← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 138

Sashe 47

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin yadda yake barci yasa baki daya aka yi shiru, babu wanda ya kara tada zancen. Asalima kowa tausayin Hajiya suke ji hatta Amaan da yake ganin duk wani abinda ya faru da laifin Hajiya tun farko. "Tow ki daina kuka mana, ba gamu a raye ba, idan mutuwa aka ce zai yi ai kowa ya huta." Juyawa Aryan yayi yana kallon shi. "Dadina da kai baka boye waye kai? Gab'o kawai." "Kai waye gab'o." Ya taso a fusace. "Idan bakincikin Mamman Ba'are bai kashe ni ba, bakincikin abin da kuke aikatawa ya isa ya kai ni kabarina, don Allah ku bari." Ta fada tana kuka. "Hmmm Alhaji meye kuskurena akan Yaran nan? Jama'a su jefe ni, suma su koma gefe suyi dariya, Alhaji idan nace maka bana jin dadin rayuwata zaka dauka rashin godiyar Allah ne ko? Tow wallahi bana jin dadin rayuwata." Ta fada tana kuka, "sun mai dani mahaukaciya, basa jin magana ta, basa son junansu kamar su kashe kansu suke ji don Allah ya ake son nayi?" Baki daya sai jikin kowa yayi sanyi. "Alhaji da zaka Duba zuciyata, Yarana ne a cikinta,, ina son su hade kansu ina son na gansu cikin farinciki. Ina son nayi alfahari da haihuwarsu, sai dai idan na cire maka Aryan da sauransu, Amaan zai kashe ni. Bakincikin shi zai kai ni lahira ban shirya ba. Amaan ya zame min wake daya me kona gari." Yadda take kukan kawai xai saka kaji kamar ka tayata. "Ban san meye nayi mishi na kuskure ba, ya tsani yan uwanshi mata da maza ba, Alhaji Abubakar na hakura da kome na zauna da mutumin da ya haife ni kasan ba karamin al'amari ba ne. Mace ta zauna da namijin da tasan bata sonshi. Kuma ta zauna akan babu yadda zata nime hakkinta. Alhaji amsar ƙaddarata da nayi hannu bibbiyu shine laifina ko zama da nayi nai ta haihuwarsu!" Yadda Hajiya take kuka yasa bakiɗaya tashin hankalin da suke ciki ya nunku. "Idan da ace Amaan yana da adalci ba zai tab'a had'akai da makiyana ba, nawa zasu bashi? Nawa suke da shi? Bana son nadama tazo mishi bayan ya haɗakai dasu sun kashe ni."
Yadda take kuka yasa Majid ya tashi da matsanancin ciwon kai, wanda yasan baya raba daya biyu jininshi ne ya hau. Hajiya bata fasa fadar abin da yake damunta ba, tana ganin idan bata fada ba, tabbas kafin su koma Niamey ta mutu, shi yasa ta hakura ta fadi abinda yake damunta ko zata samu sauki. Kuma bata fasa fitar da abinda yake ranta ba, domin taji sauki kuma Allah ya taimaka tana faɗa tana jin kamar ana zare mata k'ayar da yake ranta, ruwa Aryan ya mika mata, ta amsa ta sha sannan ta sauke ajiyar zuciya. "Allah kagani na fita hakkinsu, saura su ya rage su futa nawa."
"Kiyi hakuri Hajiya, Indai aure kike so nayi zan yi in sha Allah." Inji Majid yana dafe kanshi, "A'a Majid kayi yadda kake so, ba sai kayi auren ba, tunda baka da lafiya." Ta fada tana share hawayen da yake zubo mata, "Aryan don Allah kai ni, asibiti kada na fadi don zan iya samun shanyewar b'arin jiki." Ya fada kamar zai fadi, da sauri ya tare shi, suka bar falon Hajiya tana me bin su da idanu, don a tunaninta shirinsu ne suyi wasa da hankalinta. Sai da ta ga sun tafi baki daya, sai Amaan kaɗai ya rage, yana son ya hada rigima. "Ba wani ciwon da yake damunshi, kawai renin hankali. Fisabilillahi Hajiya kina ji kina gani wai board director aka bani?" Sai kuma yayi kasa da murya yana faɗin. "Hajiya Chairman bai yiwa Aryan girma ba? Ki ga fa Yaro ne? Sannan."da
"Duk da Yaro ne bai saka dukiyarshi gaba ya lalata ba, har yau bai tab'a kaso biyar na dukiyar shi ba, kai ina naka dukiyar? Wai me kake yi da kudinka?"
Shiru yayi yana kallon yadda take tsare shi da idanu. "Wato Hajiya " "ya isa haka! Kada ka kara kawo min sukar kowa sannan da na san board director za'a a baka wallahi da sai na hana a baka, domin ba zai yiwu a dauki jahili a bashi abin da ba zai iya rikewa ba "
"Allah ya baƙi hakuri Hajiya, naga kamar ranki ya b'aci "
"Hakuri shi ya kashe Uwar jaki." Yadda tayi maganar yasa shi kame kanshi kada Hajiya ta kara fusata.
----
A can Asibitin kuwa, Mahdi shi ya musu jagora aka kwantar dashi bayan an saka mishi ruwa. Likitan da ya duba shi ya fito yana kallonsu kafin ya ce su same shi a office ɗinshi. Bayan sun shiga ya zauna yana ta rubuce-rubuce. Kafin ya d'ago kai domin har Aryan ya gundura da zaman ya ce musu. "Gaskiya jininshi ya hau, don Allah a bashi lokaci ya huta, idan kuma yana da mata tow a dan janyeta daga gare shi, a nisanta shi da hayaniyar mutane."
"In sha Allah!" Suka faɗa, kafin ya ci-gaba da cewa. "zamu sallame shi nan da kwanaki uku, domin jikinshi yana ƙarƙashin kulawa ne. In sha Allah zuwa nan da wani lokaci zamu sallame shi." Haka suka yi ta godiya, sannan suka fito.
"Hajiya Sa'adatu tayi hakuri da maganar auren nan, Yaron nan yana buƙatar nutsuwa."
"Abba me yasa ba zai yi auren ba?" Kallon shi suka yi ta window, Alhaji Abubakar Abzin yana tuna ranar da ya kai mishi ziyara da yadda aka fito dashi baya iya tafiya. Sai riko shi aka yi. Idanunshi ne ya cika da kwalla. "Ya hadu da hatsari ne, bayan an kai shi gidan horon, Yaran da suka fi karfinshi suka mishi duka tare da doke mishi gabanshi. Wanda sanadin haka gaban ya mutu."
Rufe baki Aryan yayi da karfi jikinshi yana rawa, hawaye na zuba mishi kamar mace haka yake kuka yana kallon dan uwanshi. "Hammayo ba xai tab'a zama da mace ba kenan?"
"Gashi nan dai, bamu sani ba ko Ubangiji zai yi ikonshi, amma Abdul Majid yana cikin jarabawa." A hankali ya fashe da kuka, yana jin wani irin tausayin dan uwanshi. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ubangiji mun gode!" Ya fada Aryan akwai karyayen zuciya, haka yake ga saurin kuka kamar mace, gani yake kamar dan uwansa zai mutu da damuwar lalurar.
Shi yasa yake nisanta kanshi da mutane, baya yarda ya zauna da kowa rayuwarshi cikin duhu, akwai wani irin shakuwa tsakaninshi da duhu tun yana Yaro, gashi ya girma da wannan trauma ɗin. A rayuwar Abdul Majid bai san soyayya ba, bai samu soyayya ba, ita kanta Hajiya ta haifi Majid ne amma bata damu da damuwarshi kamar yadda ta damu kanta da yayi aure ba.

