← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 138

Sashe 133

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama!" Na kira sunanta. "Ina ihu ko?" Hawayen da take dannewa ne ya zubo mata. "Zahra baki ihu, sai ma magana a hankali." Rike hannunta nayi ina jin kuka yana zuwa. "Shin kina nufin Allah ba zai jarabce ki ba ne? Ko kina son Allah ya fahimci kin butulce mishi ne? Don Allah ki daina kuka ki mikawa Allah lamarinki, yana sane da ke. " Nasiha da ban hakuri babu wanda bata min ba, rarrashi da kulawa babu wanda na rasa, domin nuna min tayi kaf duniya babu irina. Babu kamata, a daren ranar Hajiya da Nana suka iso, fadi take. "Wani tsinannen ne ya boye min Alhajin Allah, Allah ka tsine mishi albarka."
Haka Alfah da tazo ta ganni ina hawaye, ba zan ji sweet voice dinta me cike da gwaranci da kunne duka biyun ba, sai na fashe da wani irin kuka ina me rungumar ta. Sai ya kasance kowa tsoron komawa gida yake don kada su dawo ace musu na mutu ko an sace ni, sannan wani abin da ya kara b'ata min rashin Majid wato nayi wannan sadaukarwa ne don shi amma sai ya tsallake ya tafi nashi sabgar.
A cikin wannan yanayin labari ya zo mana, an kama Hajiya Turai. Da laifin kashe Maysara ita da Alhaji Haladu, abin tausayi kuma suka saka dan uwansu Alhaji Kamilu a cikin tashin hankali tsamo-tsamo. Wani abin kuma shine niman Tani da aka yi ta gudu,sai daga baya aka samu labarin ta mika kanta ga yan sanda tace gara su hukuntatta kafin Sajjid ya ji labarin abin da tayi mishi don ba ita ta haife shi ba, da ita da yan uwan Alhaji Mamman Ba'are, wato Haladu da Kamilu suka shayar da shi guba ya mutu, amma ita ba ta kashe Maisarah ba.

A hankali duk wani sharri yayi ta fitowa, hatta sakawa Hajiya Rabi da Yaranta wuta ,sune domin kada a samu matsala wurin tona musu asiri bayan dukkansu family suka had'a kai a dauke Majid, kuma aka yarda sai daga Baya Hajiya Rabi ta ce tana tsoron tsinuwar Nana da kullum take yiwa duk me hannu a cikin rayuwar Majid. Wato yarinyar nan matar Maina ta zame min alkhairi, zuwanta ya zame min alkhairi. Ta gaya min ni daya zan iya dawo da mijina gare ni, sai gashi ya faru. Kwanan mu biyu, a asibiti aka sallame mu, don ma Nana bata da lafiya idan ta ga abinda Yaranta suka aikata, sai ta ji kamar ta mutu.
Tayi kuka kamar ranta zai fita, amma haka ta ce ba ta zama a gidanta. "Atow na sani ko nima kashe ni zasu yi, tunda akan dukiya suka kashe junansu." Haka muka tare da ita a gidanmu baki daya, Amaan da Majid suka wuce Algers, don tunda abin ya faru sun ji ban yi maganar shi ba, ko da naji ana maganar shi sai nayi pretend kamar ban.ji ba, haka yasa suka tafi duk tsiya ya dawo yayi jinya a gidan yafi yana wata duniya.
Kamar yadda suka tafi haka suka dawo yaki biyo su, wannan abin ya kara harzuka ni wato don na nakasa yasa ba zai dawo ba, wannan abin yasa ran Mama ya kara b'aci,. musamman da ta kamani ina kuka da rubutu a wani ƙaramin littafi.
_Dama duk wata soyayyar da bata gaskiya ba haka take? Da gaske Love is gone_ faɗa tayi ta min tare da cewa na cire shi a raina yayi duk yadda yake so, dama lafiyata yake buqata tunda bani da shi bata ga amfanin zamana a nan ba. Rike hannunta nayi na ce mata. "A'a Mama ki bari yazo ya gaya min hujjar shi na tafiya idan lafiyata yake so kwana ɗaya ba zan kara ba, zan tafi kiyi hakuri kin ji."
"Na gaya miki gaskiya ba zan iya kallon yana wulakanta ki ba, akan me zai tsallaka ya bar ki bayan don..."."Don Allah nayi Mamana, kada Hajiya ta ji ki." Na fada ina zaunar da ita, ita uwa akan danta wata irin dabba ce da bata iya sauraron kowa sai dantan nan, uwa wata irin duniya ce da bata gane kome matukar akan danta ne. (Amma ba kowacce ba)

A hankali na samu hankalin Mama ya kwanta,yau muke saka tsammanin Majid, gobe ne har ta gaji ta bar Nijar Majid bai dawo ba, sannan ta ce nayi ƙoƙarin nazo naga likitan kunne, ganin har lokacin bai dawo ba, yasa na gayawa Hajiya zan tafi Kamaru. Ban san sunyi rigima da Mama ba, sai dai naga tsoro da tashin hankali a cikin idanunta ƙarara, "Kin gaji da zama ne? Zahra don Allah kiyi hakuri kada ki gaji da Majid."
Girgixa mata kai nayi na ce mata. "Ban san uxirinshi ba, amma nasan zai dawo zan tafi ne don naga likitan kunne." Hawaye ne ya zubo mata, "Da ina son ya dawo ne sai a kaiki asibitin kunne da yake Baihak." Murmushi nayi nace mata. "Hajiya da an barshi nayi kewar Zaytoonah ne xan tafi."
Ganin takasa shawo kaina, ta ce min. "Shi kenan za a shirya miki tafiya nan da kwana uku." "Tow na gode. Allah ya kara lafiya da nisan kwana." A yadda nake jin tana kallona sai nake jin kamar na rasa duk wani abin da nake dashi, sai nake jin wani irin tausayi a raina, don haka ina shiga dakin na fara kuka, shigowar Alfah yasa ni share idanuna dake ina mata turanci da fulatanci, Aryan suna mata Buzanci da Faransanci, da turanci ta ce min. "Ma kina kuka ne?" Kallon bakinta nayi na fahimci me take nufi, sai da tazo kunnen da nake ji ta kara maimaita min, wannan wacce irin rayuwa ce. Murmushi nayi mata nace mata. "A'a abu ne ya faɗa idanuna." "Ayya soli!" Ta fada da tsamin turancinta, haka na rungume ta muka zauna a dakin.

