Aryan din, idanunshi rufe. *Ka taimaka min kada na mutu!* Bude idanunshi yayi yana kallon gefen hanya, tare da juyowa yana kallon su Hajiya da suke dariyar Widad, ta dage sai magana take tana mita. "Ya dai Hammayo?" "Babu kome." Tabbas yaji muryarta, amma kuma yasan don ya damu kanshi jiya da niman Umaimah bai samu number ta ba, asalima jiya har da mafarkin abinda ya faru, yana son ganin likitan da yake mishi therapy, lumshe idanun yayi cikin wata irin gajiya, domin baki daya yana jin wani sabon yanayi na kara kusanto shi, kara jingina yayi da motar, ya shafa fuskar wayar shi da aka sauya mata screen. A hankali ya gwada kiran Ammar. Ai kuwa yana shiga ya ƙara bude manyan idanunshi masu kyau da sheki. "Ammar ka nimo min number da zan samu Umaima."
"Ok Sir ya kake ya hutun naka."
"Alhamdulillahi! Sir sai muka ji labarin ba zaka dawo ba. Sir"
"Zamu yi magana an jima;" ya fada yana kashe wayar. "Wai da gaske ba zaka koma Nijeriya ba?" Inji Aryan, "I ba zan koma ba " ya faɗa yana kauda kanshi,karar da wayarshi tayi ya sa shi duba screen din wayar. Shiga kan message din yayi ya tura mishi. "Thanks!" Sannan ya danna number, can sai gashi ta shiga. "Ya yarinyar nan take?" "Eyeeeee!" Bakiɗaya suka zuba mishi idanun suna jiran abin da zai fada, "ok please ki bincika ina son sanin yadda take." "Amma ya kamata kayi min sallama sannan ka gaishe ni!" "Kin ga bani da." "Yes nasan baka da lokacin gaisuwa. Nima na bincika last month an ce an samu crisis a garinsu." Cikin wani tsuke fuska ya ce mata. "I don't care Koda ace garin babu kowa, ki nima min information akanta. Domin ina son sanin yadda take ne." "But niman abu kake sai nake jin babu dad'i kamar kana saka ni lallai sai na maka abinda." "Ok taimaka min" ya faɗa a gajiye da kuma son maganar ya ƙare. "Shi kenan zan bincika in sha Allah."
A hankali ya sauke wayar daga kunnenshi yana me fatan Allah yasa ba mutuwa tayi ta sanadin abinda ya farun nan ba, domin bai san me zai ce ba. Zufa ne ya shiga karyo mishi Aryan da Hajiya kuwa sun tsare shi da idanun suna son ƙarin bayani. Juyawa yayi ya ga yadda suka saki baki. "Wacece ita?" "Aaaah ba fa wani abu ba ne, kawai na mata treatment ne a gidana." Daga haka ya ja bakin shi shiru , duk yadda suka so yayi magana gum yayi da bakinshi. Zurfin ciki irin na Abdul Majid ai ya b'aci, ita kan Hajiya tayi mamakin yadda aka yi ya bukaci jin labarin wata. Tasan duk inda yake rayuwa bata taɓa jin labarin mace a tare da shi ba, duk da taso hada shi aure da Yar Kanwarta wato Zaytoonah, amma al'amarin yaƙi yiwuwa asalima tunda tayi mishi maganar aure bai kara yarda ya bada fuska ba, har suka isa marad'i bai ce uffan ba, itama bata kuma yarda tayi magana ba, sai da suka isa Gidan Alhaji Abubakar Abzin, dake ya tashi daga tsohuwar unguwar da suka san shi. Aryan kadai yasan unguwar da suka koma.
Sun same shi a gida, Hajiya na bayan Aryan ita da matar Aryan da Yaranshi, Majid yana mota yana waya. Suka shiga cikin gidan, yana kallon Amaan Mamman Ba'are ya fito tare da Matarshi, da Yaranshi sai lokacin ya bude motar shima ya fito suka kalli juna. "Hammayo ina wuni!!" "Lafiya!" Ya faɗa, don ya lura matar Amaan bata da nutsuwa da tarbiyya, yaran ma gasu nan kamar su kamar uwarsu, an musu shigar diban albarka. Dauke kai Amaan yayi, hala yana jiran Majid ya gaishe shi. "Daada ina kwana!" Inji Amir. Daukar Yaron Majid yayi, yana ce mishi. "Lafiya lau Amir Ba'are." "Daada kafi Abbanmu kyau, kuma ka fishi kirki." Murmushi yayi yana kallon Amaan din. "Baya daukarka ne?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Daada kana dariya shi kuma baya dariya." Murmushi ne ya kwace mishi yana kara rike Yaron, da sallama suka shiga babban falon gidan. "Daada nima ka ɗauke ni." Inji little Abdul. Ajiye Amir yayi ya dauke shi yana dariya. "Abdul Majid kannenka sun maka wayo kaga sun tara zuri'a saura kai." Murmushi Iya tayi tana kallon Abdul Majid, ta nuna shi da sandarta tana faɗin. "In sha Allah, Matarshi da uku-uku zata cika mishi iyali."
Murmushi ne ya subucewa Hajiya, ta ce mishi. "Allahummah Amin, Iyah Allah ya yarda." Ta fada tana kallon Majid da yasa fuskar shanu. Wasa da hannun Abdul yake. "Captain Allah ya kawo mana kai kenan " murmushi yayi yana me sunkuyar da kanshi, "Eh Abba!" Kura mishi idanu Alhaji Abubakar Abzin yayi kafin ya ce. "Allah ya jikan Mamman da rahama! Ya yafe mishi kurakuransa."
"Allahummah Amin" suka fada baki daya,. Abincin da aka kawo musu, suka ci bayan an basu wuri. Bayan sun gama Hajiya suka shiga cikin gidan yan mazan suka nufi masallaci, basu dawo ba sai da aka yi la'asar sannan suka shigo, anan aka kara gaisawa sannan aka bude shafin hira. Kafin, suna hirar karamin D'an Alhaji Abubakar Abzin ya shigo. Mahdi Abubakar Abzin, sosa kai yayi yana faɗin. "Abba kayi hakuri don Allah." "Taya zan cigaba da barinka a matsayin lauyana? Dole na nemo wani da zai cika min alƙawari." "Ka kara hakuri dai Abba! Nifa ba zance ka biya ni ba, duk Lauyan da zaka dauka sai ka biya shi kudi me yawa." Daure fuska Alhaji yaji ya ce mishi. "idan har bukata zata biya ai shikenan babu matsala sai inbiya, amma meye amfanin badi ba rai? Meye amfanin ka tunda bana biyanka jeka ka ajiye min aikina." "Alhaji ni zan nima maka wani lauyan." "Bana so ai Ni ba makaho ba ne."
"Allah ya huci zuciyarka." Ya zauna yana dauko wasu jakakkuna ya ajiye, waya Alhaji Abubakar Abzin ya dauka yayi magana. Kafin ya ajiye. "Lauyan Mamman yana zuwa." Kallon shi Hajiya tayi sannan ta ce mishi. "Abba ban gane ba!" Kallon Majid yayi kafin ya ce mata. "Majid zan bawa hakkinshi sanadin rayuwa da mutuwa, sannan ga shi nan ya bukaci na yi mishi wani aiki." Sunkuyar da kai Majid yayi, yana murmushin farinciki, yau Allah ya kwace shi daga tarkon Hajiya.
