Sashe 94
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Dakyar ya lallaba kunyar shi yaje yayi sallah, sannan suka bar marad'i yaki yarda ya kalle su, sai dariya suke suna hirar su kamar basu san da shi ba. "Aryan kaci dambun nan ne?"
"Eh!" Ya faɗa yana kauda kai, don yasan Majid ba zai tab'a cewa kome ba. Sai da suka iso gida, Aryan ya bawa Amaan labarin abin da ya faru, ai kuwa suka kwashe da dariya har da ta fawa. Tsarguwa Majid yayi ya buga tsaki tare da haurawa sama, yasan ba mutumci ne da su ba, ai kuwa yana haurawa suka fashe da dariya.......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
07035133148 or 08130269641
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB249
_AUNTY UMMIE DAI AUNTY DAI, TAYA ZANCE NAFI SON YAN AREWA DAKU ❤️😭🙄 INNALILLAHI'WA'INNA'ILAIHI'RAJI'UN_
Dariyar su yasa Hajiya nishadi domin ta bude idanu ta kalli yaranta cikin farin ciki shima arziki ne, ba za ta tab'a manta wannan lokacin ba,haka yasa take murmushi. "Gulmar waye kuke?" Dariyar suka sake fashewa da shi, Amaan ya ce. "Mutum idan junarshi munafurci ne, ai zai gani a kwalarshi. Ina dalili kaci abinci ka tsaya sanabe, karshe ka kare da ɗaukar abu kana ci a boye."
"Bana cike da munaurci, kun zauna kuna gulmar shi idan ba tsoron ba kuyi a gabanshi mana!" Watsewa suka yi suna dariya don yau ba karya Majid ya saka su dariya. Haka suka tafi washe gari. Karfe biyu na rana, Anisah da suka kulle kansu a matsayin o gidan suna hira da Hajiya take tambayarta. "Hajiya naji board members suna maganar samar da sakatariyar ga Hammayo kuma baki ce kome ba"
Murmushi Hajiya tayi tana faɗin, "Duk abinda suka yi daya ne." Ware idanu tayi tana faɗin. "Hajiya amma kuma haka za a bar su." "Wa kike so a kawo?" "A kawo me hankali namiji da zai iya fahimtar Hammayo."
"Meye Hammayonki ya karanta?"
"Medicine!"
"Wani aiki yayi?"
"Soja!"
"Yana da kwarewa ne a aikin kamfani?" Ta girgiza kai. "Masha Allah, me yasa kika ci mutuncin Fadime?" Tsuru-tsuru tayi tana wulli-wulli da idanu, kai Hajiya ta iya kai hari. "Ba ki bani amsa ba?" "Hmm!" Anisah ta faɗa. "A jami'ar da take tana jan ragamar ajin ne a matsayi na biyu, ana saka tsammanin idan ta gama zata fito a first class, kina tsammanin kawai haka take kara zube? Ni a kaina ma fatan da sonta Amaan yake da ni zan tsaya mishi ya aureta, shine don rashin kunya da rashin mutunci kika yi ta cin zarafinta a kamfanin ko? Ai kome ya dawo har kunnena."
Ta kunna wayar hannun ta, ta nuna mata. Ranar da suka ci Mutuncin Zahra a kamfanin lokacin da ta je cin abinci, suka watsa mata abinci ajiki sannan suka zage ta har da cewa me bin maza, magana iri da kala, ita kuwa bata ce kome ba. Har suka gama. Don wani irin girmansu da jinsu take a zuciyarta. Tana jin kamar idan ta rama zata iya yin abin kunya ne yasa bata rama ba, kuma ta yanke hukuncin barin kamfanin.
"Baki ji kunya ba? Kin ci mutuncinta a madadin ta rama, ta wuce bata ce miki uffan ba. Ke har wani alfahari zaki yi da dukiyar Ba'are me hana barci. Tashi ki bani wuri."
Tashi tayi kamar munafuka, tana share hawaye don Hajiya bata saba yimasu faɗa ba, amma yau da Hajiya tayi mata fada sai take ji kamar zane ta, take don shagwab'a haka ta fito tana kuka, a bakin kofar fita suka hadu da Nana. "Uwar algungumai me aka miki kike kuka?" Ta tambaye ta fuskarta a had'e, dake wawuya ce ta shiga bawa Nana labarin har da kiran Zahrah mayya bata rufe baki ba, Nana ta tsinke ta da Mari, "Yar bakinciki, shine kike tsammanin zan goyi bayanki Allah sarki Zara haka don ubanki na gaya miki sai na ci ubanki akan Yarinyar da nake Addu'a Alhajin Allah ya auro min ita."
Yadda Nana take bala'i sai da Anisah tayi danasanin gayawa Nana, ita a tunaninta Nana zata bi bayanta su zage Zahrah sai akayi rashin dace Reshe ya juye da mujiya. Haka ta bar gidan tana kuka wiwi. Tare da kiran Hammayo ta gaya mishi rarrashinta yayi suka rabu lafiya.
