Sashe 136
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Yafendo da Goggo Sume suka daka musu tsawa, kafin Baba karami ya shigo yana kallonsu. "Baku ji kunya ba? Kuna cece ku ce akan yaranku."
Wani irin kuka Hajiya ta fashe da shi tana faɗin. "A kodayaushe Amina ce me gaskiya nice mara gaskiya." Malamijo ya ce mata. "Dole tayi gaskiya kina ganin Yarki tana kuskure baki tsawata mata, ko an gaya miki bamu ji irin abinda Anisah take yiwa Zahra ba ne? Don haka ga Yaranki nan ki saka Abdul Majid ya saki Zahrah ai da nasan da wannan tashin hankalin da ban kara mai da mishi ita ba, Mun ji Zahra kurma ce kuma karuwa ce, Zahra ina babu iddarshi a kanki? Maza sake ta yau ba gobe ba za a daura mata aure da Yazid."
Wani irin rikicewa Majid yayi ya mike tsabar ya kidime, fadi yaƙe. "Shi kenan sun kashe ni, sun gama da rayuwata." "Ko mutuwa zaka yi ba zan koma ba, ba zan koma.ba ka zauna da danginka, bani da kunne yan uwana karuwai ne, ka rike nagartattun danginka, yarinyar da take tsakaninmu idan baka yarda da yarka ba ce itama zan rike amma ba dai gidanka ba."
Na fada bayan na fito dakin sannan na koma, ina jinsu tunda na koma kuka nake. "Shi kenan,ta kwana gidan sauki oya sa shi ya saketa." Zubewa yayi a kan gwiwarshi a falon babu wanda bai bawa tausayi ba. Har itama Mama sai da ta dauke kanta. Babu abinda Majid zai nima ta hana shi, amma yau bata jin zata bashi Zahra ta sauki. "Innani, gaya min waye kike so na kashe zan kashe idan zaki bani Zahra. Innani gaya min waye kike so na b'atar da shi zan yi haka idan zaki bani Zahra. Innani ga shi wannan shine takardun duk wani abin da na mallaka idan zaki bani Zahra na bar miki ko da dako zan rike Zahra zata daura zanin da matar shugaban kasa zata daura. Innani gashi wannan bindigar tawa ce, ki kashe ni idan har zaki bar min Zahra a rayuwata na amince."
Ya ajiye mata kome, sannan ya tafi gaban Hajiya da jikinta yayi mugun sanyi ya ce. "Tana yi ne domin yarta, tana yi ne domin darajar Yarta, zo ki bata hakuri zata hakura, idan bata hakura ba idan na tafi sai dai a dawo muku da gawata."
Gaban Alhaji Isma'il ya koma, "Kawu na kawo ka ne domin ka nima min alfarmar Mama ta bani yarta me daraja, Kawu kada .ka zama dan kallo mana."
Rarrafawa yayi gaban Nana wacce tun da aka fara take share hawayen takaici. "Nana kukan kawai zaki yi Nana kuka kawai zaki min, Nana ba zaki bata hakuri ba, Goggo Sume Yafendo. Wai me yasa ban mutu ba" ya faɗa yana kallon kofar dakin. "Yarinyar ce ni take cewa ba zata zauna da ni ba, idan kowa ya guje ban cancanci ki guje ni don laifinsu ba. Zahra ki gaya min me zanyi don farincikinki?"
Ina dakin sai kuka nake, Ya bude baki zai magana aka ji Muryar Mama tana faɗin. "Ba zan hana ka Zahra ba, ba zan saka ka kashe kowa ba, kuma ba zan so ka rabu da kowa ba, sai dai sharadi." Da wani irin sauri ya isa gabanta. "Kwashe kayanka, kafin nayi ra'ayin sauya tsarin."
"Kiyi hakuri don Allah, Aminatu ki bashi damar zama da Zahrah wallahi billahi azim ba zan sake wani ya muzanta mata ba, na rantse da Allah." Inji Hajiya nan aka shiga bata hakuri tana ji sai da aka gama ta ce musu.
"Zahra ba zata zauna gidan Mamman ba'are ba,. kasancewar ina da wasu Yaran zasu zo wurinta, bana son su zo a musu gorin arziki. Na biyu babu Abdulmajid ba kara aure, sai ranar da Zahrah ta mutu, idan yaso a ranar ya kara aure. Na uku duk wanda ya kuma zagar min Ya ko Yarana kotu zata shiga tsakaninmu,. Ga wanann takardan yarjejeniyar ce sannan Abdul Majid zai biya miliyan dari biyar kudin diyyar rasa kunnen Yata da kuma ci mata fuskar da ake yi, sannan zai ɗauke ta zuwa jinyar kunne. Bayan nan na gama magana idan ya muku fine idan bai muku ba, a sako min ita."
Ta fada irin ko a jikinta, take aka bata goyan bayan, jiki na rawa ya shiga ware kudin ta wayar shi da wasu kadarorinshi ya kalli Mama ya mika mata ya ce. "haka yayi?" Yadda jikin shi yake rawa yasa ta riko hannunshi tare da kwala min kira. "Ban yi haka don kwadayin kudinka ba, nayi ne a san darajar Y'ata, sannan kada na kuma ganin Anisah a inda Zahrah take idan ba haka ba, sai kotu ta raba mu."
Fitowa nayi ta galla min harara. "Munafuka,ga mijinki nan kudin diyyar kunnenki nace miliyan dari biyar."
