← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 138

Sashe 26

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dake yarinya ce kuma da sauran kuruciya a tare da ita, da kuma a fusace take da Addah haka ta rufe idanunta tayi ta dukar Addah. Ganin da gaske zata kashe ta yasa ta saka ihu da kururuwa tana niman ceto. Amma ina zuciyar Ummi ta kai iya wuya, domin ta gama sarewa matukar basu nan Addah kashe mata uwa zata yi, tunda ta iya sayar da Yarta Uban waye ba zata kawar don cimma manufarta ba, Ihun Addah yasa mutane suka farga aka kawo mata dauki. "Ke ba Babarki ba ce!" Aka shiga d'aga ta dakyar. "Da wannan ta haife ni gara ban zo duniya ba, in sha Allah Addah mushe sai yafi ki daraja." Ta fada tana kuka me ciwo, ta d'ago kai tana kallon yadda kowa yake bata laifi. "Wannan da haihuwarki gara b'arinki, sam baki cancanci zama uwa ba, Allah ya isa tsakanina da ke, Addah In sha Allah lahiranki sai tafi duniyarki muni." Ta fada cikin kuka domin bata san wani level zata ajiye Addah ba, domin matar bata buƙatar addu'a sai Addu'ar iftila'i da masifa da jafa'i. Sai da Uwar Mugu ta shigo ta zubawa Addah idanu. Kafin ta ce. "Me ya had'aki da ita?"
"Eyeee! Hmm kawai don."
"Karya take zuwa nayi ma same ta, zata kashe min Yakumbo." Harara Uwar mugu ta watsa mata tana faɗin. "Ka da na kuma jin makamancin haka."
"Naji Hajiya haka ba zai kuma faruwa ba," inji Addah da kumburaren bakinta, kallon Ummi tayi ta ce mata. "Kema wannan ya zama na karshe ki kula da Mamanki. A wannan duniyar mutane na iya kome saboda kuɗi kiyi tunani dakyau...
#money
#evilalive
#trueordare
#mai_dambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