Falon Hajiya Nana ta shiga tana haki. "Sa'adatu me kuke nufi da Alhajin Allah da Zahrah matar wata."
"Hajiya ya kike so na ce miki."
"Ya kuwa zaki ce min, bayan yanzu naji wannan me kama da mujiyar tana faɗin wai ta tozarta Yar baiwa Zahra."
"Nana kin ga yarinyar nan, aiki tazo yi bamu san asalinta ba. Shakuwa ce irin ta"
"Jini! Yarinyar nan ina jinta kamar Jamilah, yanayinta da sanyin halinta yana min kamar da uwar Jarabibiyar Yarki, kanwarki Aminatu."
Gaban Hajiya ne ya fadi, wannan maganar Nana ya tab'ata. Sai yanzu ta kara gano yanayin yarinyar. "Allah sarki kama ce!" Ta fada a fisge, don ita kaɗai tasan me take ji, Nana dai ta gama mitarta ta fita, a hankali Hajiya ta dafe kanta tana jin wani irin yanayi. Har wani jiri -jiri yake ɗaukarta.
•
Wasu lokutan ana iya amfani da kai don cimma wasu abubuwan, wani lokaci kuma sai ka ga wani abun yazo maka kamar sauyin yanayi. Haka yasa na tsaya da addu'a akan zabin Allah maɗaukakin sarki. Haka na mika lamarina ga Allah, domin ina matuƙar son Allah ya shiga lamarina, nasan shi ne mai kowa mai kome, har azumi nake domin facing Mr Chairman don Allah ya gani bana son fitinar shi. ShiYasa nake ta addu'a Allah ya bani hakurin zama da shi. Haka muka fuskanci final exam dinmu, wanda daga shi bana jin zan kuma dawowa makaranta sai karbar result.
Haka muka yi ta fama har muka gama, bayan na gama na shirya Amirah na gayawa Aseem a waya, ya shirya min tafiya Nigeria. Tunda na fara shiri ba kama hannun yaro, domin har taraba nake son zuwa na duba Ummi ko ta iso gidan Ya Babangida. Haka muka kwashe kwanaki muna shiri kafin ranar wata Asabar muka bar marad'i, ni kan ma tafiyar mota naso muyi yaki ya nima min ticket, muka bi jirgi.
A Kano muka sauka, daga nan na sake sayan ticket din yola. Lokacin da muka isa jikina yayi laushi, hotel muka wuce muka kwana domin ba zan ɗauki Yarinyar mutane izuwa taraba a dare ba, na daina wannan tafiyar ƙaddarar, washegari muka shirya cikin riga da wando rigar pink wando blue, sai bam da na sakawa Amira ni kuma na daura farin abaya, sannan na wuce na riko suitcase ɗinmu muka fito, Amirah tana rike da teddy bear dinta, gashi na mata kalaba, an jera bead a kitson. A hankali na bude kofar, ta fita da gudu yarinyar tayi kyau so much domin idan ka kalleta sai kaji a ranka tayi maka, haka na fito na ja musu kofa, ashe ita tana fita da gudu ta iso babban falonsu tana d'aga min hannu, d'aga mata hannu nayi nima, ina murmushi. Wayata ce tayi ƙara na duba kafin na d'ago naji ana faɗin. "Subhanalillahi. Baki ji ciwo ba ko?" Kallonshi tayi ta juya tana kallona, dariya tayi tana faɗin. "Daady ban ji ba." Ta mike zata kara gudun ya rikota, murmushi yayi yana faɗin. "Me kike so?" Isowa nayi nace mishi. "Kayi hakuri tayi maka barna ko?" Mikewa yayi yana faɗin. "Yarki ce?" Gyada kai nayi ina faɗin. "eh Amirah!" Daukarta yayi yana faɗin. "Princess ko!" Gyada kai tayi, zuwan wasu mutane guda uku, daya ya ce mishi. "Yallabai Madam ce da Magajiyar Lamido?" A hankali ya juya yana kallona, "A'a princess buge juna muka yi yanzun nan, na zata ma ta ji ciwo ne."
"Ban ji ba Daady." Murmushi yayi ya ajiye ta yana faɗin. "Gaskiya Malama ki kula da ita, ina sonta kamar tsokar da take kirjina." Ya faɗa yana shafa kanta, "yarrrrr!" Naji wani irin abu ya taso min, "in sha Allah zan kula da ita." Na fada hannunshi ya saka a cikin aljuhu ya ciro wani kati ya mika min, sannan ya dubi daya daga cikin mutanen shi. "Ka buɗe aljihun motar nan ka bawa princess bunch na dubu dari biyu ta sha chocolate."
