Sashe 138
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Amma babu Paul sai yan aiki wai ya mutu bayan tafiyar Munaisah sai yarinyar da aka bar mata tarin dukiya kamar hauka. Lokacin da ta ganni, da gudu ta faɗa jikina. "Kece Mamana?" Hawaye ne ya zubo min, muna zaune sai ga lauyoyinta dama wai jiran wani daga cikin dangin mahaifiyarta ake, Babanta ya ce a damkata ga danginta, yarinya yar shekaru takwas. Kuka nake na saka hannu da kome, muka tattaro abinda zamu iya kwananmu biyar muka dawo Kamaru nace lallai Zuzu tazo ina son ganinta.
Jin haka suka tattaro ita da Mijinta, ta manta da rayuwar Yarta baki ɗaya. Ta amshi sabuwar ƙaddararta, lokacin da muka zauna nasaka aka kira min Lilly, sai da uwar ta zubda hawaye domin babu abinda ya fi jini ƙarfi, na mika mata takardun yarinyar da kome na dukiyarta. Na tura mata dukiyar. Dawo min da shi tayi. "Ko a lahira, zan amsa sunan Uwar Fatima ne, amma ki saka a ranki ba tawa ba ce taki ce, kada ki sake ki gaya mata cewa nice na haifeta. Zahrah taki ce ba tawa ba. Idan da nasan don haka kika kira ni da ban zo ba, ai na gaya mata ke ce mamarta ni Yayarki ce ina zuwa gareta a madadinki, hatta waɗannan abin ba nawa ba ne naki ne."
Wannan wacce irin rayuwa ce? Haka Munaisah ta bar min yar, ko dukiyar bata waiwaya ba.
Haka na kama Yaran duk na rungumesu. Haka na cigaba da rayuwa,. ina zaune kawai sai ga Amirah ta dawo min. Baraka ma d'anta namiji ta yaye ta kuma dauko magana. Haka Ummi itama tana haihuwa ina ga Arba'in kawai tayi ta kuma dauko magana, Ni ce dai daga guda biyun nan ban kara ba. Sai rike na wasu.
Daga baya dan renin hankalin yake gaya min shi ne yake family plan, nace yayiwa kanshi.
Haka muka cigaba da tafiya, Hajiya ma ta dawo gida ta zauna ina kula da su.
***
Bayan shekaru masu yawa, ina rungume da jikata yar wurin Zahra, da ta haifa da wani dan majilsa. Don Allah yakara bunƙasa Majid, ya gina asibitinshi shima.
Amirah da Zahra suna aiki anan dukkansu nurse ne, Alhamdulilahi domin naci ribar hakuri, kuma Dukansu na aurar da su, sai Alfah da take karantar likitanci itama, naji Uban yana cewa Abdul Majid Aryan Mamman Ba'are ya mata miji Nijar can zata.
Mimin Zaytoonah ma tana wurina.
**
Ina zaune ya shigo na ajiye Amnah, na amshi jakarshi. "Barka da dawowa litikan zuciyata, sojan rayuwata. Chairman din duniyata ya aikin dai?"
"Alhamdulilahi ki kira Zahrah ta amshi yarta yau zamu wuce Baihak za ayi nadin sarautar Maina, ban isa da Abin kunya ba."
"Da gaske?"
"Yes of course"
Raka shi nayi zuwa dakinshi yayi wanka na bashi abinci yaci, sannan na fara ciro kayanshi da nawa da zamuyi tafiyar da su. ina gamawa na kira Zahrah. Ina gaya mata ta fara rikici kamar zata fasa ihu. "Mami don Allah ina xan.kai yarinyar nan wallahi yayeta zan yi ko na kaita wurin Umma Zuzu!"
"Kaniyarki nima haka na yi fama da ku ni daya, oya kizo ki amshe ta sati zamu yi mu dawo."
"Mami!" Kashe wayar nayi domin Yarana sun san lagona, yanzu sai su sauya min lissafi. Da dare suka zo suka dauki Yarsu.