*Ni ban san me Adda tayi aka tsane ba, salon ku saka mata ido da baki ta lalace 😹😡✊🏻🤔 da alamu Adda tana girgiza ku😹 mutuniyar kirki saura ku ji ban dadi 😡😹🤣*
___________________________________________
```Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....```

*013*

"Babu abin da kudi basu saka mutum ya aikata, rayuwar mahaifiyarki ko kuma ki wayi gari babu labarinta shine gaskiyar da zan gaya miki." Daga haka ta juya ga Addah, "Ba kowa yake da hakurin da zai ga kina shirin lalata mishi goben shi ya iya hakuri ba, don haka sai a kula." Daga haka ta fice a dakin, ita kuma Ummi ta koma gaban Mamanta, tana shafa fuskarta hawaye na zuba mata, a duniya idan akwai abin da ta tsana shi ne ka tab'a mata Yakumbo, haka yasa ta kece da kuka me ban tausayi, gani take kamar duk abin da ya faru Addah ce sababi domin da bata yi shawarar kawo Zahrah Taraba ba, da basu faɗa wannan bala'in ba, bakiɗaya ta tattara laifin kacokan ta aza bisa kan Addah, tsanarta da wani sabon kiyayyar Addah take ji, a hankali ta juya tana kallon Addah kafin ta ce mata. "In sha Allah sai na gayawa Zulaihah kin sayar da ita, sannan abinda baki sani ba, Zulaihah ciki ne da ita, don haka ki saka a ranki bakin ciki da goyon shege yana wuyarki. Mu dai duk lalacewar da muka yi bamu daukowa iyayenmu shege ba, kinci ribar bariki da hujja." Ta fada tana sakin wata dariya me daukar hankali ta cigaba da cewa. "Ni dake shege ka fasa, idan baki ga bayana ba, ni sai naga naki wallahil azim ki ajiye a ranki daga yau na fara farautar rayuwarki. Ba iya ke ba, hatta ta Zulaihah sai na saka ta tsane ki sama da yadda kike tsammani."

Cikin da Ummi ta faɗa mata, bai bata mamaki ba. Kamar yadda take ji take gani zata rasa Zulaihah. Murmushi tayi ta ce mata. "Ai ciki na san da shi, sai me? Kuma ki saka a ranki cikin ya kusan b'arewa matukar ina raye. Na gama magana sayar da ita zan yi idan ma suna sonta da cikin jikinta shi kenan, idan har zan sayar da d'iyar cikina Wacece ke da bazan iya cusawa a tashin hankali ba? bakya gaba na domin ina da abin da ya fiki daraja." Shigowar Munaisah ta kura musu idanu, "ba sai kin zuga Zulaihah ba, Addah sayar da ita kika yi ra?" Ta tambayi Addah dafe da goshinta, "Addah na zata duk abin da zamu yi miki akan kuɗi iyalinmu da mu kanmu mun tsira." Dariya Ummi tayi, ta ce mata. "Baki san wani abu ba, tow ina kallon lokacin da Addah ta danne Nenne har dai da ta shiga wannan halin."
Cakume wuyar Ummi Addah tayi. "Munafiki algunguma me nayi miki?" "Addah ba zamu kara miki biyayya ba ne, na gaya miki kuma sai na rabaki da duk me shirin yimiki biyayya." Ummi ta faɗa tana dariya. "Domin idan ta kashe iyayenmu, bamu da kowa bayan ita, zata saka mu lallai mu amshi ƙaddarar da bata rubuce cikin littafin mu, wallahi ina gaya miki sai na ga bayanki"
"Ummi kina tsammanin don kin gaya min Addah tayi yunkurin kashe Nenne zan yi mamaki ne? A wannan takin ni kaina na samu damar zan kawar da Nenne domin matukar tana raye ba zan samu yadda nake so ba, don haka ki ajiye a ranki mutuwarta shi ne tashina."

Wani abu ne ya tsaya a ran Ummi wato, ita ta ma lura duk wanda ya zauna da Addah sai ya zama mara mutunci, fisabilillahi uwar da ta haife ka, zaka nuna bata da amfani a rayuwarka. Komawa jikin Yakumbo tayi, tana jin kamar ta goyata su gudu, domin kuwa tana hango rashin imaninsu kada ta matsa jikin Mamanta a kashe mata uwa. Tana jin yadda suke shewa da ihu, kudi suke kirgawa tun daga lokacin bata tashi a gaban Yakumbo ba, sai da taji sallamar Zalaihah. Sai lokacin kunya ta kamata, tabbas bata kyauta ba amma kuma babu wanda zai so a tab'a mishi uwa. Abin da ya fara fitowa bakin Zulaihah shi ne. "Addah hatsari kika yi ne?" Ta tambayi Addah hankalinta a tashe. Kallon Ummi Addah tayi, ta fashe da kuka tana nuna Ummi. "Ban gane ba, kina nuna Ummi gware kuka yi da ita?" Girgza kai tayi ta fara magana. "Kashi ta bani." Juyawa Zulaihah tayi ta kalli Ummi, bata ce mata kome ba, ta wuce ta zauna tana nishi. "Ashe dama zulai har zaki yi ciki ba zaki gaya min ba?" Da sauri ta kalli Ummi, eh Ummi tasan da cikin, kallon Addah tayi kafin ta ce mata. "Ina son cikina ne, domin ba don naci abinci na same shi ba, domin ina son Ubangiji ya gafarta min ta sanadin cikin."
"Shi yasa Uwar da ta haife ki, ta sayar da ke ba." Inji Ummi, sannan ta cigaba daga inda take cewa. "Babu wanda zai yarda yana ji yana gani don biyan bukatar wani a kashe mishi Uwa, kama wannan tsohuwar kilakin nayi zata kashe min mahaifiya, kuskure ne don na kare rayuwar Mahaifiyata? Nayi laifi kenan?" Girgza mata kai Zulaihah tayi, tana jin zuciyarta kamar zata buga, ta kalli Addah . Gyara zama Ummin ta kara yi ta ce mata. "Ta sayar da ke. Idan kina da yadda zaki yi kafin su bukaci ɗaukarki da cikin jikinki sai ki sani." Daga haka ta mike ta suri gwangwani. "Zan tafi sallah ga Yakumbo, idan wani abu ya same ta, Addah ce." Daga haka ta fita daga tantin, Zuzu kan bata ce kome ba,.domin kuwa tasan idan tayi magana ba mamaki zucuyarta ta buga, haka ta zauna shiru har Ummi ta dawo. "Ki duba tana raye?" Zuzu ta tambayeta.b'ata Yakumbo Ummi tayi ta cewa Zuzu. "Eh tana raye." A hankali ta juya ta fara sallah, tana idarwa ta fara addu'a a lokacin Munaisah da Addah suka fice a dakin, ita kuwa ta cigaba da musu munanan addu'a da tsinuwa. Duk wanda ya jefa rayuwarta cikin hatsari.

"Ya isa haka, kada garin fushi ki jefa rayuwarmu cikin tsinuwa. Tunda Yakumbo tana raye, ki saka idanu akanta. Kuskure daya kika min, na bayyana zancen cikin jikina ko Zahra sai yau na gaya mata. Addah kuwa ba zan yi mamaki ba, idan ta nuna bata san da zancen cikin ba, ai ba laifi ba ne, to amma kada ki kara min haka." Itama Ummin cikin kuka ta ce mata. "Wallahi na gaji ne da halin Addah, a can idan ta ce ta dauki nauyin mu da na iyayenmu ba laifi amma a wannan lokacin da muke, cikin tsaka me wuya ta ce zata saka mu, karuwanci ai babu kanta sannan haka bai ishe ta ba, sai da na kamata zata kashe min Uwa, gaya min Zalaihah me ya dace nayi?"
"Kare mahaifiyarki;" inji Zuzu, "Gaya min ta ina nayi kuskure? Akan addah wani irin bala'in rayuwa ne ban gani ba? Kafin na waye a harkan sai da aka zubda min ciki sau uku, ya take son nayi? A haka ta haɗa ni da mutumin da ya goga min infection da kyar na rabu da ciwon. Haka kawai sai ta nime kashe min uwa? Duk abin da nayi fama da shi addah bata bani kudin magani ba, ni daya nayi fama da kaina.
Chapter 26 · 0% Book details