← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 138

Sashe 102

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka yasa shi jin ba zai iya ba, har ya tashi zai tafi wata zuciyar ta ce mishi. "Lusari katon sikago, haka zaka gudu ka bar macen da kake so? Waye ya gaya maka ana gudu, ka dauki salon shi ka kyautatta mata sama da shi, ina zaka sakarai." Dawowa yayi ya zauna har likitoci suka fito daga dakin, shima ya shiga tana kwance numfashinta da bututun iska take ja, sai da ya zauna yana kallonta, murmushi yayi yana kallon bakin tsiwar nan"
Yana zaune yana kallonta, Yazid ya shigo kallon juna suka yi, kafin Yazid ya juya baya yana zama a gefen gadon. A hankali yana waya cikin wani irin isa da mugun gadara, abin ya motsa halin da mulkin ya motsa haka yasa yake jin wani irin isa a ranshi.
"Duk yadda suka gadama su yi, ba zan dawo ba sai lokacin da na gama abinda naje Aseem ka gaya musu inji.". Jin hakan yasa Majid gane da mutanen gidansu yake, bayan ya gama wayar ya ja tsaki tare da kwafa. Wannan abin ya kara harzuka Majid ya bar dakin, tab'e baki yayi dama ai babu wanda ya gayyace ka ya faɗa a ranshi. A dakin ya kwana yana tsaronta, yadda zaka fahimci Yazid yayi masifar nisa a kan Zahra, nisar da baya sauraron kowa sai kanshi, wani irin tsaftataccen so yake mata me dauke da kauna zalla, babu duba jinsi babu duba kabilar da ta fito, babu duba waye Ubanta waye danginta, soyayya yake mata irin na ko daga sama kika fado haka nake sonki, Yazid ya san inda su Addah suke amma saboda kada wani ya d'aga mata hankali yasa shi hakura da kawo su inda take, Yazid ya binciko inda dangin Mamanta suke don har ya je da kanshi don sai da ya ji kome a bakin Babangida, burin shi ta sauke abin da take jira ne ya kaita wurin Mamanta amma gashi nan wancan dan shegiyar ya lalata mishi kome, saboda tsaro ko bakin kofa bai fita ba, dakin da take akwai karamin firji tashi yayi ya dauko abin sha, ya zauna yana sha yana latse latsen wayarshi. Hoton shi da ita ne a india, sun yi kyau sosai, murmushi yayi yana kallon yadda take fama da na'ura kanta.
Haka ya kwana a kanta, yayinda Majid ya tafi gidanta ya dauki Amirah da Barakatu, iya su ya samu duk da akwai tsaro a gidan amma a firgice suke, gidan Jamilah ya kaisu yasan Zaytoonah zata iya saka su a gaba, ba musu aka basu dakin. "Hamma yarinyar." Kallonta yayi a hankali ya ce mata. "wacce?" "Yar Zahrar bayan rabuwa ku ne ta haife ta?" A hankali ya zuba mata idanu, "Umaimah ta gaya miki abin da ya faru ne?" "Wa Zaytoonah da Anisah ta gayawa,Ashe karuwanci suke a fatakwal din?" Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata. "Tayi kama da karuwa ne da kike ganinta?" Jin irin amsar da ya bata yasata rike bakinta. "A'a, ai.nana tace ko Magajiyar karuwai ne haka take sonta."
Murmushi yayi ya mike tare da nufar waje, "ki kula da ita don na yarda dake ne na kawo su."
Daga haka ya fice, yana mamakin yadda Umaimah tayi irin wannan maganar a daren ya kirata, yayi ta masifa har da cewa bata da sirri kome dai ta faɗa ne, ta ji ko a gidan karuwai Zahra ta fito yana bukatarta haka, shi ita yake bukata ba virgin ba. (Karya kake munafuki 😭🙄🤣 Ja'iri zai raba masoya)
Koda ya iso gida yaki yarda ya nufi part dinsu, wurin Nana ya wuce ya samu tana sauraren Radio. Kwanciya yayi a dogon kujeranta. "Ya jikin Zahra'u, Allah sarki baiwar Allah ashe har kashe ta ka kusan yi?" Kwanciya yayi ya juya mata baya. "Ina magana Alhajin Allah kayi banza da ni?" Ta fada tana kashe radio din, tashi yayi yana faɗin "kina min magana amma kin kunna Radio Nana da naki zan ji ko da raido"
"Allah ya baka hakuri Alhajin Allah, dama nace ko zaka san yadda zakayi ne, ni dai ina son yarinyar domin dai ina hango alkhairi a tare da ku, ban damu ba ko a gidan karuwai take." Murmushi yayi yana faɗin. "Shi yasa nake sonki Nana."
