← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 138

Sashe 34

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Lokacin da suka isa gidan, ba laifi ana ta hada-hada, falon Alhaji Mamman suka nufa suka gaishe shi sama sama ya amsa. "Kai me yasa meka?"
"Ba Barawon can bane ya dawo ya targad'a min kafa ba."
"Waye barawo!"
"Abdul Majid!" Wanda ya shigo falon, mikewa Alhaji Mamman yayi ya ce. "Sa'a me yasa kika kawo min shi gidana!" Juyawa yayi ya bar falon. Ai kuwa garin bashi hakuri ya rufeta da duka, har waje. Wannan abin ko a jikin Amaan domin shi gani yake Hajiya ta rabasu da jin dadin gidan Ubansu ta kawo su wata duniya suna wahala. Shi yasa duk abinda Alhaji Mamman zai mata baya tausayinta ko kaɗan.
Da gudu Anisah ta fita waje, "Hammayo kazo Alhaji xai kashe Hajiya." Sun saba duk lokacin suka zo haka xai mata duka a gaban jama'a. Amma na yau ya wuce tunaninsu domin biki ake yi a gidan, kuma ga mutane babu wanda ya damu sai ma tsayawa da suka yi suna kallon abin. Haka ya ratsa taron ya shiga. Ya rike hannun Alhaji Mamman Ba'are da yake zuba mata duka. "Ya isa haka!" D'ago kai yayi yana mamakin waye ya isa ya dakatar dashi daga dukar Sa'adatu. "Ya isa haka Alhaji Mamman Ba'are!" Ya sake hannun shi yana kallon cikin idanunshi. "ya isa haka nace!" Ya fada yana me dago kai yana kallon Hajiya Nana. " Na rantse da Allah,duk ranar da danki ya kuma d'aga hannu ya tab'a min Uwa, sai na hauro sama na bugaki da kasa daga saman zan wurgo ki billahi azim, Uwa bata fi Uwa ba duk sunansu Uwa." Ya faɗa yana d'ago Hajiya. ""Kai waye ya baka damar shigo mana gida?" Inji Sajjid Mamman Ba'are, cikin wani irin fushi, ya juya ga Sajjid wanda ganin idanun Abdul ya bashi tsoro. Ƙwayar idanunshi a fusace yake fushinsa daga zuciya take kunno kai ga idanunshi, kamilalliyar fuskar shi bata nuna fushin ba..
"Kace me?"
Hadiye yawu yayi, ya juya ga Alhaji Mamman Ba'are zai magana Hajiya ta ce mishi. "Kul ka kara magana!" "Hajiya idan ya kuma dukanki sai kashe shi, Nana kin ji me nace." Ya fada da karfi, juyo shi hajiya tayi ta watsa mishi mari, ta kuma marin shi. Jikinshi ya hau cira kamar zai tashi sama. "Ban doraka akan haka ba,me yasa zaka min haka?" Inji Hajiyar tana kuka."Mahaifinka ne me yasa zaka mishi haka a gaban jama'a?" Zube gwiwarta tayi ta ja hannun Majid din, sai yaki. "Ki cewa danki ya fita na tsame shi cikin zuri'ata."
"Haka yayi ai dama kafin yau ni ba danka bane."
"Ba zai fita ba, rashin kunyar da yayi sai Uwarshi ta biya akan idanunshi." Jin Nana tana saukowa. A fusace yayi kanta tare da tsare ta da idanunsa masu Bala'in ban tsoro. Da gudu Hajiya ta rufe shi da duka, "ka bar tashin hankalin nan, ka koma inda ka fito na roke ka, don Allah na roke ka ka tafi ka yi nisa da mu na yafe maka zuwan."

Juyawa yayi zai tafi Nana ta dauki sandarta ta shiga bugawa Hajiya, "Hammayo tana dukan Hajiya" bai ce kome ba, ya nufi falon Alhaji Mamman ya ce mishi. "Ka fita ka jawa Mamarka kunne ko na kona gidan nan baki ɗaya wallahi billahi azim." Ya fada a haukace, zuwa yanzu shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are tsoron Majid ya darsu a zuciyarshi. Ganin yadda ya fita da gudu, inda motar gidan take ya nufa, ya cire rigarshi ya bude wurin tanki, ya saka rigar sai da ya jike da fetur, ya Ciro yana watsawa a kan kome na gidan, "Hajiya kyale ta don Allah." Alhaji Mamman Ba'are ya fada, sannan ta tsaya tana hakki. "Me yasa ka dakatar dani?"
"Saboda d'anta zai aikata kome don mahaifiyarshi."
"Kenan idan aka dake ta zai dau mataki?"
"Zai aikata kome.ma". Ya faɗa yana kallon yadda Majid din ya d'ago Hajiya suka dauki kayansu, suka nufi gidan. " Ita da Yaranta su zauna a gidan shi ya bar magana gidan mu!" Inji Nana domin ta shirya sai Hajiya ta biya abinda Abdul Majid ya aikata musu.

Suna da kudi suna da karfi, Majid ba xai zubda musu kimarsu ba. Don haka suka hana Hajiya tafiya, suka sakata a gaba. Shima Majid din kin tafiya yayi yana tsaye a kofar gidan, yana jiran ganin ko Aryan ne, suna can Alhaji Mamman yasa Hajiya a gaba da cin mutuncin, har aka gama bikin cikin kuka take, karshe ma turawa maradi yayi aka rufe gidan wai kada Majid ya tafi can ya zauna.

Shi kuwa rubuta wasika yayi ya bada aka kaiwa Hajiya da ban hakuri,

Bayan tafiyarshi da wata biyu, Alhaji Mamman ya yanke mata rabin wahala ya sakata a gaba ta fara zuwa aikin kamfaninshi. Da iliminta da kokarinta ta fara aiki inda ta fahimci wasu na azurta kansu da dukiyarshi, don haka ta fara aikin binciken anan ta gano har da hannun Alhaji Haladu da Kamilu. Ta mika mishi duk wani abinda ta tattara, sannan ya ce mata. "Ki saka Yaranki a gaba su koma makaranta, naji ance wancan dan mahaukaciyar, likitanci yake karantawa. Tow sai ya cigaba amma ya sani ko ya gama karatun anan zai yi aiki xa a fara gina mishi asibiti."
Zuwa yanzu baya shakkar mutuwa dama abinda yake so ya samu, Yaran hajiya zasu iya tsaya mata, duk da yasan yayi kuskure amma a yanzu yana da damar barin mata kome domin shima yanzu ya san girma ya cimma shi.
Majid da y koma sai da yayi jinya, a haka yake karatu, bayan wata uku aka kawo shi har marad'i, don bai san waye akanshi ba, abu daya yake faɗa sai na kashe ka idan ka tab'a min Mamata. Hajiya bata iya ganinshi a wannan halin ba, kamar an mata bushara ta wuce da shi wurin danginta,. A can ya zauna har ya samu lafiya sannan aka yi cuku-cuku ya dawo nan da karatu, amma abin ya zame mishi cutar damuwa dan mental health ɗinshi ya tabu, don ma Kakanshi yana tsaye akanshi da sauran dangin Mamarshi haka yasa shi ya boye yadda yake shan wahala, ya cigaba da karatunshi....
Bayan shekaru bakwai.....
#Dambuje
[2/18, 11:33 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*017*
Bayan shekaru bakwai.
Duk da wannan shekarun zaka dauka Hajiya ta huta daga jidalin dangin Alhaji Mamman Ba'are, amma ina domin bala'in ya kara hauhawa ne bayan Alhaji Mamman Ba'are ya nad'ata sabuwar shugabar kamfanin ya sauke wanda yake kai ya dorata, ai kuwa sai gashi fitina ta kunno kai, daga kamfanin har gida bata da sukuni.
Chapter 34 · 0% Book details