← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 138

Sashe 129

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kun dace!" Hawaye ne ya zubo min, kaina a sunkuye. Nace mata. "Eh haka kullum nake faɗa, amma a yanzu ya tafi ya bar ni, ba tare da ya ce min ya tafi ba."
"Tow ki bishi mana!" Ta faɗa min, (wato dai yar baka hali na nan ko) murmushi nayi mata. "Ina jiran mutuwar ce, domin nasan ba zan mori kaina ba, kuma babu me morata, tunda jigon rayuwata ya tafi!" Jin haka yasa tayi shiru, shigowa dakin Zaytoonah tayi da Alfah. Ta mika min Yar. "Bata abincinta" "yau aikin rana ake?"
"Eh mana "
Sannan ta fita, kallona Maimunan take kafin ta ce min. "Ashe kin san Mami Makarantar da nayi shi kika yi."
"Eh" na bata amsa ita gani take tafi kowa miskilanci, sai na nuna mata ni bani da shi amma ina da wata irin dabi'a tsakanina da kai eh ko a'a, ai kuwa haka muka zauna can ta mike zata fita. "Mu yan uwa ne, don haka next idan muka hadu mu tarbi juna as familie!"
"Hmm!" Nace mata, muka sauka na shiga dakin da kayanmu yake na zuba mata turare da da atamfofi kala biyu nata daya na Dean daya. Muna zuwa suka mike, har waje Hajiya ta rakasu, ni kuma aka yi ta shigo min da kayan baby masu yawan gaske har na rasa bakin godiya,bayan tafiyar su Hajiya ke gaya min nasabar da yake tsakanin mu yi......
[5/29, 07:48] Hlm: BHB273
Banyi mamakin haka ba, domin ina yawan jin Malamijo yana fadar waye Kawu ila sai gashi ta sanadin b'atar Majid ya haɗa dangin wuri guda musamman kawu ila, wani abu da na sani a kasar Nijar shine duk wani dan kasar Indai a ƙasar yake zaka same shi da girmama zumunci da kawaici, uwa Uba yarda da kowa. Akwai tarin albarka a rayuwarsu domin mutane da suke da halayyar zamantakewa tun zamanin baya, wannan yasa na ji Majid ya kara shiga rayuwata ta kowacce fuska. Sannan mu'amalarsu da kowa akwai son Barka.

Mutane daga ko ina na zuwa min jaje, da ta'aziya sannan a bangaren Munaisah d'aga aurenta aka yi tace ba zata iya biki babu ni ba, domin mijin da ta samu ta sanadina ta same shi don haka ba zata yi aure ba, kuma naji mugun dadi ashe haka yan uwa suke da dad'i? Sai nake ganin kamar duk wanda zai ce bai dace da yan uwa ba, hakuri ne bai yi ba, idan kayi hakuri kai da kanka zaka ce ashe haka dangi suke. Bana jin daidai da rana d'aya zan iya murmushi ni kaina nasan na sauya fiye da lissafin mai tunina, a duniya bana jin zan iya sakewa nayi farinciki, rashin Majid ya sauya min dabi'ata. Alhamdulillahi domin duk da haka na san ya gyara min rayuwata sama da tunani na. Watan mu biyu na matsa aka yi bikin Munaisah domin Mahdi yayi min kira ya kai sau dubu, zuwa kuwa har Hajiya ta gane wurina yake zuwa domin aurenshi. Tunda na mata magana tuni ta amince aka fara shiri. Ranar da na shiga dakinshi ina gyarawa domin abisa ala'adar da na koyawa kaina kullum sai na shiga na gyara dakin. Don ji nake cikin kowane yanayi zai dawo gare ni, haka yasa nake gyaran dakin kada ya zo ya samu da kazanta. Ina cikin aikin na sharo datti a kasan gadon ni dai nasan ni daya nake shiga dakin,, sannan babu wanda yake zuwa sai ni, wasu takardu ne a hankali na sharo tare da bude su. Abin mamakin shine yadda ya ajiye min sakon auren Munaisah wato gudummawarshi. Ai kuwa bana manta lokacin da aka saka bikin sai bayan na haihu na tab'a shigowa na samu yana abu ina bude kofar ya wurga kasar gado dama shi ne? Na tambaya a raina.
Zama nayi na fashe da wani irin kuka, me yasa ya tafi ya barni. Me yasa? Ko tausayina baya ji yayi tafiyarshi. Hajiya jin shiru shiru yasata haurawa da Alfah. Ganin dakinshi a bude ta turo kofar ganin yadda nake kuka yasa ta tsaya turus. Na rungume takardu, bata yi min magana ba, ta ajiye min yarinyar a gabana ta fita. Ita kanta Hajiya tasan majid danta ne, amma bata kawo Zahra zata so irin wannan yanayin ba, domin tasan tana da hakuri da juriya. Amma kuka ya karya mata zuciya, haka yasa ta fara wani tunanin amma bata jin zai zama kwalliya ga ita Zahran.

