← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 138

Sashe 67

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau ban shigo ba sai karfe goma, ina shiga department ɗinmu na ganshi dauke kai nayi kamar ban ganshi ba, koda na kusan wucewa ya ce min. "Zahra Buba!" Juyawa nayi nace mishi."Ni!" Tasowa yayi daga inda yake zaune ya ce min."Bayan ke akwai wata Zahra Buba ce?" Share shi nayi naki magana. "Ok! Dama akan yanayin gari ne ya kike?" "Bashi ya kawo ni ba." Na fada ina karawa gaba. "Ai naji labarin baki da miji zaman kanki kike." "Ina baka shawara da ka kiyaye kanka da bin rayuwar wasu, bin rayuwata kamar wasa da wuta ce."
"Ai na zata wasa da mutuwa ce."
Murmushi nayi na ce mishi. "Ban yi wannan wayewar ba, amma ka tsaya a matsayinka."
"Ok zaki gani, wallahi matukar kika yi wasa sai na baki mamaki."
"Ina mai baka shawara kada ka bani mamaki, kayi harkar gabanka nayi tawa."
"Mtsew dani kike zancen."
Ban kula shi ba, na wuce aji abina na gama abinda nake muka fito. Bayan nan aka sanar da mu dawowa makaranta sallah da kwana biyar.
Haka muka bar makarantar, zuciya ta tayi min dad'i. Ba karamin dadi ba fa. A wurin ajiye motoci na ganshi, sai da gabana ya fadi. Sai da na isa jikin motar ya wani fisgo ni. Fitowa Badar yayi ya zagayo ban san me yayi mishi ba, sai dai naga ya sake ni da sauri. "Madame shiga gani nan zuwa." Shiga motar nayi babu musu. "Kayi hankali ba kowane abinci ake ci don koshi ba, akwai abincin da a madadin yayi maka dad'i, guba ce domin kashe ka zai yi. Nasan labarin kowa a cikin makarantar nan. Hmmm kace me?"
"Ban ce kome ba!"
"Yayi kyau, ko a hanya ka ganta ka kiyaye abin da zai saka ku had'a idanu. Ni nayi maka da sauki idan da wani ne tuni ya tashi kanka." Daga haka ya juya wurin motar ya shiga ya bar shi a nan tsaye, nima nayi mamakin me yasa yayi laushi lokaci guda, haka muka bar makarantar. Alhamdulillahi Yazid ya kare min mutuncina da kimata, yadda yayi alƙawarin. Abin ya tab'a ni da yasani kuka ban sani ba, baya raye amma babu wanda ya isa ya min barazana a kyale shi. "Meye alakarka da Yazid?"
Juyawa yayi ya kalle ni, kafin ya cigaba da tuki. "Sultan zaki ce, idan ba Sultan ba. Ba zan iya baki amsar tambayarki ba."
Ya fada yana cigaba da tukin, "Sultan kuma?" Na kuma tambayarshi, bai bani amsar ba domin har mun iso gidan. "Sultan! Waye Sultan Yazid?" Murmushi yayi sannan ya ce. "Mun iso gidanki.....

```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available da saukin price
Huluna da Mayafai,na manya da na yara sai Wanda ranku yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shaddodi na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya mun tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayanmu na Uwayen gida da Amare ne```
*TUNTUBi WANNAN NUMBER 08130269641*
Leshi
ATAMFOFI
SHADDODI
Materials
Kayan yara
Veils
Huluna....etc
#Mai_Dambu...

*BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

Sorry Dearest yau babu editing 🥰❤️.
*033*
Jikina a matuƙar mace na fito daga motar, "Waye shi?" "D'a ne ga sarki Hamir Julaibi na kasar Algeria!" Bakina na rufe, jikina ya dauki wani irin rawa. "Me?" "Na gaya miki gaskiya." Juyawa nayi tare da barin motar, ina shiga falon na zube kamar wata matacciya, domin kuwa Yazid yana kashe ni da Mamaki,idan nace ban jijiga ba kayi karya. Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tashi nayi da gudu zuwa dakina na shiga banɗaki na bude ruwa a kaina, zama nayi can gefen can banɗaki. Yadda na ke kuka ni kaina ban san akan me yasa nake kuka ba? Kukan me nake yi? Kukan ya boye min waye shi? Ya cutar dani ta hanyar boye min kanshi. Ban iya tsinanawa kaina kome ba, har aka sha ruwa tea nasha, sai kunu da kosai da na sha, da dare yayi na ta fasa indomi da kwai, na koma gefe ina ci ina hawaye. Da asuba kuwa sahur nayi da tea kawai.
Washi gari wuni nayi kamar mara lafiya, ban kara wani walwala ba domin na sha mamaki.
