Sashe 91
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Tun daga lokacin na fahimci daga Hajiya, sai jarababbiyar tsohuwar nan suke masifar kaunata, sai wata da babu ruwanta da ayi da kar ayi, amma kuma sauran kiri-kiri suke kirana da yar iska me bin maza, na makalewa dan uwansu. Wani lokacin idan naje asibitin sai su hana ni shiga, haka yasa na hakura da zuwa tare da kame kaina, tunda ba dole ba ne.
Sannan nayi apply wani kamfanin, a nan cikin Niamey na bar musu nasu kamfanin, don na fahimci ko wasu basu kashe ni ba, takaicin Ba'are family ya isa ya kashe ni, ina komawa wancan kamfanin sai gashi Allah ya taimaka na samu mataimakiyar shugaban tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, kuma abin da na fahimta nazo a daidai lokacin da suke bukata ta, sai gashi na samu kawaye da Abokai, haka yasa naji kamar an tsamo ni daga wuta zuwa Aljanna.
***
Poland embassy.
A hankali take taku kamar me tausayin kasa, idan har jiki da kuɗi suna biyan bukata a tsawon shekarun nan hudu tana jin babu wanda ba zata yi gogayya da shi ba,kai tsaye ta wuce office din jakadan Nijeriya, wanda haka yasa aka bude mata cikin nutsuwa ta zauna.
"Munaisah Abubakar Takum." Kura mishi shanyayyun idanunta tayi ta ce mishi. "Ina son visa zuwa Nijar."
"Amma." Ya kalleta tare da lashe bakin shi. "Ba zan baka ko sisi ba, haka kuma ba zan baka jikina ba, domin na fahimci baka da lissafi wallahi."
"Amma kuma me yasa ba zaki gane yadda rayuwar nan take ba, shi fa kome bani gishiri na baki manda ne?"
Wayarta ta dauka ta kira wani layi. "Baby!" "Me kike so?"
"Wai sai na bashi "
"Waye haka?"
Mika mishi wayar tayi, Mikewa mutumin yayi yana faɗin. "Afwan Sir ban san yarinyarka ba ce. An bata kome yau zata bar Poland "
Yana gamawa ya kashe wayan yana faɗin. "Shegiya kice bujenki na wasan manya ne."
Tabe baki tayi, tana faɗin. "Zan je na dawo ba zama zan yi ba, don ina da mara lafiya."
Ta juya ta kwashe kayanta ta yi waje.
"Duk da ban yi karatu ba, bana jin xan kare rayuwata a wulakance." Ta fada tana tafiya a nutse, domin wani buri da take da shi ba zata iya give up ba, taya zata ganshi kuma ya zame mata haramiyanta. Murmushi tayi zuwa yanzu ta daina bariki. Mr Paul kawai take tare da shi, shima saboda yana masifar jin dadinta ne, yasa bata rabu da shi ba kuma.yana zuba mata kuɗi. Hatta kudin fansar kanta shi ya bata, ya kuma bude mata manya manyan store na kasuwanci a Poland din. Kuma ya hanata mu'amala da kowa, ya mata abubuwa dayawa. Mr Paul yana cikin manyan attajirai kuma yan kasuwan kasar, shi yasa yake manne da ita. Babban abinda yake so a tare da ita shine ta amince ta aure shi amma kafira taki, haka ya faru ne shekaru biyu da suka hadu da wani wanda ya dace da tsarinta, sannan musulmi kuma dan kasar Afrika ba irin mr Paul da yake kirista ba.