← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 138

Sashe 111

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai da gari yayi haske muka dauki motar Marwa. A ranar naji kamar anyi min bushara da aljanna, haka muna tafe ina share hawayen farinciki. Sai da muka isa a wani babban gida me haɗe da masallaci, a kofar gidan manyan maza ke karatu gabanshi kadan yara ne suke karatun suma. Kallona yayi yana faɗin. "wancan shi ya haifi Mamanki, Sheikh Aliyu Wodabbe." Hawaye ne ya zubo min. "Share hawayenki kin ji." A hankali ya fito tare da bude min kofar, Barakatu da Amira da suke gaba suka fito, wani irin kuka ne ya kwace min ina rike da rigar Yazid. "Ya isa haka bana son kukan nan."
D'ago kai yayi ya zuba mana idanu, hannu ya d'aga ya fara addu'a, suma almajiran suka d'aga tuni aka tashi. A hankali ya mike tare da dogara sandarshi har inda muke. "Fatimah Batula!" Wani irin kuka ne ya kara zuwa min, "Sannu da zuwa, sannu da kokari Mai martaba, ka cika dan halak. Kayi abinda ya dace."
Daga haka ya wuce damu cikin gida. "Fendo? Sume yau ga kishiyarku tazo gare ku."
"Maza a kira min Aminatu ga Qurratul-Ayn dinta ta zo." Kafin kace me an cika falon Malam, tare da kiraye-kirayen waya,Yazid kuwa kamar su goya shi. A ranar dai muka rabu da shi, don tunda ya fita bai dawo ba, Baraka da Amirah ma ban kuma ganinsu ba, gani ga kakata sun gayawa dangi da yan uwa,washe gari da sassafe ina barci naji ana shafa kaina. Bude idanu nayi na ganta na zata Hajiya ce sai na lura ita bata kai Hajiya girma ba, murmushi da hawaye cabe-cabe a idanunta, tashi zaune nayi a hankali na ce mata. "Mama!" Rungume ni tayi, tana kuka ina kuka. "Kiyi hakuri Kiyi hakuri na tafi ban ce kome ba"
"Babu kome Mamana." Haka muka yi ta kuka, har dare ina dakin can aka kawo min Amirah. "Yarki ce? Kin yi aure ne?" Girgixa kai nayi na ce mata. "Eh Y'ata ce amma bani na haife ta ba." Ina lura da hawayen da ta sauke har suna gudu. Haka muka ci kuka muka godewa Allah.
Bayan kwana ɗaya, aka ce baki daga Nijar zasu zo haka kawai naji gabana yana faduwa, wurin karfe biyar muna falon da Yazid da yayi kewata, muna zancen mu na masoya, ya ce min.."na gayawa Malam ina sonki kuma kin ce na fito har mun yi magana da Babangida, amma Malam bai ce min kome ba sai murmushi da yayi min ina cikin damuwa."
"Kada ka damu..." Ban karasa abinda zance ba, naga Majid a kanmu. Murmushi yayi yana faɗin. "Ashe kanwata ce nake tare da ita, sakatariya maza ki haɗawa Yayanki Tea."
Banza na bawa Ajiyarshi, Yazid ya mike yana saka hannu a cikin aljuhun wandonshi na rako shi waje, "Zahrah ina ganin kamar ba zan same ki ba."
"Kada ka ce haka."
"Majid;" ya faɗa da sanyin murya, "ina sonka, ina kaunarka yau zan gaya maka ina sonka." Na fada cikin matsanancin kuka, shafa sajenshi yayi yana faɗin. "ranar da aka kai min ke ba zan barki ki huta ba."
Rufe idanu nayi tare da juyawa da gudu, yana dariya. Wato lokacin da suka iso ganin Aamirah da Baraka a falon Goggo Sume haka yasa suka san nice bakuwar, shi kuwa uban rawan kai ya zata daga ni sai malam ne yana zuwa ya ga ni da Yazid ne, shine bari ya zuba min iyayi. Shi gashi nan zanzalale kaudadde.
Lokacin da na koma zauren zan shiga cikin gidan ta zauren ya ce min. "Ni da shi waye yafi wani a wurinki?" Daidai malam zai shigo zauren.
"Sake ni na wuce."
"Ba zan sake ki ba, ki gaya min meye ya fini da shi? Ni fa dan uwanki ne? A Yanzu da kika gano dangantakar mu ba zaki kauna ce ni ba?"
"Ko ɗaya, kai matsayin da na.baka Yayana ne shi kuma matsayin da na bashi abokin rayuwata ne, idan na aureka me zan kira auren da shi? Auren dole ko na tausayi? Ko auren tilastawa? Ka gane ni ina son Yazid ne ko babu kome kayi min wani alkhairin da ba xan manta da shi ba, amma Yazid yafi cancanta a rayuwata."
"Zahra ni dan uwanki ne?"
"A bangaren auratayya ana ajiye dangantaka ayi batun auratayya ni shi nake so!"
"Zahra ina sonki!"
"Kayi hakuri!" Na faɗa tare da juyawa na fita daga zauren, juyawa yayi ya kalli Malam. "Ina sonta, Malamijo!"
"Koda ƙaddarar ku daya, zan nime Allah ya bata wanda yafi kwanta mata, ita mace ba a mata dole, idan ka iya bakinka da kokarin niman yardar ta Allah ya taimaka, idan kuma taki duk da ƙaddara ɗaya ce, zan bata wanda take so."
Hankalin Majid ya sake tashi, sai.dai yanayin yadda ya rayu yasa bai da wani hanyar da zai tankwarani, Malamijo yasan abinda yake faruwa, sauran yan gidan babu wanda ya sani asalima a gaban kowa lafiya lau, amma ni da shi bamu ga maciji.........300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB260
A wannan duniyar babu abinda bazai baka mamaki ba, wai Hajiya take kula dani a matsayin nata, haka Anisah da Zaytoonah. Kallonsu nake kawai. Da suka matsa min na daina zama a cikinsu gara Jamilah da Amaan, idan ka ga ina Dariya tow daga kakannina sai Jamilah da Amaan, sai ko Yazid, kiri-kiri na nuna musu bana tare da su.
Chapter 111 · 0% Book details