← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 138

Sashe 56

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washi gari.
Aka kai sakamakon office din Aryan suna tattaunawa da Majid da ya kawo mishi, "Yallabai gashi nan, sakamakon binciken da muka yi." Ya mikawa Aryan kallon Majid yayi kafin ya dauke kai, yana amsar takardan. Mikawa Majid yayi ya ajiye, yana kurbar coffee. "Mun gode!" Sannan mutumin ya fita, zama Aryan yayi ya fara bude takardar, mikawa Majid yayi, "ban fahimci abinda suke nufi ba."
A hankali ya amsa yana faɗin. "Kiran da yayi kafin faruwar lamarin, sai sakon da aka turo mishi aka goge na barazana, sannan a daren da abin zai faru kamar bibiyar shi aka yi. Ka duba ka gani"
"Wannan number kamar na san ta." "Amaan Mamman Ba'are!" Majid ya faɗa, tare da ajiye kofin. "Kada ka ce min!" Aryan ya faɗa yana zare idanu waje, "Tow yanzu ni da kai muna nan taya zan sani bayan an bar masu bincike sun yi aikinsu, ace abu sati daya a matsayinka na Chairman ka gaza yi, ok zan tafi tunda kome ya fito zan bar kasar nan yau. Amma kafin nan ka fara duba number na farko kafin na Amaan Mamman Ba'are."
Saka number yayi a wayarshi, "Haladu Abdul Majid ba'are." Ya furta. Sai daya number kan babu baya ma amfani alamar an daina amfani da shi.
"Don Allah ka tsaya a kammala binciken!" Aryan ya faɗa, shiru yayi bai ce mishi kome ba, har suka fita daga Office din. "Office dinka ko!" Sai kuma yayi shiru bai kara magana ba, har suka isa gida kafin su kara mika sakamakon ga yan sanda sai da suka ritsa Amaan. "Me Manaja yayi ka kashe shi?" "Ni kuma?" Ya fada a razane, "a ranar da zai mutu ka kira shi!" Majid ya faɗa yana kallon Aryan. Kamar ba da Amaan yake magana ba sannan ya cigaba da cewa. "Kunyi waya da shi na tsawon minti ashirin, wanda har Muryar ka ta fito."
"Idan ka tsane ni, sai ka min sharri." Aryan zai magana ya dakatar da shi. "Kyale shi, ina daidai da shi."
Ciro wayarshi yayi a cikin aljuhun riganshi, ya kunna.
_Kada ka sake ka bawa Aryan wannan files din Sajjid idan ka sake ka bashi sai na kashe ka na gaya maka_
"Ina fatan ka fahimci wannan Muryar?" Shiru yayi yana kallonsu. "Bani na kashe shi ba wallahi." "Eh kowa ya sani ba kai ne ka kashe shi ba, amma me yasa ka faɗa zaka kashe shi?"
"Tow ai barazana nayi mishi!"
"Barazana da mutuwa?"
*Yallabai Amaan nasan meke faruwa tsakaninka da Sajjid ni dai ba zan baka ba, amma ina maka fatan shirya idan kai me shiryuwa ne, idan ba zaka shiryu ba Ubangiji ya gaggauta kashe ka, amma ba zan bada Files din nan ba*

"Hammayo akwai wani abu da Amaan yake aikatawa tunda har irin wannan addu'ar ya fito bakin Manaja, mutumin kirki ne, ya kai sama da shekaru ashirin da biyar yana aiki a kamfanin mu." Inji Aryan, shiru Majid yayi yana nazarin yadda zai shawo matsalar, kafin ya tafi amma tabbas akwai gaggarumar matsala. "Kai da Sajjid kun kashe bawan Allah kenan? Domin da alamu ya ga kuna aikata wani abu ya dauke files din."
"Wallahi a ranar ban shiga kamfani ba, asalima ban san yadda aka yi ya mutu ba."
"Shi kenan! Aryan riko shi muje da shi, zan tabbatar da yayi magana in sha Allah." Inji Majid. Riko Amaan Aryan yayi suka fita daga gidan suka nufi inda motarsu take, Turus suka yi..
***
Zahrah
Raba ni dasu Addah da Yallabai Yazid yayi ya fi kome, saka min nutsuwa sannan an bani mai taya ni reno, bani da aiki sai karatu, domin a yanayin yadda muke yau da gobe har ya san na fara karatu na bari. Don haka da kanshi yake gaya min.
"Zaki koma makaranta."
Murmushi nayi na ce mishi. "Yaushe? A wata duniyar? Wannan duk mafarki ne." Na fada ina kokarin mikewa. "Da gaske zaki koma makaranta domin ki karanci tattalin arzikin kasa, ta haka zaki samu aiki me kyau ki gina kanki ba tare da wani ya sayi abu me daraja a tare dake ba, naso da ina da hali ba zaki kara zama a kasan wani ba. Sannan ba zaki kara yadda ki mu'amalanci waccan kanwar Baban taki ba. Akwai wani abu da kike dashi kin kasa fahimtar haka, sai dai nan gaba zaki gane haka. Amma kiyi karatu sosai domin ta haka zaki zama Madam Zahra babban akawun kamfani."
Don haka na kara maida hankalina sosai, sannan da kanshi ya nima min wani cikin mutanen shi,yana koya min yadda ake amfani da laptop, rayuwata da ta baby tana cikin kwanciyar hankali, sannan bani da Matsalar kome, sai ta cigaba da kula da Baby da karatu na. itama Baby tayi katuwa bul bul da ita tayi kyau.