Duk laifin abinda ya same su, laifin Alhaji Abbati ne, da bai saka Hajiya a cikin caca ba da babu yadda zata hadu da mahaifinsu ya kashe rayuwar dan uwanshi haka,. Sai yanzu yake fahimtar me yasa Majid ya tsani dukiyar Mamman ba'are, asalin don a gina duniya da dukiyar aka lalata musu rayuwarsu. Cikin shashekar kuka yake faɗin. "Saboda hab'aka dukiyarshi ya lalata rayuwar wanda babu ruwanshi."
"Asibiti muke kayi hakuri ka bar wannan zancen." Haka suka cigaba da zama har wani lokaci kafin Alhaji Abubakar da lauya suka bar asibitin tare da Mahdi,. Suka tawo da Hajiya tare da abinci, mika mata kome Aryan yayi sannan ya koma gefe yana kallonta, ajiye takardar tayi ta zauna tana kallon Majid. A hankali hawaye yake zuba mata, wannan wacce irin rayuwa ce? Me yasa kome yake zuwa mata haka? Me yasa daga wannan sai wannan? Shin anya bata yi wani laifi Ba tare da ta saninta ba.
Su da suka zo da zimmar kwana ɗaya, sai gashi sun kare da dibar kwanaki har sama da biyar, a na shida aka sallami Majid din, ba laifi ya ɗan samu sauƙi. Kuma dama yanayinshi ba mai yawan walwala bane, sai abin ya kara yawa. Ita kanta Hajiya ta damu sosai kamar ta cire ciwon. Haka suka tawo Niamey zuciyarta babu dad'i.
Lokacin da suka isa gidan A tsakar gida suka hadu da Nanah, tana jin rigima. "Ya zamu yi da wannan tsohuwar?" A hankali ya fito yana tafiya, kamar ba zai taka kasa ba, saboda rashin karfi da kuzari. "Kai Alhaji!" Ta fada tana mikewa tare da dogara sanda har inda yake ta ce mishi. "wallahi ka sake ka mutu sai Allah ya mana hisabi. Kai ma mutuwa zaka yi?" Ta faɗa, yadda tayi maganar zaka fahimci bata cikin nutsuwarta. "Munafukan can ne suka kaika zasu kashe min kai ko?" Kasa magana yayi yana kallon yadda take fada. "Nana likita yace a barshi ya huta." "Muje daga yau ni zan yi jinyar shi " duk da bata kaunarsu amma a lokacin da takira Hajiya take fadan ba zasu dawo bane, an barta kamar ba a damu da ita ba, gashi kayan abincinta ya kare, babu nama babu kome Haladu da Kamilu sunki saya mata, me take nufi na dauke mata Aryan shi ko zata mishi meye baya fasa saya mata kayan abincin.
Chapter 47 · 0% Book details