Gida na kuwa na barshi a wurin su Mama da Hajiya. Na bar Amina da Aliyu.
**
Mun sha shagali na bikin nadin sarautar, sai a lokacin muka kebe da Yarinyar nan, ta kai ni bangaren Uwargidanta, wacce na yabada da hankalinta da kirkinta kwarai da gaske, Yanzu King Muhammad Maina yana da irin wannan matar ya auro fagal. na fada a raina. "Aunty Zahra ni ba fagal ba ce " rike bakina nayi, ta juyo tana kallona.
"Kada ki gayawa Ya Majid ya karanci abinda yake ranki, domin zai gayawa Maina shi kuma zai cire rai da zan dawwama a rayuwarshi."
Ta fada tana kyafkyafta idanu. "In sha Allah, Queen!"
Na fahimci kowacce rayuwa da Y'a mace zata yi tana yin shine akan abu uku, Na farko Mijinta, na biyu Yaranta na uku domin kanta, abin da na fahimta kenan akan Queen, yaranta kyawawan gaske suna zagaye da ita domin wani irin so take musu, ina ganin tana share hawayen da yake zubo mata. "Me yasa kike kuka?"
"Nasan ba xan yi nisan kwana ba ne, a koda yaushe mutuwa tana kara kusanto ni. Gashi wannan shine labarina The Last Empress"
Amsa nayi ina rarrashinta, tare da saka mata iklasi da Tauhidi abin da na fahimci ya yi rauni a rayuwarta kenan. Na nuna mata ikon Allah ta hanyar bata labarina, sai gashi ta ware sannan wani abu da na fahimta tsoron kada wani abu ya faru da ita ta zama wata iri.
Haka muka bar kasar muka dawo tun a jirgin nake son karanta labarin amma Ya hanani, muna isa gida bayan an huta mun nutsu kanshi yana cinyata, na bude farkon babin.
"Bakar wata!"
"Ke tsaya bana son labarin ban tsoro muje ki min tausa.."
"Kayiwa kanka ba zan baka labarin ba nan gaba in sha Allah."
Cak yayi sama dani zai wuce dani daki, Aliyu ya ce. "Ikon Allah na zata kun tsufa baku soyayya ashe, shi yasa kuka kore mu, tow sai an jima Ram Layla."
"Yawwa Romeo dan sa'ido, me leken sirrin mutane!" Da gudu ya fita dan kimanin shekaru sha tara, shi da Aminah.
Bayan shekara daya nayi bikin Alfah, ta tafi Nijar Aminatu kuwa Jikan su Mama ya ce yana sonta aka sha baki Sharhabil. Sai dan autana wai ce mishi suke dan hauka. Wata biyu da bikin, Allah yayiwa Nana rasuwa a hannun Alhajin Allahn ta, tsakanin Nana da Malamijo sati goma sha daya, ya rasu shima. A rasuwar ne muka sake haduwa Familyn Wodabbe aka yi hoton Familyn bakiɗaya.
Addah kuwa tana can bata mutu ba, amma Allah ya daura mata jinya har da rubewar gaba sakamakon Cancer da ta kama. Muna yawan tattaunawa da Majid akan matsalarta. Nima ta bangaren lalurar kunnena sai godiya, na hakura domin har sau biyu ana min aika babu ji sai da wannan karamin abin jin. Haka daman rayuwa take, ba kome kake samu dukan ba, tunda na samu farinciki shi me sauki ne, Daman ai farkona na gani abin damuwar me zai faru a tsakiyar Alhamdulillahi Allah yasa mu cika da imani...
Alhamdulilahi anan na kawo karshen bakin haure, wanda abinda ake nufi da sunan yan gudun hijira. Na gode sosai da bibiyar labarin da kuka yi.. sai mun hadu a ( the La empress) wanda zai zo maku a free in Sha Allah.....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce.