Sashe 53
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
{Greed for Money is the roots of all evils🫀} Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu *025* "Daga yau kada na kara jin kin ce wani abu akan Aryan, ko me kuwa idanunki ya gani ko kunnuwarki suka ji, babu ruwanki da Yan uwana. Ba zaki raba ni da shi ba ko ina raye ko bana raye Aryan shine Magajin Mamman Ba'are, kin fahimta bani da shakikin da ya kai shi. Sannan ni ba d'anki ba ne da zaki tsara ko ki saka mishi idanu akan abinda yake, Waccan da kika ce ba zaki amshe ta a surukarki ba ita ke da ikon saka ni ta hana ni. " Jikinta yayi matukar sanyi, tabbas a duk lokacin da zai yi magana yana gaya mata ba ita ta haife shi ba, Sa'adatu ce ta haife shi. Kafin ta gama tunanin abin da yake gaya mata, ya kara dukarta da wasu kalaman masu zafi da ciwo. "Kamfani namu ne, kuma ni na saka Hajiya tayi murabus. Domin a cigaba daga inda ta tsaya Hajiya ni da kika ganni ina son mahaifiyata, kuma ina son ganin ta huta idan kina son mu zauna lafiya da ke, ki fita hanyarta idan ba haka ba duk abinda ya fito bakina sai na gaya miki. Ba iya ke ba duk wanda ya ƙara shiga harkarmu sai na kure mishi lissafinshi. And ki tattara kafarki, ki koma inda kike zaune bangaren Sa'adatu na Yaranta ne babu wanda ya isa kara zuwa ya shiga tsakanin Yaranta. Da kika ce tana ganin abin da nake aiakatawa tana gani, kema kina ganin lokacin da d'anki yake wulakantata kin iya dakatar da shi?" "Majid!" Hajiya ta kira sunanshi, domin bata son abin da zai d'aga mishi ciwonshi, su shiga damuwa. "Hajiya kada ki damu, ita ta manta lokacin da take fadar cewa a kuntata miki ko zan bi hanyar da suke so, bayan da saninta d'anta ya haramta min ganin Mahaifiyata, ta manta da saninta danta ya nisanta ni da kowa nawa, yanzu Nana don bakya tsoron Allah kin zo zaki hada ni faɗa da dan uwana, ki tashi tun muna girmama juna ki fita kafin raina ya b'aci mu samu matsala." Bai gama rufe baki ba,Nana ta mike a hankali zata fita Aryan ya ce mata. "ki gyara hijabinki." "Tow!" Ta fada tana gyara zaman hijab din, har zata fita ta juya tana kallon Abdul Majid da yake cin naman a nutse. "Ka yafe min abin da nayi maka, nasan na cutar daku amma don Allah a wurinku nake samun damar yin yadda naso don Allah ka yafe min." Ta sharce hawayen da yake zubo mata, sannan ta fita tana kukan sarari da na zuci. "Baka kyauta ba, da baka gaya mata haka ba." Murmushi yayi ya cigaba da cin abincin shi, "Hajiya idan ba haka yayi mata ba, Nana bata da kirki haka kawai xata mai dani abin zargi." Inji Aryan yana cika bakinshi da namar gaban Abdul. Harara ya watsa mishi yana faɗin. "Kaje kaci naka mana." Da sauri ya wafci namar yana faɗin. "Ba zan iya cin nawa ba, naka zanci gaskiya wannan gashin yafi nawa dad'i." Lokacin da Nana ta koma taci kuka har ta godewa Allah, tana me kara ganin laifinta ne duk kiyayyar da Yaran Hajiya suka nuna mata laifinta ne. Kamata yayi ace su taso sama da sauran jikokinta tunda ba karamin dadi taji da aka haifi Abdul Majid ba, amma daga baya kawai ta tsane su idan ta tuna cewa a caca aka ciyo uwarsu sai ta ga kamar sun zo da wani irin gurbataccen jini mara kyau da amfani. *** Zahrah. Wata na guda ina nan bana kome sai aikin noma, idan na koma dakinmu kuwa idan na kwanta dakyar nake barci, abincin da nake ci baya isa ta Sannan duk tsawon wannan lokacin, ana kawo min abin da Yallabai yake kawo min, Addah take amsa tana cinyewa ko Ummi bata sani ba, ranar da dubunta ya cika, ranar ya fara fita domin ya warke kamar bashi ba, da kanshi ya kawo min abincin sannan itama Reshmah bata san cewa zai futa har ya nimo ni ba, tunaninta ai abinda ya faru zai saka mishi shakkar nima ta ne, sai dai shi namiji ne da yake da ra'ayin kanshi, babu wanda ya isa ya sauya mishi. Lokacin da ya zo ya zauna yana jiran na dawo har dare yayi yana zaune a wurin karewa da wayar da suke amfani da shi a dan kauyen, ya kira Aseem ya kawo mishi abin sallah, a wurin suka yi sallah suna hira, tunda ya zo Addah ta leko ta ganshi tsoro ya kama ta, yana tsaye a wurin mamaki ne yake kara kama shi ya cewa Aseem ." Kuma kai ne kake kawo mata abincin?" "A'a Ghadafi ne!" Gyada kai yayi. Har aka yi sallah Isha ban dawo ba yasa aka tara kowa. "Ghadafi ita kake kawowa abincin?" "Eh Sultan" ya fada yana kallon Adda. Dafe kirji tayi tana kallon shi. Zuba mata idanu yayi, ya cewa Aseem. "Ita wannan ita ce ta je ta gayawa Reshmah ina fita da Zeehrah!" A fusace Aseem ya mike, "kyale