"Mama yayi mishi yawa, miliyan goma ma ta isa, idan aka duba girman zumuncin."
"Uwaki da zumunci ni kan Aminatu hala babu zuciya a kirjin wannan yar taki anya ba sace miki Y'a aka yi ba? Yarinya bata da kishin kanta."
A hankali akayi ta bata hakuri, Ana rarrashina da ita tare da mana nasiha, ita kuma Anisah Kawu Isma'il yayi alƙawarin daureta idan ta kuma shiga sabgata. Kai an sha drama sannan suka juya kan Hajiya da nuna mata tarbiyyarta sakarci ne ba tarbiyya ba, Anisah tana son fin karfinta. yadda aka mata tass yasa ta ce Anisah ba zata bita nijar ba, ta zauna anan Kamaru,
Bayan nan aka rufe da addu'a, sai dai me kuma zai faru, Majid yana mikewa ya yanki jiki ya fadi....... Tsugune bata kare ba..
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400.
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:48] Hlm: BH79
Kamar wacce aka dasa ni nake kallonshi kwance, ashe kuka rahama ce dadi yake sa ayi . Ban san wacce duniya nake ciki ba domin tun ina jin salatin mutane har ta kai nima na daina ji da gani na zube a wurin.
Dukkan mu biyu naji labarin an kai mu asibiti, a yadda Zaytoonah take gaya min damuwa tayi mishi yawa, domin ni na farka da yammacin washe gari. Shi kuwa naji ance har yanzu bai farka ba, domin kuwa a gajiye yake. Tunda na sauke sallaolin dake kaina, na wuce dakinshi nake zaune ina azkar da salatin Annabi, haka na cigaba da du'a'i sallah da abinci yake tadani har tsawon kwanaki uku, a rana ta hudu bawan Allahn nan da na cire rai ya farka. Dama abisa ala'adar da na dauka kullum zan daura kaina a kirjinshi, naji ko yana raye, idan kuma bai min ba, zan tab'a hancin shi da gefen wuyarshi. Ashe tun ina gyangyadi ya farka, yana kallona kamar a mafarki nake jin kamar ana kallona, bude idanu nayi ya lumshe idanunshi, tashi nayi na fara yan dube -dube, can sai da na gama nakan sumbaci bakinshi. A hankali na kai bakina kan nashi zan sumbata kawai naji ya cafke bakina, ban san lokacin da na daka tsalle ba, na koma bakin kofar. Hannunshi ya kai saman bakinshi. "Zaki yi disvirgin din balagaggen bakina Allah sarki bawan Allah." Ya shafa bakinshi. Tura baki nayi hawaye na zuba min na ce mishi. "Fisabilillahi idan da ina da ciki ne fa? Ba asara zaka ja min ba wannan wane irin abun ne haka!"
Kura min idanu yayi yana faɗin. "Zo ki cire min waɗannan monitor din." Na isa kanshi ina taya shi cirewa aka turo kofar, fisgo ni yayi na fada kanshi, muka leka kofar a tare. Su Hajiya, Mama, Nana Zaytoonah. Da sauran dangi.
"Alhajin Allah!" Inji Nana, "Ke dai ba zaki hutar da ranki akan Hammayo ba?" Inji Zaytoonah. Da sauri na sauka akan gadon, ina me nufar banɗaki na hada mishi ruwan zafi, kasancewar ana sanyi. Sai da aka gama mishi ya jiki ya shiga ban dakin yayi wanka, na isa bakin kofar bandakin na buga amma yaki budewa, ganin haka Nana ta ce. "Tow tow zamar uwar me muke musu, Alhajin Allah bude tazo ta wanke maka bayanka."
Wayyo Allah wata irin kunya ce ta kama ni, take na diririce kafin na gama dawowa nutsuwa sun gudu abinsu, suka ajiye kayan Abincin da sukazo da su. "Nasan sun gudu oya rufo kofar kizo kiyi aikin lada."
"A'a ni nayi wanka na"
"Tow rufe kofar" ban ki jin nashi ba, na rufe kofar, juyawar da zan yi na ganshi tsaye daga shi sai yar gajeran wando. Kunya ce ta kama ni na juya, sai ji nayi ya riko ni.
Ba zance kome akan lamarin ba, sai dai da na biye shi da ya ajiye min kunyata cikin asibiti sai dai ni ina da kunya kuma kunyata tana da mutunci. A daren ranar aka sallame shi, gidanmu da yake jikin gidansu Mama muka tare, ni a nawa tunanin za a ce bai da lafiya, amma ina ban da Majid, a daren sai da na hada da magiya wai ba zai kyale ni ba, sai ya rama abin da na mishi, a dai takaice ya min dakar sakwarar shege. Har asuba ya manne min yana makale da ni, sai da yaji za a shiga sallah ya janye daga jikina ya shiga ban daki yayi wanka da alola ya tafi masallaci, nima wanka nayi da Alola na gabatar da sallah, ina azkar ya shigo min. Nan ma naga yana niman kafi shayi, rudewa nayi kamar zan yi kuka, amma babu yadda na iya, haka na bashi damar ya zane ni son ranshi. Kafin ya janyo ni muka yi barci.
Sauran kwanakin da suka biyo baya, har su Nana sun tafi, Anisah ma Mama tace ba zata zauna mata ba, ta tafi Hajiya ta gyara kayanta da ta lalata. Tun daga ranar muka bude wani babin soyayya da kaunar juna, nayi kyau nayi kiba.