← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 138

Sashe 132

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'ago kai nayi na kalli Admin da sauri ya boye kanshi, na wuce abuna Amaan da zai tafi gida muka tafi tare. Anan na bar Aryan ina shiga da gudu Alfah ta zo ta rungume ni. "Ina sonki love!" Na fada ina sumbatar goshinta. "Hmm! Yar nan ya aiki?" ,"Alhamdulillahi Nanan Alhajin Allah, nace a kawo miki kilishi gobe in sha Allah"
"Allah ya miki albarka!" Ta fada tana share hawayen da ya cika mata idanu. "Ya Allah idan Alhajin Allah yana raye Allah ka bayyana shi idan baya raye Ubangiji ko gawarshi ka bayyana mana!"
"Amin Nana!" Na wuce daki na zube a gado ina ajiyar zuciya. Top din jikina na cire na kwanta ban yi yunkurin cire skirt din jikina ba. Haurowa gadon tayi ta kwanta akan ruwan cikina tana mita. "Love me kike so "
"Haji kuka " Amira tayi baki da wuri amma alfah babu baki sai gwaranci me sifirin, "me ya same ta?"
Wayyo Allah na, da ta buga min wani gwarancin bansan yadda aka yi na tashi zaune ba. "Haka aka yi? Babban magana magajin gari da kiran wambai, tow jeki gani nan zuwa."
Tana fita na tashi na cire skirt daga ni sai dan gajeran wando, na cire shirt din rigar ya rage daga bom short sai transparent bra, sannan na wuce ban daki nayi wanka na fito, sallah nayi domin nayi alola, sannan na fito falo, shinkafa da miyar bindin sa aka yi, sai coslow na zauna ina ci ina jin hirar Hajiya da Amaan, shigowar Aryan yasa muka bada hankalinmu kanshi.
"Hajiya an shirya muku tafiya hutu har Kamaru ma." Juyowa tayi ta kalle ni.
"Me kike nufi?"
"Zaku tafi nan da kwana uku, dukkanku."
"Ke fa?"
"Ina da aiki!" Na fada ina cigaba da cin abincina. Ai kuwa Nana ta fashe da kuka ai babu abinda ya fi haka dad'i. Ina cin abincin na ce mata. "Nana ke da zaki tafi aikin umara sai ki mishi addu'a a can!"
"Haka ne yar nan"
Ta fada tana goge kwallarta.
Da na gama na wuce sama, dakin da yake motsa jiki na shiga na dan kunna walking, don abincin da naci ya ragu don bana son kiba, haka yasa na samu damar yawan motsa jikina. Kuma tun haihuwar Alfah na fahimci cewa tumbi na ba zai koma daidai ba, sai na rage shi.
Ina cikin haka ne Alfah ta shigo itama ta fara nata, ina yi tana min surutu, wasa ta fara a cikin dakin can kamar an ce ta tab'a inda aka saka mirror sai ga kofa ta bude. "Ma!" Dake haka take kirana, zuba mata idanu nayi tana kallon kofar, nima bin kofar nayi da ido, muka tsaya kallon kofar, da sauri na koma na rufe kofar shigowa, sannan na riko hannunta muka shiga cikin dakin. Kunna wutar dakin nayi ina kallon ko ina na dakin, lalube aka rufe wani jikin wani bango ina zuwa na ga hotunan mutane ne. Dake ina yawan nuna mata hoton shi, tana ganin shi ta fara tsalle. "Daada."
Rufe mata baki nayi, na ji wani motsi me karfi, "welcome to Abdul Majid Mamman Ba'are, secret room service." Katon tv ne ya bayyana, sai ga shi hotunan mashigar kamfanin ne ko ina kai tun daga gidan nan har zuwa wajen garin nan bakiɗaya.
Wasu takardun na gani na juya a hankali ina kallon hotunan wurin. "Waye ya kashe Mamman Ba'are da Maysara?"
Hoton Sajjid don dama ban san shi ba, sai da ya saka sunan a kasa, Tani na santa. Tana can kamar mahaukaciya. Kawu Haladu, Kawu Kamilu, Hajiya Hadiza,. yaya Umma. Yaya Ikilima, Yaya Saratu. Hajiya Harirah.
Admin, Commodore Magaji Chindo, Mr Bukola,
A hankali na fara bude takardun. _Koda wata rana zaki shigo nan, ki saka idanu da kyau ki kuma nimo wanda yake da gaskiya ya taya ki wannan yakin._
_Zasu iya tab'a iyalina, domin ban san karfin su ba, amma nasan idan kika nemi Taimakon Yazid zai taya ki wannan yaƙin!_

Wata takardar na kuma dubawa na ga ya saka.
_Zabi daya na dauka sadaukar da rayuwata domin naki da na yan uwana, ki kula da abin cikinki_
Kuka na saka a hankali ina jin wani irin tausayinshi dama yasan haka zai faru ne? Bai gaya min ba. Fitowa nayi na dauki wayata na shiga na dauki videon kome na fito na kira Yazid yana ganin kirana ya kashe ya kirani. Kuka na saka mishi tare da kashe wayar. Sake kirana yayi na shiga mishi bayanin abinda na gani, sannan na tura mishi videon.
"Na jima da sanin haka don ya turo min, ya ce bai san lokacin da zaki iya fahimtar haka ba, yanzu ya ake ciki?"
"Mijina yana raye!"
"Taya zamu tabbatar da haka."
"Hanyar bibiyar Admin!"
"Baki da matsala, yanzu wani sati xan shigo."
"Na gode." Fitowa nayi a dakin na wuce zuwa dakinmu muka ci kuka muka more, sannan na shiga shirya kayan Alfah. Dole mijina ya dawo gare ni, amma kafin nan sai na fara gayawa Allah. Washe gari na tashi da azumin niman biyan buƙata. Na kuma saka ana sadaka, har su Hajiya suka bar garin ban daina ba, karshe na cewa Aryan . "Zan koma hotel da zama, Yazid zai zo wani sati."
Don ban gaya mishi ba, sai dai barina gidan zuwa hotel din ya saka shi zargin wani abu. Amma na share shi don bana son ya gano kome sai Yazid ya zo, kwana na hudu Yazid ya zo a ranar na bude mishi kome, zuba min idanu yayi yana faɗin. "Me yasa baki gaya min ba?"
"Kawai babu kome!"
Nasan yaji haushi amma ya zan yi nima haka nake ji, daga nan muka shiga shiri, na farko shine saka Admin a tarkona yana ganina zai fara zufa, kamar yaga abin tsoro. Kafin nan Alhaji Kamilu da yake zuwa domin ganin yadda kamfanin yake tafiya, shima baya son haduwa da ni,

