← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 138

Sashe 60

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakyar ya bar gidan Hajiya, don dole ya nufi wani kanti, ya sayi wasu bakaken kaya yasaka. Sannan ya nufi wani asibiti. Dakyar yaga likitan, a lokacin wani sabon ciwon cikin ya kara turnike shi kamar zai mutu, haka likitan ya mishi scanning. Yana ganin yadda sperm ya dankare a cikin wurin kashinsa, shi yasa yake jin ciwon ciki.
"Alhaji wannan abin da nake gani, matukar aka cigaba da yin shi zai haifar maka da Cancer cikin makasayarka, sannan idan ma baka yi fama da Cancer ba, karshe zai zama tsutsa ya cinye maka duburanka, idan da hali tunda Allah ya ce kada ayi shi haramun ne, tow a barshi wannan shine nasihar da zan maka."
Idanunshi cike da kwalla ya ce mishi.
"Likita ka raba ni da shi, don Allah nayi alkawarin ba zan kuma aikatawa ba."
"Tow zan daura ka akan magani, na tsawo kwanaki sannan idan muka tara shi wuri guda sai, a maka aiki a cire amma ka kula gaskiya domin zaka iya rasa lafiyarka sannan idan ka cigaba zaka iya kamuwa da wasu cututtukan da babu magani sai mutuwa."
Tashi zaune yayi ya rike hannun likitan, kamar yaro karami ya ce mishi. "Likita na daina don Allah ka taimaka min bana iya rike kashi ma."
"Shiga ga ban daki, kayi." Haka ya shiga da gudu, tausayin Amaan din ne ya kama shi. Can da Amaan din ya fito ya zauna yana dafe goshinsa ya ce mishi. "ka kula sosai sannan idan mun yi aikin na cikinka zamu duba wurin muga ko zamu iya aikinshi."
"Ba zaku iya bane?" Girgza kai likitan yayi yana cire handglove din hannun shi yana faɗin. "A'a ba haka ba ne, wurin yana da matukar hatsari ne matukar aka tab'a wurin ya samu matsala tow kai baka isa ka rayu lafiya ba, zamu duba yiwuwar dubaka ko mu turaka wani asibiti."
"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Allah na tuba don Allah likita kayi wani abu."
"Ban ce ba zamu iya ba, shi makasaya yana cikin wuri me matukar muhimmanci da hatsari da zarar an tab'a shi zai yi wuya mutum ya kara morar kanshi."
Cikin kaduwa Amaan ya kalli likitan. "Ka min bayani yadda zan fahimta don Allah."
"Zan maka bayani ai, shi idan aka maka aikin matukar bai yi kyau ba tow ba kai babu rayuwa saida famfas zaka kare rayuwarka kamar yaro karami da ake goyo ne. Kullum duwawunka cikin kunzugu."
Wani azababben rawa jikin Amaan ya dauka. "Likita babu wata hanya ce?" "Gaskiya babu tabbas, koda akwai kuwa."
Jikinshi ne ya dauki wani irin rawa, kamar zai saki fitsari a wandonshi. Kuma shima likitan yayi amfani da waɗannan kalaman ne domin ya barranta shi daga wancan barnar domin idan ya mishi aikin zai iya komawa aikata abin da yake amma idan ya bashi tsoro dole ya hakura daga aikata shirmen domin wannan masifar da ta fad'o wannan zamanin ba karamar bala'i ba ce.
Don haka ya cigaba da razana shi, har sai da yaji nadamar aikata haka yazo mishi, sannan likitan ya rubuta mishi magani, ya tafi.
Koda ya sayi maganin gida ya wuce, a falo ya samu Matarshi. "Amaan ina son kudi?" "Ki kyale ni bani da lafiya don Allah." Ya fada mata yana wucewa. "Wallahi sai ka bani, kana board director ace baka da kudi uban me kake yi a kamfanin?" Juyawa yayi ya kalleta kamar zai buɗe baki yayi magana sai kuma yayi shiru, ya haura sama ya shiga dakinshi sai da ya rufe kofar ya nufi gefen gadon shi ya dauko kudi me yawan gaske ya fito. Kai mata yayi sannan ya juya zuwa dakinshi, kanshi kamar zai tsage haka yake ji. Lokacin da ya shiga dakin ya rufe kofar shi kwanciya yayi kafin ya tashi ya sha magani da fresh milki, kafin ya koma ya kwanta yana ji kamar ana tsatsagar zuciyarshi. Bai san dalilin fadawar shi wannan yanayin ba, amma tabbas bala'in da ya fada baya fatan wani ya kara faɗawa, babban abin da yake kara tsorata shi ranar da Hajiya zata gane me yake aikatawa ranar kashin shi ya bushe, wani irin tsoro ne ya kara mamaye ilahirin lungu da sako, na cikin zuciyarshi. Tabbas ranar zai bukaci mutuwarshi da ganin wannan ranar.
-----
Aryan.