Hajiya Bayan Zahra ta bar falon, kiran Number da aka bata na dakin Majid tayi suna gaisawa yana dauka ta ce mishi. "Idan har ka sake ta saka kafa, ta bar Nijar yadda naga ran Aminatu ya ba'ci wallahi billahi azim ba zaka samu Zahrah ba, duk rintsi ka dawo wurin matarka kada ka sake ka kara wani lokaci ba ka dawo ba, domin ina jin kunyar yarinyar da ta nakasa domin ka, sannan ka dawo kana can ka zauna yau wata biyu kenan ana niman na uku."

Kafin ta Kashe wayar , tana faɗin. "Ka dawo kada ka rasa matar rufin asiri,da haka na jajurce akan mahaifinku da ban san yadda xan zama ba, ita da ta tsaya akanka zaka tozarta? Anya Majid kana kaunar Allah!"

Ta faɗa tana mita don haushi ya kamata, ya bata haushin kaniyarsu shi da likitan. Haka tayi ta faɗa.
**
A can kuwa babu shiri ya fara hada kayanshi. Shigowar Yazid yana kallonshi. "Ya da shiri?"
"Zahra zata tafi ta barni." Murmushi Yazid yayi yana faɗin. "haba dai."
"Wallahi mamarta tana da matukar zafi, yadda kasan volcano haka take, kai lokacin da ta bani auren Zahrah kada ka ga yadda ya tsayar min, yanzu kuwa tace idan ba zan iya xama da Yarta ba, na sako mata,don ni ne ɗan Zainab mahaukaciya da zan saki Zahra, ai ko Shawara wani ya bani sai inda karfina ya kare, balle kuma babu ɗaya kanwar biyu zan koma jibi zan koma gida na gaya maka "
Fir Majid ya ki zama, don babu wanda ya gaya mishi ga halin da take ciki an dai gaya mishi tayi rashin lafiya ne, kuma dalilin da zai saka Zahra tafiya bai dawo ba, dalili ne babba, don haka ya tattara ya ce zai zo shekaru uku ba wasa ba ne da wasu malamai zasu zauna zasu ce babu aurensu. Haka yasa gara ya tattara ya koma gareta.
**
Bayan kwana biyu, sauran kwana ɗaya tafiyata,
Duk yadda nake son sakewa, sai nake yawan fuskantar kamar ana min dariya, ko ana nuna ni, haka ya faru ne a hidimar da ake yi a familyn har su Maimuna da mijinta da abokin Mijinta da kanwarta. Jikina rawa yake saboda ban san taron na meye bane, sai dai duk yadda na juya sai na ga ana dariya da karfi, haka yasa na sulale zuwa dakina. Zauna dama haka nakasassu ke jin wani iri? Ina zaune a dakin Anisah da wata kawarta suka shigo wai sun zo min jajje. Ina tab'a wayata suka shigo ban ji sallamarsu ba, sai ganinsu nayi a kaina.
"Ya zaku shigo babu sallama?" Dariya tayi tana faɗin. "Kiyi magana a hankali, kina magana kamar da mutanen waje kike yi. Mun yi sallama baki ji da kunne me lafiyar ba ne? Au ashe fa kin kurmance."
Kura mata idanu nayi sai na saki murmushi, sannan na ce mata a hankali. "Idan kasan farkon ka, tsakiyarka ya dace ka ji tsoron isa, domin karshenka mutuwa ce.

Ni ta sanadin aure da kuma yaki akan mijina idan kin ji haushi ki zama sarauniya a dangi ta hanyar tsayawa mijinki, ba korarriya da kishiyar da zata zo ta koro ki ba " kome ya ja hankalinta suka fita da gudu,ban sani ba amma tabbas taji d'acin maganata,. Da gudu Amaan ya shigo ya riko hannuna muka fita da sauri. Har kasa ya sauko dani an zagaye shi bakiɗaya sai raba idanu yaƙe, yana zaune a tsakiyar falon. A hankali naja na tsaya tare da kwace rikon da yayi min zai kai ni gare shi. Zubawa juna idanu muka yi, a sannu a hankali na janye nawa idanu daga gare shi nayi kasa da kai, ina wasa da yatsuna. Hannun Alfah naji cikin nawa tana kallon yadda hawaye yake zubo min. "Ma!" Ta jijjiga hannuna. Daga kai nayi sama ina shanye hawayena, kafin na sauko da kan naji ya bani wani irin hugging da ban zata daga gare shi ba. Wani irin kuka nake me ciwo da zafi,kuka nake me cin rai da kowa a falon sai da ya taya ni, kuka nake na farin ciki da bakin ciki da suka hadu lokaci guda suka min dabaibayi, kukan sanin cewa bani da wani amfani a duniyar Majid sai dai ya min alfarmar zama da ni, kukan sanin cewan na rasa ji na da kunne ɗaya na har abada.
Chapter 133 · 0% Book details