Sashe 115
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Kiran Yaya Babangida nayi na tambaye su suna wane asibiti, ya fadamin haka muka nufi asibitin. Koda mukaje sosai ake dubata, ina zaune sai hawaye ke zubo min. "Amma matar nan bata da hankali ne ko?" "Da hankalinta tsabar mugun hali ne." Na gaya mishi, ina share hawayen da yake zubo min, "Ba iya Zuzu ba hatta Mama sai da ta sha wahala a hannunta, duk wanda yake inda Addah take sai ya sha azaba, don haka kada kayi mamakin abin da take yi domin kuwa zata aikata."
Haka ya saka ni a gaba muka yi ta hira, koda yake ba wata hira ba ce, amma kamar dama yake nima irin wannan muyi magana, Aamirah kam sk Lamido ya dauke ta, ko ya lura Majid din yana son magana da ni ne oho, a yau na gaya mishi abubuwan da suka faru tun daga Fatakwal har zuwa yawon da nayi, rintse idanun shi yayi tare da dunkule hannun shi."Kina son zaman nan ko zaki tafi?"
"Zan tafi idan ta farka." "Me yasa da muka hadu baki gane ni ba?"
"Taya zan gane ka? Bayan ni kaina ba gane kome nake ba, fatana na gudu daga masifar mutumin nan."
"Na zata baki da yarda ne?"
"Ina da yarda amma ba akan kowa ba." Na fada ina mikewa,.kusan kwana muka yi a asibitin, kafin ta farka kallona tayi. "Baki tafi ba?" Girgixa mata kai nayi "ina xan je? Bayan baki da lafiya."
"Nayi kuskuren da na saka ki a damuwa, Aamirah bata da uwar da ta wuce ki,.ki tafi da ita ni nasan...."
"Dangin Babanki suna Gombe a kumo, na san idan kika je can kome zai zo da sauki. Idan kuma zaki bini kamaru ne ba kome muje."
"Zahra zan bi ki" ta faɗa hawaye na zubo mata, rungume ta nayi ina shafa bayanta. "Zahra na gaji, so nake na mutu na huta., Hawaye ya cigaba da kwaranya daga idanuna. "Muna tare Aamirah tana bukatar kanne daga wurinki da wurina." Na faɗa ina kuka. Murmushi Majid yayi yana shafa kanshi. "Tayi kukan mutane, nata kukan ta shanye shi kamar ba kuka ba.
Haka yasa shi jin ta ƙara samun matsayi a zuciyarshi.
Bayan sallar asuba, aka kawo mota muka wuce Gombe, karfe biyu muka shiga garin Gombe kafin muka wuce nafada, wurin karfe biyar muka isa garin su Babanta, lokacin da suka ganta ba karamin farinciki suka yi ba, ranar mun sha kindirmo kamar me, kwanan mu uku saboda jikinta Majid ya saka mu a gaba har Kamaru, inda SK Lamido ya ce zai kawo Aamirah, tunda muka isa ake zirga-zirga akan Zuzu. Da gaske bata da lafiya, domin zuciyar ta kamar zata buga, saboda masifar Addah.
Haka ta cigaba da jinya, har Allah ya bata lafiya satinta daya. Hmm ko kunsan Majid tattarowa yayi ya dawo gidanmu da zama, Zuzu kuwa idan ta ganshi tayi ta dariya tana faɗin. "Wai Hamma Majid ba zaka koma nijar ba ne?"
"Zuzu babu ruwanki da ni." Yake fada yana kallona. Ni ban kawo don ni yake zaune ba, kawai dai na ga yana zaune a gidan ne wurin kanwar Mamanshi. Watan shi biyu da zuwa Zaytoonah tazo. Da farko na zata kamar zata sake don ina yar uwarta ne, a'a sai daga baya na gane ba haka ba ne, harkar gabanta daban tazo yi, ina ban daki na fahimci haka domin tazo tana ta rusa kuka, kuma bata zata ina ban dakin ba, ko nace basu san ina ciki ba.
"Kiri-kiri kina nuna min kin tsane ni,ita farincikin da kike bata Allah kaɗai ya sani, ni kuma kin barni a can"
"Tow ki dawo nan sai na hada Ku na baku farincikin ba shikenan ba!" Inji Mamanmu.
"Tow ki mishi magana." Ta fada da kuka, "Mahaifina bai tab'a zartas da hukunci nace ga abin da yayi min ba,.ya sha gaya min babu alaƙar aure a tsakaninki da shi don haka ni ba zan mishi magana ba, domin ya gaya min gaskiya.baya sonki."
"Mama Babu adalci cikin wannan al'amarin."
"Duk abinda kike so ki faɗa."
"Ita da ta gama yawon Duniya za a dauki mutumin kirki....." Tass ta tsinka mata mari, "Akan me? Me tayi miki? Haka kawai zaki tsane ta ai an gaya min abinda kikayi ta mata a nijar wallahi kika sake wani abu ya haɗa ku sai na sab'a miki."
Ta fada tana nuna mata waje,.fita tayi da gudu tana kuka,tabbas abin akwai ciwo. Duk da ban san akan me suke Maganar ba, amma a hankali na bude kofar na fito. "Mama me tayi kika dake ta? Me yasa zaki dake ta?" Ita aka mara ni nake kuka wiwi. "Fita ki bani wuri sakarya mara zuciya." Haka na fita na shiga dakin mu, Zuzu da take saka jan farce a yatsun Aamirah na kalla harkar gabanta take ga Zaytoonah na kuka. "Zay!" Riko ni tayi, "kyaleta tayi abin ta, kowa ya debo da zafi bakin shi." "Kanwata ce fa!" "Sai me? Kashin awaki kukayi kuka fito shegen shisshigin da yake ja miki bakin jini da tozarci."