Har aka tashi aiki bai ga Amaan ba, don haka daga wurin aiki ko gida bai shiga ba, ya nufi wurin Hajiya haka ya zame musu al'ada tunda dama suna zuwa da safe sannan da rana suna zuwa wurin aikinta, yanzu da ta daina aikin wurinta suke fara zuwa kafin su tafi wurin matansu. Da sallama ya shiga falon tana lazimi. Zama yayi sannan ya jira ta gama, kafin ta kalle shi. "Ya aiki?" "Alhamdulillahi!" Ya faɗa yana kallonta tv. "Da magana ne?" "Matsayin Aneesah yayi mata nauyi, ita matar wani ce, mai zai hana a bawa wani wanda muka yarda da amanarshi da nagartar shi. "
Kallonshi tayi kafin tayi shiru na wasu dakikai ta numfasa sannan ta ce mishi. "Ina ga a bawa Abdul Majid dan Hadiza."
Murmushi yayi ya ce mata. "Hajiya nayi tunanin haka, sannan idan kin lura sam ko cusa kanshi baya yi a cikin harkar gidan nan. Shi yake damun Hammayo amma shi Hammayo ko a jikinshi. Shi ya fi dacewa da xama CEO na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES."
"Kuma idan aka bashi a bazata Uwarshi zata sha mamaki, duk makaman yakinta zata zubar, sannan rigimar da yake tashi akan kamfanin zai yi sauki " inji Hajiya.
"Tabbas nima na amince da haka, amma hajiya Amaan ya shigo kuwa?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Ya shigo."
"Tow shi kenan" ya faɗa yana me mikewa.
"A gaida Nabeeha da takwara. Da dan Daada."
***
Agadaz
OIM : Organisation International pour Les iMigrations
office din yan gudun hijira suke kai takardun su ne domin a basu damar zama a cikin camp din oim yana under African countries ne, domin duk wasu ƙasashen Afrika da suke makotaka da Nijar suna turo mutanensu, domin akwai hulɗar zaman lafiya a tsakaninsu. Sannan akwai kyakkyawar fahimta idan har kasa ta turo dan gudun hijira Nijar zata mishi duk wani abin da ya dace har ta mai da shi zuwa ga gwamnatin ƙasarshi sannan da abin yi me kyau, don haka *OIM* yana kasar Nijar a cikin jahohi biyu na ƙasar, kusan kullum na duniya Addah da Ummi sai sun tafi office din amma kuma babu sa'a, domin yawan yan gudun hijirar da suke zuwa don niman a basu agaji.
Yau ma kamar kullum bayan sun bi dogon layi, Adda da idanunta daya da ya samu matsala take ƙare shi, wani jami'in wurin ya zo wucewa ya ganta ana ƙoƙarin ture ta a layin, ya ce musu. "Sannu Inna muje ke daya ce?" Ummi da take bayanta tayi maza ta ce mishi. "A'a oga tare da ita muke ina mata jagora."
"Amma ai ke ya dace ki tsaya a bayanta ba a gaba ya dace ki tsaya bs." Cikin gajiya da turereniyar da ake mata ta ce mishi. "Shi kenan oga." Ta faɗa tana komawa gaban Addah. "A'a muje a duba takardunku, domin ba a son me ciwon idanu yana tsayawa a rana."
"Mun gode fa " suka bi bayanshi har cikin office din, mutane sai surutu suke, suna zuwa aka duba takardunsu, Asalima stamp na Hukumar tsaro ne a jikin takardar. Ba ajima ba aka sallame su aka tura su camp, wato OIM camp shine ake kiranshi da aljannar yan gudun hijira. Duk wani abu da zaka bukata na rayuwa a cikin camp din an tanadar maka, kulawar da ake bawa yan gudun hijiran ko yan kasar basu samu, domin babu abinda ba a musu. Ana kyautata musu, sannan kome nasu ana basu. Daga zuwan su aka wuce da Addah Clinic da yake cikin camp din aka fara duba matsalar idanuhta. Ita kan cewa take. "Ku barshi zai tsiyaye da kanshi, ai idanun ya mutu." Ta fada cike da takaici, duk ranar da ta haɗu da Zahrah sai ta mata abinda ba zata manta ba, sai ta mata sanadin da ta sake komawa zero daga Add din da Yazid din ya sama mata, matukar tana numfashi sai ta saka mata Fargaba da tashin hankali a ranta, zata cigaba da zaman jiranta har ranar da zata bayyana.
Ko a cikin Uwarta ya kaita sai ta zakulota ta rama abin da tayi mata, ba zata kyale ta ba. Haka tayi ta kintsa mugun nufin da yake ranta.
Haka suka gama dubata, sannan suka sallame ta. Da magungunan masu yawan gaske.
***
Marad'i...........
#Mai_Dambulaaaaaaaaaaa
[3/4, 9:14 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*029*
Bahaushe yayi gaskiya da ya ce d'an uwa rigar k'aya, kabarshi a jikinka ya soke ka. Ka cire shi duniya ta zage ka. Ban fadi haka don kome ba, sai yadda nake cike da kewar Addah da Ummi, musamman Zuzu da ban san wata duniya take ba, ina matuƙar son ganin Zuzu ta gaya min meye nayi mata haka? Me yasa tayi min haka? Me yasa ta ha'ince ni? Kowacce rayuwa tafe take da kalubale. Sai dai a wannan lokacin na fahimci girma da muhimmancin nisantar su Addah. Sannan akwai wani abu daya da na kasa sabawa shi, wato tunanin Yazid, na kasa yarda ya mutu domin zuciya ta bata bani damar amsar labarin Mutuwarshi ba, sannan haka su Addah bana fatan ace suma sun mutu domin ciwon zai min yawwa.
Chapter 60 · 0% Book details