***
Tunda aka kawo shi asibitin, suke ta fama da lafiyarshi. Domin hankalin kowa ya tashi yadda yake duhu da fama da rama. Shafa kanshi Aryan yayi cikin tausayi. "Amaan" bude ido yayi yana kallon Aryan ɗin da yake kara shafa kanshi. "Me ke damunka?" Yana son magana amma babu bakin magana, haka kawai aka same shi a tsakar dakinshi yashe kamar matacce, haka yasa suka kwaso shi zuwa asibiti sai dai ko da suka zo an bincikar lafiyarshi ne. Tunda Majid ya ganshi yasan bai da lafiya boyewa yake, a binciken da suke ne aka gano aikin da aka mishi na cikin, Jamilah ta fito daga Lab rike da wasu takardun tana faɗin. "Hamma babu aikin basir. Akwai abin da Amaan yake boye muku wallahi." Amsar takardun Majid yayi suka wuce office dinta, shiru tayi tana kallon shi kafin ta bude baki zata yi magana ya ce mata. "Allah ya kyauta meye a cikin test din jininshi?" "Sakamakon bai fito ba" ta faɗa a hankali tana wasa da pen din hannunta. A nutse yake kara kallon takardun hannunshi, yana jin kamar ya fasa ihu ne ko kuka. Mikewa yayi ya nufi dakin Amaan. Yana shiga ya samu Aryan yana rike da hannun Amaan din. Shi kanshi bai san irin kallon da yakewa Amaan din ba, shin tausayi ne ko takaici ne? Domin bai kawo lalacewar shi zata kawo har haka ba. Dakyar ya bude baki ya ce mishi. "Tun yaushe ka fara...." Turo kofar da aka yi yasa shi shiru ya zubawa Hajiya idanu, "Majid meke damun Amaan din ne?" "Ciwon ciki ne, tare da borin jini!"
"Ban gane ba." Hajiya ta fada a rikice, "Hajiya zaki gane, bari a gama bincike." Inji Aryan yana kallon Amaan, shigowar Jamilah yasa Majid suka kara fita, nan suka kara rikicewa kamar zasu tashi sama, domin ciwon sanyi ya shige shi sannan jikinshi zai iya daukar kowani mahaukacin ciwo matukar ba a kula ba. Haka yasa bakiɗaya Majid ya shiga wani irin d'imuwa da tashin hankali.

Duk Familyn Ba'are babu wanda zai zo ba, domin Amaan bai da wani matsala da su, dake wawa ne yana shiri da kowa, haka yasa aka yi ta zuwa gaishe shi. Bakiɗaya ruwan kan Majid ya kone, taya zai gayawa Hajiya Amaan luwadi yake bai san da wata kalamai zai iya gaya mata ba, kallon Jamilah yayi yana faɗin. "Kada ki sake Hajiya ta ji labarin halin da yake ciki. Ki bari zan ji da kome." Numfashi ta ja tana kallon shi kafin ta daure ta ce mishi. "Hamma" "kada ki damu zamu yi magana da Aryan." Ya furta tana lashe bakinshi da ta bushe. A hankali ya a nufi hanyar waje, yana nazarin abinda zai fadawa Aryan domin bakiɗaya ya tattara damuwar ya azawa kanshi. Don yasan matuƙar Aryan da Hajiya taji sai zuciyarta ta kusan bugawa, ya kuma san idan aka gayawa Aryan kamar an gayawa Hajiya ce.
Murmushi Hajiya Tani tayi tana kallon, videon Amaan tana faɗin. "Wannan lokacin ya dace na tashi kan Sa'ah." Shan ruwa da yake gaban shi Sajid yayi yana faɗin. "Hajiya Sa'adatu ta kare mata, dole ta biya abin da ta saya."
Suka fada suna dariya, "Meye tsakaninka da Afiyyah?" Ware idanu yayi yana fadin. "Ba wani abu fa, chill out muke da ita kuma nasan an dauke ta aiki a kamfanin Ba'are."
"Lallai kwanyarka bata ja Sajjid, taya zaka fara wannan aikin." D'aga kwalba yayi yana faɗin. "Bana kuskuren harkalla, duk abin zan yi Hajiya da tsari a cikinshi. Yarinyar ita ce Bingo dina, tana sona ina bata abinda take so. Sannan zan san yadda zata matsa jikin Chairman din kamfanin yadda zan basu mamaki."
Murmushi Tani tayi tana faɗin. "Yaro yaro, ni na gama shirina saura ja jira tashin bom."
Ta fada tana dariya, tare da barin falon. Da sauri ya bi bayanta yana faɗin. "Hajiyata me kika shirya?" "Lokacin da zai faru zan gaya maka, domin ni kome nawa da tsari bana faɗar tsarina kada a samu matsala. " Hura iskar bakinshi yayi yana faɗin. "Ni dai ki gaya min shirinki, domin kuwa ba mamaki na tayaki."
Chapter 67 · 0% Book details