Sashe 18
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fada tana kallonsu, kwana biyu da suka wuce har cikin gidan suka biyo ta suka ci mata mutunci har da mata gorin a caca aka aurota, haka duk bai isa ba Nana ta gaya mata cewa ta zuba idanu tayi kallo hatta wannan gidan da take ciki sai ta fice daga cikinshi, sai gashi Allah ya raba gardama ya kawo mata shi cikin sauki, don haka ba zata lamunci rainin hankali ba. "Hmm! Nana tashi muje!" Inji Hadiza, haka suka fito a harabar gidan suka same su, a ran Hajiya Hadiza ta ce. *Shaidanun biyu* kallon Nana Aryan yayi, ita hankalinta yana kan hannun Captain yana goge wata sabuwar bindiga. "Captain ni dai ka nima min lasisin rike bindiga!" "Munafiki algungumi uban me zaka yi da bindiga?" Juyawa yayi ya kalli Nana. "Hajjaju laifin me na miki? Uwar Mamman Ba'are!" Ya tambaye ta, yana wasa da katon lion dog ɗinshi. "Uwarka Sa'adatu gata can a sama." Juyawa yayi ya sumbaci hannun shi ya wurga mata. "Ta iya haihuwa tunda ta haifi Abdul Majid Mamman Ba'are, ta haifi Aryan Mamman Ba'are ba, Uwar Jamilah da Aneesah, Babar Amaan Mamman Ba'are, akwai saura ne?" Ya tambaye ta, cike da takaici ta ce mishi. "munafikin banza." "Da nayi miki me?" "Kai dai wutarka dabance." Sam baya son hayaniya, don haka ya d'anna kunamar ya sake harbi a iska, shiru wurin ya dauka. Musamman Hajiya Nana da ta ji kamar zuciyarta ya harba, kafin su farga daga ita har yarta sun gudu baka ganin alamarsu, sojojin da aka bawa Captain ɗin suka shigo a guje. "Sir!" Murmushi yayi ya musu alamar su tafi da hannunshi.
Kar'ar harbin Majid Mamman Ba'are, ya karad'e ilahirin gidan baki daya, wanda yasa kowa ya sha jinin jikinshi, lallai Majid ya iso, Gidan Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kuwa tab'e baki yayi ya ce. "Kowa ya sayi rariya yasan zata yi yoyo, ai na gaya musu, babu ruwansu da Yaran Sa'adatu amma suka ki, gashi nan sun takalo mana jaraba." Ya fada yana shan tea a hankali, "ni kuwa sai nake ganin kamar da gayya aka takalota."
Kallon Matarshi yayi, kafin ya ce mata. "eh da gayya ce mana, tayi abu ko Yaranta suyi su zama masu laifi ake so." "Amma me yasa suke haka ne?" "Saboda dukiyar Mamman ya raba biyu ya basu rabi, rabi aka yi rabon gado da ita."
"Allah ya kyauta!"
"Kin yi waya da Maisarah?" "Eh mun yi waya, amma tace min idan suka samu hutu zata zo." Shiru yayi yana kara jin ba dad'i. Kowa a duniya yana farinciki da nutsuwa idan yana tare da ahalinshi, amma shi a nashi ɓangaren dole ya hakura da Maisarah ta koma wurin dangin Mamanta da suke labenon, tunda a can ya auro ta,kuma ba karamin son Yaransu suke ba. Sai dai tun bayan Mutuwar Mamman Ba'are yarinyar taki zama a wurinshi. "Ina Jamal?" " Ya tafi wurin kallo!."
Gidan Hajiya Tani.
Cikin matsanancin b'acin rai take kallon Sajjid Mamman Ba'are, "kasan yadda na ɓata lokaci akan ka samu damar shiga cikin dukiyar Mamman Ba'are?" Girgiza kai yayi yana durkushe a gabanta. "Kiyi hakuri Hajiya!" "Idan ka kuma bani hakuri sai na tsine maka." Ta fada ranta yana suya, "sai da na gaya maka ba zan dauki kuskure ba, kace babu matsala Amaan zai bamu hadin kai, amma sai gashi daga kai har shi kun fad'i." Kasa magana yayi domin yana matukar tsoron kada yayi magana ta tsine mishi.
"Yanzu kana da hanyar da zaka iya dawo min da asarar da nayi?" Girgiza kai yayi, tayi kwafa sannan tacigaba da cewa. "Dake kai lissafinka baya ja, shine ka bude shegen bakinka zaka mishi barazana da rayuwarshi!" "Na tuba Hajiya!" Ɗaukar glass cup tayi ta jefe shi sai da ya tasa mishi goshi, jini ya shiga zuba a Kyakyawar fuskarshi.
"Ka sake bani hakuri sai na illataka!" Jini da yake zuba yasa shi rike wurin. "Ɓace min da gani." Mikewa yayi ya nufi dakinshi,ya shiga kallon kanshi a mirror din dakinshi. Wayarshi ce tayi ƙara. Dauka yayi ya ce. "Na'am!" Cizon fatar bakinshi yayi ya ce. "Ban san asara ba, kayan nan Libya zaa shiga da su, ka gayawa Guru ya binciko min duk inda Jaguwa yake a tsakanin sahara da dazuzzukar Kamaru da Nijeriya, idan kuka sake na fita farauta ba zai muku kyau ba." Ya kashe wayar yana me jifa da ita, asara biyu yayi yau baki daya bai tab'a shiga damuwa irin ta yau ba, ban daki ya wuce ya wanke fuskarshi da jikinshi, sannan ya bude first aid kit ya gyara goshinsa. Yana gamawa ya fito yana tsane jikinshi, ya ji harbin bindigar Majid. Datse fatar bakinshi yayi da hakorinshi sai da ya fara jini.