Wannan yasa lokaci guda Yazid ya kawo shawarar rufe kamfanin na tsawon wata guda, haka kuwa aka yi tare da rufe kamfanin da mashigar kudin kamfanin, a cikin kwana biyu rak aka fara bibiyar Aryan, ya kira ni ya gaya min nace mishi. "Ba kai ba kwanan gida dawo hotel." A gefe guda kuwa Admin muka kama yana ganin mu ya bude bakinshi. "Don Allah ki min rai, wallahi kina bani tsoro ne, idan na ganki kamar na ga mutuwa ta."
A hankali nake murza zoben, zubewa yayi a kasa, yana jin wani irin abu a ranshi.
"Ina kuka kai min mijina?"
"Yana can gidan ajiye kayan da suka lalace."
Juyawa muka yi ni da su Aryan muka fita, gidan ajiye kayayyakin muka nufa, a lokacin aka fara bin motarmu da gudun gaske. Mun isa gidan babu kowa, muna shiga aka rufe get din, har cikin store din muka shiga, anan na fara hango Majid zaune. "Kada ki isa wurin" cak na tsaya ina kallonsu.
"Mijina ne!" Na isa da gudu.
"Zahra!" Ya faɗa a hankali. "Me yasa kika zo ke daya?"
"Bani daya ba ne!" Na fada da wani irin kaduwa. "Ai haka kawai ba zasu baku damar zuwa nan ba, tarko suka shirya muka, kuka fada"
"Soja muma da namu shirin!"
Matsawa suka yi aka shiga dirowa ta sama, a hankali na rufe fuskarshi, jami'an tsaro ne, suka mana kawanya, a hankali naji wani abu me karfi da sauri ya wuce ta kunne na, wanda yasa sani jin wani irin abu kamar an girgiza ƙwaƙwalwa ta, daga nan ban kuma sanin kome ba.

Jin karar harbin yasa Jami'an tsaro suka yi ta dauki ba dad'i, kafin daga bisani aka tsayar da harbe -harbe, a lokacin aka lura da harbin Aryan da aka yi fita da shi aka yi, a daren aka tafi har gida aka kama Alhaji Kamilu da Haladu, Zahra da Aryan aka wuce dasu asibiti, har da shi Majid ɗin da bai da karfi a jikinshi. Sai dai ana kai shi asibiti, aka duba shi Yazid ya nemi su bashi takardun Majid din, ya wuce da shi Algers domin yace mishi. "yadda ka kare kamar kudin guziri gara ka tafi wani wurin kayi jinya idan kayi a gabanta zata kuma shiga wani yanayi sama da baya.
Aryan an samu an ceto rayuwarshi dakyar, amma Zahra kan sai a hankali domin wannan harsashin da ya wuce ta kunnenta yasa kunnen ya daina aiki baki daya, saboda karfin gudun shi.

Kwanan Aryan biyu ya warke tare da mai da hankali akan jinyar Zahra suna waya da Yazid har yana hada shi da Abdul Majid, sai dai a tsawon shekaru biyu ya koma kamar bashi ba, tsabar azabar da suka mishi. Sai da na kwashe sama da kwanaki goma sha biyar kafin na farka, kamar a.mafarki nayi ta kallon kowa, ina ganin bakinsu yana motsi amma bana gane me suke cewa sai na juya da daya kunnen nake gane musu.

Aryan ne ya gaya min na rasa kunnena daya, wannan abin ya dake ni wanda ban san lokacin da na fashe da kuka ba, dama ai idan baka mutu ba, ba a gama maka halitta ba.......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:48] Hlm: BHB276
Wani irin tashin hankali na shiga, cikin d'aga murya don gani nake kamar baya jina. "A haka zan rayu babu kunne ɗaya?" Na tambaye shi, turo kofar dakin da Mama tayi yasa ni sa ke fashewa da kuka ina fadin. "Bana ji da kunne ɗaya, na kurmance." Ita kanta na hango hakuri da juriya a kwayar idanunta, na ga tarin ban hakuri da lamuni fuskarta. Rike hannuna tayi tare da fadin. "Ba dashi Allah ya halicce ki ba, tunda samu kika yi dare daya zai dawo " ta faɗa tana rungume ni, nima kuka nake tare da surutai Shafa bayana take, ita kan ta gaji wallahi gara Majid idan ya warke ayi ta da wajewa, damuwar tayi yawa, ya sakar mata Yarta tunda Aryan ya kira ya fadi halin da ake ciki ya Allah ne da rayuwa, ta ji kamar da ita ce ciwon ya same ta, ba Zahra Yarinyar da bata ji dadin rayuwa ba, tun tashinta. Kamata yayi a ce Zahrah ta san farinciki da jin dadi, amma daga wannan matsalar sai wannan.
Chapter 132 · 0% Book details