---- Wata na biyu ban saka Addah a idona ba, yau da ya shigo da yake sai ya jima bai shigo ba, "ina son zuwa ganin Addah." "Hmmm! Tow." Ya fada yana kallon yadda nake shiri, yan uwanka yan uwanka ne komai muninsu, haka ya raka ni yana rike da Baby da take niman wata biyar, yadda na gansu babu wahala a tare da su, sannan suna cikin nutsuwa. Kamar na fashe da kuka haka na isa gare su, na mikawa kowacce jakarta da na kawo musu. Ganin yana tsaye yasa Addah kame bakinta. "Naji daɗin ganinku, Addah ya idanunki?"
"Kina farinciki ne don ba zan kara gani da shi ba ko?"
"Ko daya Addah, ya kamata ki daina tsanata."
"Saboda ke na rasa Y'ata."
"Addah don Allah ki daina faɗar haka, idan don nice ya kamata ki gane na amshi hukuncina da rikon Yarta."
"Idan ina raye sai na saka yar ta kashe ki, wallahi sai na saka ta wulakanta ki." Murmushi nayi ina wasa da hannuna, "zan yi fatan ki kai wannan lokacin sannan ni kuma zan yi ƙoƙarin naga na daurata a kan layina, in sha Allah, sai kin sha mamaki ba zan hana ki ita ba, amma kuma sai kin yi tunanin anya jininki ce." Hmm Addah kenan, bari mugani Ni da ita waye zai yi sa'ar cika burinshi ni zan nemi taimakon Allah ya taya ni, rikon Allah ya kare min ita da zuciyarta. Cikin fushin da ban san ina da ita ba, na kalli Ummi na ce mata. "Ummi zan tafi." Na kalli Addah, na ce mata. "Ki ajiye hakan ni dake Allah ya bawa mai rabo sa'a!"
Na fita yana kallon yadda muke magana da fulatanci ya fahimci faɗa muke da harshen mu, don haka yayi ta kallon yadda nake magana, ina fitowa na share kwallar da zai zubo min, na amshi yarinyar ina jin wani irin kuka ya kwace min, domin kuwa ina jin tsoron kada Addah ta sake raba ni da wani abu mai daraja.......

```Shahararrun goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136 KADA KU MANTA KAMAR KOWACCE WATA Wannan akwai Promon Azumi me kike jira ne*
#Mai_Dambu
[2/29, 7:47 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price
Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne```
*TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641*
Hular Yara
Mayafai
Dogayen riguna
Hijabai
Takalma
Kayan Yara
ATAMFOFI
Laces
SHADODDI
Materials
Sayan na gari mai da kudi gida.....

Wannan page din na kune.
Hajiya Sa'adatu wato Ambassador
Auntyna Addah gashi nan kun zungud'o ni nayi muku posting....😍🥰 Nagode sosai da kulawarku... In sha Allah sai Talata ina da uzuri me girma 🌹🥰😍

*027*
Duk wanda Allah ya jarrabe shi da fitinar Addah, tabbas ya gamu da jarabawa, kamar dai ni da ta addabi rayuwata, amma ban iya daukar mataki ko na mata wani abu ba, na barta da Allah da kuma halinta, in sha Allah Ubangiji shi yasan yadda zai yi da ita.

Bayan fita ta, Ummi ta fisge kayan da na kawo musu, "bani nan, ke da bakya kaunarta, taya zaki ci abin hannunta bani ko babu komai Na ci tudu biyu." Ta fada tana buɗe ledar. "Ki bani kayana tunda kema ta baki naki." Inji Addah kamar zata yi kuka. "Wallahi ba zan baki ba." Inji Ummi. Cikin bakinciki da abin da Ummi take mata, ta ce mata. "Allah ya isa ban yafe ba." ke ai mu zamu miki Allah ya isa bamu yafe ba, tunda kika lalata mana rayuwa, kuma muka cigaba da zama dake ai kin san mun yi hakuri, oya wuce tsohuwar banza kawai."
Ta haɗa da abinda na kawo mata, ta cinye har da na Addah.
Chapter 56 · 0% Book details