"Hmm ayi sha'ani kawai, wani irin kiyayya ce ban nunawa Uwarku ba? Yau waye yake rike da ni, wallahi Mamman bai tsane ka ba, raba ku aka yi domin irin tanadin da yayi maka a kanshi Allah ne kaɗai ya sani. Don Allah kada wasu su saka ka kauce hanya akan yarinyar nan."
Murmusa mata yayi ya kwanta abin shi, ai baya jin akwai me dakatar da shi tunda Nana ta ce ya nime ta, ya nime ta kawai. Barci yayi a falon Nana, tana gama zamanta ta wuce dakinta.
**Bayan sallar asuba, ya wuce wurin Hajiya a falo ya same ta tana lazimi. Zama yayi har ta yi sallama, suka gaisa jin bata ce kome ba, yasa shi mikewa zai haura ta ce mishi. "Ina ga kada ka fara dauko maganar sakatariya, idan da a wani wurin ce ka hadu da ita ba laifi, amma a ji karuwanci suke abin zai tab'a zuri'a har duniya ta tashi, ba wai kinta nake ba. Amma ina son kayi mata adalci kada abin da ya same ni ya same ta."
Ban da Hajiya ce ke wannan maganar , da wani ne sai ya san yayi magana. "Na san lafiyarka lau, ita kake jira ba, ka nimo wata macen. Idan har ni na haife ka."
Murmushi yayi sannan ya ce mata. "Zahran da a yanzu ma bana jin na isa namijin da xan tsaya a gabanta, Hajiya kina ganin karya na miki da bani da lafiya ko?" Ya faɗa yana jin wani irin bakinciki yana cika shi. "Wanda yake tsaye kan Zahrah, cikakken namiji ne kuma Basarake ne wanda yake da kome, don haka ban isa na tari Zahra da labarin nine wanda ƙaddara ta haɗa mu can baya ba, taya zata kalle ni ma. Hajiya ga number likitan da nake gani idan baki gamsu ba, ki shirya muje na ga likita ni koda na samu Zahrah son kai na zai iya janyowa mu rabu. Kin ga babu damar auren wata mace balle Zahrah kenan."
Hawaye ne ya zubo mata, shima don yana namiji ne, a hankali ya ce mata. "Ina ta ƙoƙarin na fitar da abin da yake raina akanta, amma a yanzu na hakura da kome."
Ya faɗa yana nufar hanyar dakinshi, idan har Hajiya bata fahimce shi ba, waye zai fahince shi Nana ta fahimci halin da yake ciki, amma Hajiya ta kasa fahimtar haka. Da wannan ya shirya ya bar gidan. Wasa wasa sai da ya zama ko a kamfanin babu wanda yake ganin shi baya zama bakiɗaya, amma yana zuwa asibitin sosai don har lokacin bata farka ba, abin da ya fahimta Yazid baya farinciki da zuwan shi, bakiɗaya sai ya rasa inda zai saka ranshi yaji dad'i.
Sai dai bai tab'a yarda ya nuna gazawar shi ba, amma kuma a haka kishi suke da juna, idan Majid din ya zo baya damuwa da likitocin da suke wurin, zai dauki kome yayi ta dubawa, yana tambayar su yanayinta, a satinta daya ne su Hajiya da Aryan da Nana suka zo ganinta a lokacin suka ganshi sanye da kayan aiki na asibitin shi da wasu likitocin an fito da ita daga dakin za a kaita hoton domin yadda bakiɗaya ta ki farfaɗowa shi Majid yana ganin kamar akwai wani abu da ya buge kanta. Haka yasa yayi tunanin mata hoton kanta, a wannan bangaren Yazid bai mishi katsalandan ba, amma kuma ya nuna idan wani abu ya faru sai ya maka shi kotu.
Bai kula shi ba, haka suka fita da ita anan Hajiya ta ga dan gudun hijiranta, suka tafi aka mata hoton, babu wani abu da ya sami kanta. Kiran Umaimah yayi suka tattauna da ita, don haka aka nimo likitan zuciya, anan suka fahimci zuciyarta ne bata bugawa yadda ya dace, don haka za ayi aikin zuciyar suke tunanin. "Bana tunanin aikin zuciyar shine mafita, ku kyaleta akwai."
"Wannan wani irin shirme ne kake fad'a?" Inji Majid, yake kallon Yazid, cikin fushi shima Yazid din ya ce.."Shirme akwai wanda ya kaika ne? Ka barta na ce ba za a mata aikin ba."
"Aiki ya zama dole domin na amshi case dinta." Ai kuwa suka shiga sa'in'sa akan ita majinyaciyar. Duk yadda Umaimah taso raba su kowannensu ya hau dokin zuciya.
Chapter 102 · 0% Book details