Ya sake bakinshi a hankali, yana jin Idanunshi yana cika da kwalla. Idan yana raye sai ya ga bayan Majid, ya raya a ranshi yana me kara tabbatarwa kanshi, sannan ya shirya cikin kananun kaya, ya dauki madubi ya saka domin ta rufe mishi inda aka jefe shi. A falon ya sami Hajiya Fauziya, tana kasa da murya ta ce. "Wato ban san yadda aka yi wancan dan iskan Yaron ya dawo ba, amma tabbas ita Uwarshi abin ya mata dad'i." "Zan fita." Dauke kai tayi tana faɗin. "Hm!" Daga haka ta juya ga Hajiya Fauziya. "Me kika ce?" Cikin tuntuben harshe ta ce mata. "Naga alamar babu nasara." A fusace Hajiya Tani ta watsa mata harara. "Kika ce me?" Hadiye yawu tayi ta ce mata. "Dama nace wannan karon mun fadi ya zamu yi?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Ya kuwa zamu yi? Ku je kuyi shawarar makomarku bamu ba."
A zunkud'e tace mata. "Ban gane ba?" Gyara zama Hajiya Tani tayi ta ce mata. "Dama da an samu nasara kamar yadda na gaya miki, kina da kaso saba'in cikin dari, ni zan tashi da talatin kuma gashi ya dawo." Cikin tsannanin takaici Hajiya Fauziya ta sauke kanta kasa, "Ban san ta inda aka samu matsalar nan ba, amma tabbas akwai wani abu."
"Idan ma akwai ya dace ki sani kece me yara mata baki daya, gara Rabi tana da Lukman, Harirah tana da Sharif ke fa? Babu ko daya sai Yara mata, kuma kin san koda yau gwanjon kayan ba'are aka yi kasonku bai wuce kason Aryan ba, kai ina ba ma zai kai kason Aryan ba. Duk da yadda muka yi dake na cewa zaki tsayawa Sajjid a wurin sai gashi har aka tashi baki yi kome ba, yanzu zaki zo kice min wani abu." Tana gama fadar haka, ta mike tana me barin Hajiya Fauziya a wurin. A hankali ta fita ta bar gidan, tana me jin takaici me yasa Majid ya dawo daidai wannan lokacin.
Alhaji Haladu.
Tunda ya shiga yake safa da marwa, kana ganinshi kasan lissafi ya kwace masa. Matarshi kuma me bashi shawara ta musamman ta zauna tana kallonshi. "Abban Afiyyah ban ga dalilin d'aga hankalin nan naka ba, ai ja da baya sai raggo, taya zamu zuba idanu Sa'adatu ta ci bulus bayan ka manta a caca aka ciyo ta."
Cikin takaici ya zuba mata idanu, ya ce mata "taya zan manta bayan dan uwana ya ciyo ta ne a caca,a lokacin da yake ƙishirwar d'a namiji a lokacin ya saka kudinshi aka ci kawunta."
Murmushi tayi tana kara jin haka shine abinda take bukata,bata kaunar Sa'adatu ta cigaba, amma dole haka zata hakura.
Shigowar Hajiya Fauziya kamar an watsota daga sama, yasa baki dayansu suka razana. "Ke lafiya?" "Ina lafiya kuwa." Ta fada tana gyara zama, "ya zamu yi Haladu?" Gyara zama yayi ya ce mata. "ya kuwa zamu ban da mu nime wata hanyar?"
"Kamar ya wata hanyar?"
Gyara zama yayi yana faɗin. "Dole zamu marawa Tani baya, sai mu san me za ayi kuma."
"Kana ganin marawa Tani baya shine mafita?" Inji Hajiya Turai Matarshi. "Eh mana shine mafita, domin ita ba zata watsar da ra'ayinmu ba"
Dariya tayi tana faɗin. "Lallai fa, tow Tani itama hanyar niman shiga take kan dukiyar Yaran Sa'adatu, idan kuka mara mata baya zata iya juya muku baya, idan kuka nime naku na kanku kowa zai kasance a ankare. "
Shiru suka yi kafin kuma suka ce mata. "Bamu fahimci inda kika dosa ba?" A hankali ta gyara zamanta ta warware musu fahimtarta, sannan ta kara musu kwarin gwiwa da cewa dole su kasance masu mika kai domin idan baka iya kama barawo ba tow shi zai kama ka."
Nan suka yi na'am da shawara ta, har Hajiya Fauziya ta fita, Hajiya Turai ta cewa Mijinta. "Bari na gaya maka gaskiya, matar nan munafuka ce ka sani nima kuma na sani, so abin da zan gaya maka. Zata tafi wurin Hajiya Tani da zancen nan, kai ka fara kiran tani ka gaya mata abin da ka yanke. Sai na gaya maka yadda zamu yi"
Ai kuwa kamar yadda ta fada haka ya kira Tani, ya gaya mata kome da kuma yankar bayan da Hajiya Fauziya ta mata, sannan suka dauki laifin kacokan suka daura mata, ita ce ta kawo musu zancen a shiga malamai. Jin shi Hajiya Tani take, sai da ya gama ta ce mishi. "Zan duba al'amarin"
Ta kashe wayar, murmushi Hajiya Turai tayi ta ce mishi. "Ka shirya zuwa bayan Magariba ka tafi gidan Hajiya Sa'adatu ka yi sulhu da ita. Idan ta lalace maka anan a can zaka fita"
Kurawa Matarshi idanu yayi tunda yake bai tab'a zata shaidaniya ce har haka ba. Take ya sake murmushi yana faɗin. "Lallai Hajiya ke duniya ce."