"A'a yayi mata yawa mun gode ma"
"A'a nayi mata kyauta ne as my own kada ki dawo min da shi. burina Allah ya bani kamarta ma, amma Allah ya bani ya amsa tare da uwar ma." Ya faɗa cikin yanayin damuwa yana sumbatar goshinta. "Bani number ki." "Mu baki ne daga Nijar, zan baka Number nan da na can." Na mika mishi wayar. Haka ya saka ya kira ni, "ki saka Su'od Khabir Lamido.."
Murmushi nayi na saka SK Lamido, ina faɗin. "Amirah ki cewa Daady zaki tafi " "Daady zan tafi!" Ta rungume shi tare da sumbatar goshinsa, dariya yayi yana faɗin. "Zan yi kewarki."
"Nima Daady!"
Haka muka rabu waɗanda basu yi niyyar rabuwa ba, har wurin mota ya raka mu ya bata kuɗi me yawa, ya saka aka.kai mu tasha.
Haka muka bar Yola cikin wani irin kewa, kamar me Yarinyar nan Amirah abu abu ba sai ta ce Daady, abu ba abu ba Daady gata da farin jini kowa ya ganta sai yayi magana, ina tofa mata addu'a. Lokacin da muka isa taraba gidan Yaya Babangida muka fara nima dakyar na samu gidan shi. Ranar kwana muka yi muna kuka, da nake basu labarin abinda ya faru kowa sai da ya sha mamaki, da nazo ba da labarin Zulaihah da yadda ta tafi bamu gana ba, yayi min ciwo, ama ban gaya musu yarinyar gabana Yar ta ce ba, . "Ban san inda take ba, kuma ko da na sani ban san me zance mata ba, domin ta tafi ta bar ni da kewa, Alhamdulillahi na rayu a nijar cikin farinciki."
Na basu labari amma ban basu labarin abinda ya faru damu da abinda Addah tayi mana ba.
Haka na kwana da farinciki, washe gari tun kafin ka tashi na samu an gama mana kome yau gani cikin gatanmu. Naji dadi sosai. Bayan nayi wanka na saka riga da zani na karya kallabi, ina zaune aka kawo min abin karyawa, shima Yaya Babangidan yana fama da rayuwa ga iyali nan matan shi biyu. Lokacin da ya gaya min Ummie bata dawo ba, na kadu sosai domin nasan tace zata dawo no matter how. Hawaye ne ya zubo min don tausayin Yakumbo da ta nemi na dawo mata da ita gaban Yayanta, haka na wuni suku-suku da yamma ya ke gaya min can jenuwa, babu yan uwa don haka babu amfanin zuwa. "Dangin Mamana ba su zo ba?" Girgiza kai yayi min. "Babu wanda yazo sai dai Baffa'm ya gaya min cewa Mamanki yar Marwa ce. Yar babban gidane kakanki yana nan a raye yana koyarwa."
Hawaye ne ya kuma zubo min,wannan shine karfin dawowata Taraba amma babu wani nasara. "Zan nime ta in sha Allah" na fada amma tabbas ina cikin damuwa sosai. Kudin da SK Lamido ya bani shi na ɗauka na bawa Ya Babangida ya sayi kayan abinci, hmmm ko kunsan bawan Allah nan amadadin ya sayi abinci, sai gashi ya buge da karo aure. Satina daya na bar garin, kullum waya muke da SK Lamido musamman shi da Amirah, idan suna hira kamar wanda suka saba da juna na tsawon shekaru.
Lokacin da nace zan dawo ya turo min da kudi, wai nayi tsaraba haka na yi ta mishi godiya. Zan dawo Nijar tare da fatan Ummie da Addah zasu dawo nasan Allah zai hada mu.
Haka na tawo da tsaraba har da madara aka dafa min na tawo yola, daga nan muka tsaya SK Lamido da Amirah suka yi sallama, da kaya niki-niki haka muka tawo a jirgin Kano, da yamma jirgin nijar ya cilla mu marad'i. Kai jama'a nayi kewar garin nan mutanen Nijar akwai amana, nagarta da aminci irin na mutanen da.
Bayan mun iso ne na kira Sk Lamido da layina na nan Nijar, sannan na kira Ya Amaan na ce mishi. "Zan saka maka kindurmo aje a amsa a tasha."
"Wow kin tafi Nigeria kenan!" Ya faɗa, "eh, jiya na dawo." Sama sama.muka yi magana sannan muka kashe wayar, washe gari na kai jakar tasha, bayan yayi kankara aka wuce da shi Niamey.
Lokacin da ya isa ya kira ni, tare da cewa. "Bakauyiya da kina Whatsp da kin ga yadda kowa yake sha." Dariya nayi kawai nace miishi. "Hmm! Ni bana son damuwa ne."
Na fada ina dariya,
*
Amaan bai gayawa Majid cewa daga Zahrah ba ne, a'a kawai saka Hajiya yayi ta musu dambun gero wai na a kawo mishi kinda...... Majid the king of dramatic 🙄

[5/29, 07:47] Hlm: BHB250