ta ku tambayeta." Fito da Addah aka yi ta zube akan gwiwarta. "Ina kike kai abincin da ake kawo miki " "ina bata ne!" Ta fada bakinta yana rawa. "Karya take Sultan, cinyewa take kullum aka kawo, sannan Zahrah yau ce bata dawo da wuri ba, tana can lambun wiwi tana noma a wurin.." Sakin baki yayi yana jin kamar a mafarki yake jin labarin inda Zahrah take. Bai ce uffan ba ya mike tare da barin wurin. Aseem yana take mishi baya, ita kuma Addah tana zaune a wurin da wasu masu gadinsu. "Ummi Allah ya tsine miki albarka." "Ash, Addah babu abinda zai same ni domin kuwa tsinuwar da Zuzu take miki a duk lokacin da wani ya kwanta da ita ya ishe ki zuwa lahira lokacinki bai yi ba, Addah da na haifi ɗan da xan tura shi karuwanci gara na kare rayuwata babu d'a babu jika in gaya miki, Munaisah ma da muka yi raba dai-dai akanta. Hakkin Uwarta da ta bari kika kashe mata ne. Bari na gaya miki wallahi ba zan barki ki karasa cutar da Zahra ba, muna nan sai na saka an illataki kafin mu bar nan wallahi." Shiru Addah tayi tana tsoron abin da zai kuma faruwa. ---- Yau kan babu abincin da aka kawo min, nayi noman har na kasa domin idan na sunkuya sai na fara jin amai, yunkurin aman yasa karfina ya ƙare, har rana ta fadi ina kwance a wurin, ita kanta Baby kamar bata da lafiya, jikinta yayi zafi rau. Haka yasa na kwanta a wurin daga nan ban kuma sanin kome ba, domin duhu ya lullube gani na. Kamar daga can nesa nake jin ana kiran sunana, dakyar na bude idanu kamar shi na gani, na saba yin mafarkin yana zuwa ya ce gashi ya samu lafiya ya dawo kenan, sai na kara lumshe idanuna. Har tsawon kwanaki biyu, ban san waye a kaina ba, a wannan kwananki biyu Baby ta murmure kamar ba ita ba, nice ulcer ta min mugun kamu, saboda babu abinci me kyau. Sannan jinin jikina yayi kasa bani da wadataccen jini. Don haka ya bada na shi aka saka min, na cigaba da samun kulawa har rana ta uku sannan na farka. Ina ganinshi na zuba mishi ido. "Zeehrah ya jikin?" " Da sauki" "Allah ya baƙi lafiya!" Daga haka na lumshe idanuwa na, haka ya gama zama har ya gaji ban ce mishi cikanka ba. Asalima koyawa kaina fita harkar shi nake son nayi kamar yadda suke bukata, don haka na fita hanyar shi ban kuma shiga rayuwarshi, washe gari da aka kawo min Baby tayi bul-bul da ita gwanin ban sha'awa. "Maa Yallabai ya ce kada ki kara bata nono tana shan madara." Yarinyar da bata wuce wata uku ba. Kamar tasan abin da nake tunani a raina, sai gashi ta ce min."Eh akwai madarar da zai mata,kema Dr ya ce zai bada magani a baki." Ban ji dadi ba, amma kuma zaman mu a asibitin ya sani murmurewa nima. Sai dai idan yazo bana mishi magna, haka idan yazo yayi ta magana juya mishi baya nake, haka nurse ta kawo min maganin da zan fara sha, rabin maganin na gyaran jiki ne da SUPPLEMENT na islamic. Ban taɓa zatan akwaisu ba, haka nayi ta sha har aka sallame ni, da na koma dakinmu a lokacin ne na fahimci Addah har lokacin bata dawo ba, sannan an sauke min aikin da nake yi, bana aikin fari balle baki, ina nan daga na tsoma biyar sai na wanke goma. Kwanana biyu ina barci na dora Baby a cikina ya shigo ya d'aga ta. Bude idanu nayi ina kallonshi, kafin na juyar da kaina. "Zeehrah wai me na miki ne?" "Baka min kome ba, kai ne dai nayi maka laifi" "Ban gane ba?" "Ok zaka gane!" Na fada ina kokarin sauka daga gadon, rike hannu yayi yana faɗin."kiyi hakuri ki gaya min laifina." Girgiza kai nayi nace mishi. "Wallahi baka min laifin kome ba, kawai bana son kana zuwa inda nake ne don Allah." Yadda nayi maganar yasa shi kallona. "Meye ya faru?" " A hankali na zare hannuna cikin na shi, a kundin ƙaddarata ba zan tab'a cike shi ba tare da na ambaci Yazid ba, domin shine mutum na farko da ya tare min masifar matarshi. Hakazalika ba zan tab'a rufe labarina ba tare da gayawa duniya waye shiga gare ni ba, ya min alkhairin da babu wanda yayi min, ƙaddarata rubutacciyar al'amari ce da ba zata tab'a shallake ni ba tare da na bayyanawa duniya girmansa da darajarshi ba." "Ki gaya min meye nayi miki da baki son na tsaya a hanyarki." Yadda yayi maganar cikin Rarrashi yasani fashewa da kuka idan na tuna abinda mutanen nan suka min sai naji kamar zan mutu, da b'acin rai. Rufe idanuna nayi gam naki kallonshi, a hankali na had'a kaina da gwiwa ina wani irin kuka na takaici da bakinciki. Cizon bakinshi yayi ya ce min "me kike so?" D'ago jajjayen idanuna nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Kawai ka rabu da ni." "Ba zan iya ba. domin lokacin