Bayan na gyara dakin a wurin muka wuni,don ko kasa ban sauko ba kayan daki ya saya mata da kayan kitchen kamar yadda yayiwa Zuzu, da sakon ya ajiye min kudi a drower din shi, da katin bankin shi na dauka nayi amfani da shi ga abin da xan haifa bayan wanda ya bar min, ni kaina ina da tarin kudi sai dare muka sauko bayan mun yi wanka mun sauya kaya, na samu Anisah tazo tana ta kumbure-kumbure, Hajiya da Zaytoonah sai lissafi suke. "Sannunku ukhty lissafin me kuke yi ne?" Murmushi tayi wanda ya kara fitar da kamaninta da Munaisah ta ce. "Addah Baban Mimi ne hajiyar shi ta ce ya dawo dani." Rike Bakina nayi ina faɗin. "Amma kinsan zamu tafi naija bikin Aunty Munai ko?" Dariya tayi tana faɗin. "Eh na sani mana, shi yasa Yaya Babangida ya ce za a maida auren a lokacin nata, amma kuma tarewa sai bayan sallah." Sai lokacin na juya ga Anisah "ke kuma fa?" Cikin rashin mutunci ta ce min. "Ina kin ganni kika share ni, waye ya sani ko farar kafa gare ki, har ya shafi dan uwanmu."
Kallona Zaytoonah tayi don na hanata magana idan Anisah tana haukarta, babu ruwanta. Dauke kai nayi na ce mata. "Sai dai bakar kafa, sannan idan kika cigaba da takura min gidan nan sai kin daina zuwa."
"Wannan haka yake, saboda ta hana Mijinta sakat don zai ƙara aure shine take jin haushin kowa." D'aga kafadata nayi ina faɗin. "Beb zubo min abinci, kowa ya kwaso da zafi bakinshi. Auren yanzu ma ka lallaba ya aka kare bare kuma kayi tawaye? Idan kina ganin kashe auren shine mafita sai ki gwada yi amma ki sani kowa rai ya amfana baya ga me shine." Na fada ina cin jollop din taliya da aka yi na dare wanda yaji namar rago, ganin ni da Hajiya babu wanda ya sha bakinta yasa ta mike ta wuce dakin Hajiya, nasan xamanta da Zaytoonah babu lafiya don haka na ce Zaytoonah muje mu kwana a saman, don a banza zasu yi ta gayawa juna magana.

Haka muka kwana ina tambayar Zaytoonah me take bukata na kayan daki, dariya tayi tana faɗin. "Idan lokacin yayi xan gaya miki."
Tsaki nayi na ce mata.
"Allah ya taro min ke!"
Haka na dauketa daga kasa ta dawo sama, domin daga alamu Anisah auren ta balle, ta dawo zata yi mana iyayi. Aryan ya samu Mijinta ya ce ya gaji, don haka ta zauna a gidan ta ji, ba ayiwa mutum dariya amma Zaytoonah sai da tayi da nake mata fada kuka ta saka min tana gaya min yadda take zuwa har asibitinsu tana cin mutuncinta. Murmushi nayi nace mata. "Ita motar gawa ba ayi mata dariya, idan bai dauke ka ba, wata rana zai dauki ubanka. Don tayi miki gorin mutuwar aure kanta tayiwa ni banga abin tashin hankali ba."
Cikin shashekar kuka ta ke gaya min. "Shi yasa nace Baban Mimi ya dawo mu gyara aurenmu." "Dama kece kika bukaci ya dawo?"
"Aunty na nuna mata nima mijina yana jirana tunda yaki auren kowacce mace."
"Mamarshi fa!"
"Kinsan shine ɗan auta a gidansu, da ta tada bori ya bar gidan shine ta kirani wai nasan inda yake? Ni kuma dake nasan yadda suke son shi na ce ta kwantar da hankalinta zai dawo na nime shi ta daya layin shi nayi ta rarrashinsa, dakyar ya koma gida suka yi mishi tambayar duniyar nan dakyar ya ce musu shi ni yake son na dawo."
"Shine da safe hajiyarshi ta kirani take rokona na yafe mata, domin albarkacin Mimi na dawo wurin Babanta. Aunty me yafi haka dadi, ai kuwa nace mata ni ba zan dawo su wulakanta ni akan abin da ya faru ba, matar nan tayi tsalle tace wallahi ko karen gidan bai isa ya min haushi ba, ai dama tsakanin mata da miji duk wanda ya shiga shine munafiki, haka matar nan tayi ta rokona na dawo nace ta samu Mama suyi magana. "
"Hmmm, sannu Zaytoona!" Na fada mata wato har ta gyara aurenta cikin ruwan sanyi, dariya ta yi tana faɗin. "Matar na tuba bata rasa miji,. Sannan akwai wani abu da ba a gane ba, shi auren ɗan auta yana da dad'i, idan yana sonka all over kowa yana sonka, idan baya sonka tow hatta karen gidan haushi zai maka. Ina dalili ga inda zan mike kafa nayi ta rashin jina ana tattlina ina zan yarda da zagegeduwa."
Wato yan matan yanzu wasun su, sun gane yadda zasu gyara aurensu.
Chapter 129 · 0% Book details