Can Lauyan yazo, "Malam Sulaiman!" Murmushi yayi yana faɗin. "Na'am Soja marmari daga nesa." Kallon Aryan yayi ya Banka mishi harara. Murmushi yayi ya ce. "Ba zaka gane yadda rayuwa da mutuwa take ba, shi yasa kake min kallon munafiki." Gyaran murya Alhaji yayi sannan ya bude taron da Addu'a, kafin ya ciro wasu takardu ya mikawa Mahdi. Shi kuma ya mikawa Lauyar Mamman Ba'are, shi kuma ya mikawa Majid, ya amsa yana kallon Alhaji Abubakar Abzin, "takardun ka ne, tun lokacin da aka haifeka Mamman ya bude maka kamfani anan da katsina." Sunkuyar da kai yayi yana kallon kasa, "Alhaji Mamman Ba'are bai kyauta ba, amma kuma ya rayu da boye kaunarka domin kada a kassaraka. Ke kanki ni nace ya nisanta ki da iyalinshi domin nasan cewa zaki zame mishi alkhairi." Mikewa Aryan yayi ya ce."ku dakata!" Ya nufi Amaan, kamar wani dan sanda haka ya shiga caje shi ya fitar da kome daga waya har agogon hannunshi, da zobe hatta botir din kirjinshi, a hankali wani abu ya fado. "Hmm!" Hajiya tace tana kallon Amaan cike da takaici, haka Aryan ya fitar kome. "Ko zaki bani sarkar wuyarki?" Hajiya ta mikawa Matar Amaan hannu. "Tow" ganin yadda suka tsareta da idanun. Haka ta mika musu harda agogo da dan kunnenta. Aka fita da shi waje, "Amaan baka da kunya. Baka da kunya baka da kunya ba zan maka baki ba amma ina rokon Allah ya shirye ka." Ko tari bai yi ba, "Abba ka cigaba." Gyara zama yayi yana kallon Amaan cike da takaici. "wancan takardun naka ne, wannan kyauta ce bayan an haifeka ya samu alkhairi mai yawan gaske, haka yasa ya cire wanan ya ce na baka naka ne, Hajiya Abdul Majid ya nemi na baki wannan takardur kiyi hakuri ki fahince shi." Amsa tayi ta ga takardar sallama ce daga aiki. Kallonshi tayi tana faɗin. "Ban san me yasa ka yanke haka ba, amma nasan kana da hujja me karfi."
"Aryan zai rike matsayinki na Chairwoman zai zama Chairman na kamfanin Ba'are, Anisah zata rike matsayin CEO!" Kallon Abdul Majid suka yi, sunkuyar da kai yayi yasan sarai irin kallon da Aryan yake mishi. "Amaan zai rike board director. Sa'adatu kin girma da zaki hakura da wannan gwagwarmayar, Abdul Majid ya bukaci haka domin ki huta."
"Abba shi fa?" Kallonta yayi yana son fadar mata abin da Abdul Majid din ya yanke amma yana shakkar yadda zata dauka. Mahdi ya ce mata. "Zai tafi karatu ne jami'ar sojoji da yake kasar Afrika ta Kudu." Ji tayi harshen ta ya mata nauyi da tayi magana, tana son tayi magana amma ta kasa tilas tayi shiru tana kallon Majid, "kin san me yasa bai bawa Jamilah wani matsayi ba? Saboda ga takardar asibitin shi zata rike matsayin shugaban asibitin. Amaan Mamman Ba'are zai rike matsayinshi ne baki daya."
Ajiyar zuciya Hajiya take saukewa a kai akai, cikin Murmushi Lauya yace. "idan Hajiya ta ce zata bawa Aryan matsayinta sai an sakata gaba da magana amma da mai gayya me aiki ya daura wanda yake so zai yi wuya a samu matsala." "Wallahi haka ne!" Suka fada bakinsu a haɗe. "Abba Alhaji ya gama abin da ranshi yake so, nima ina niman izinin nayi wanda raina yake so!" Murmushi Alhaji Abubakar Abzin yayi yana faɗin. "Kiyi yadda kike so!" "Aure nake son yayi, kuma na zab'a mishi yarinyar da zai Aura.............
Chapter 45 · 0% Book details