← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 138

Sashe 137

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fata ta kuwa har wani glowing take saboda nutsuwa da kwanciyar hankali, watan mu guda,.na fara wani irin jin sanyi idan ya fita office zan gudu wurin Mama, nayi ta nad'e kaina da buya a cikin dumi tunda ta ga haka tace min ciki nake da shi,.na tura mata baki. Labarin cikin yazo min da ban mamaki domin a lokacin take gaya min ai ya ce mu da Nijar sai sallah da wata hidima, zai zauna a kamaru dama can nan ne mazauninshi, kasa magana nayi ta ce min. "Dan kwali yaja hula ko!" Kifa kaina nayi a cinyarta har barci ya dauke ni. A can Nijar ma dake sun tafi da Alfah,wani irin riko Hajiya take mata kamar ta maida ta ciki itama yarinyar tana son Hajiya da Nana..

Sai da cikina ya shiga wata shida, kafin Malamijo ya dauki hakkin su Alhaji Isma'il Wodabbe ya kira yazo ya amsa ya bashi hakuri ya kai shi har gidan gonarsu, ya ce dukiyar mahaifinsu ne, shi da kanwar shi wacce har lokacin bata sauko daga fushin da tayi ba.(wato Innar Almamoon 🤣😂😹)
Bayan ya koma Nijar ya taso Inna har Kamaru, a lokacin da suka hadu kuka tayi ta yi,tana faɗin. "Kiri-kiri ka Kore mu ka bamu Iya adadin shanu goma sha biyar kace na yafe maka"
"Uwata kiyi hakuri, ki yafe min nima zuri'ata ta samu zaman lafiya da nutsuwa." Ya bata labarin abinda ya faru, ta share hawayenta, ta ce ta yafe kwanansu biyar suka koma. Jamilah da su Hajiya da Nana suna ta son ganina haka yasa Majid ya shirya min tafiya shi kan aikin asibiti ya rike shi, haka na tafi ni daya na.
Akan sati biyu zan yi musu, ina zuwa kuwa na tafi har marad'i. A can na kira Yazid na mishi maganar aure, idan yana da sha'awa.
Bai min musu ba, ya amshi Barakatu amma yace zai zo su daidaita. Naje gidan Munaisah itama ta yaye d'anta, sai rigima yake mata tana ta lissafi, .kwana ɗaya nayi a gidanta don naga ta dauko Nenne.
Ina cikin sati na cewa Aryan ya shirya min komawa gida, abin ya basu mamaki kwanana takwas kawai na ce eh gida zan koma, na kuwa dauko mana Nana da take fama da rikicin tsufa wai na hana Alhajin Allah kiranta. Nace matukar shine matsalarta muje ta zauna a wurin shi.

Lokacin da muka zo tana ganinshi ta ware, haka na cigaba da jan cikina ina turawa har ya isa watan haihuwa, wani babban rashin da muka yi ana shirin saka ranar Baraka, Allah yayiwa Amaan Mamman Ba'are rasuwa. A nan Kamaru Ashe sun zo shi da Hajiya domin daga airport asibiti suka wuce.

Ni ban sani ba, domin kwana biyu ina fama da nakudar tsaitsaye, duk da ba nan Majid ya karanta ba, amma ya kira wata incharge na asibitinsu ita ta nuna mishi kome ta kuma gaya mishi yadda zai min idan lokacin yayi, ranar da suka zo yana aikin dare, don ya tafi ya bar ni kwance a dakin Mama don tun da na fara haka su Nana suka ce a kawo ni cikinsu na zauna.
Haka na kwana ina fama, ashe sun ji labarin rasuwar domin a cikin gidan aka dawo da shi,ina jin sautin kukan Hajiya na fito na ji Mama tana faɗin. "Ba kuka zaki yi ba, jinya ya kare kamar yadda yayi fatan ya mutu a hannun dan uwanshi, ya cika a hannunsa."
"Waye ya mutu?"
Na tambaye ta, ina dafe bayana. "Amaan!" A hankali naji wani abu ya zubo min, na durkusa a kan gwiwata daidai shigowar Majid da dark green uniform.na likitoci. Da sassarfa ya iso gabana ya rungume. "Sannu Flower push!" Wani irin azabar da ta ciyo ni, ban san lokacin da na damke shi na manna mishi cizo ba, sai ji nayi kamar an b'antare abu a jikina ya sauka kasa bakiɗaya. Sake nishin na kuma yi wani ya sake durowa. "Thank You God for everything, thank you flower."

Haka Goggo Sume ta amshi Yaran, ni kuma ya gyara min jikina ya kai ni ban daki, sai da ya kwashe min kome na cikina, musamman jini me saka ciwon ciki, ya haɗa ruwa da kanshi ya min wanka ya dauki pant da pad ya saka min,. Sannan ya samu Yafendo ta dama min kunu da zafinshi yace na sha ya saka min ruwa, sannan ya gyara min kwanciya bayan ya saka min allurar barci, sumbarta bakina yayi ya fita, ya koma.kan hidimar gawar. Ana gama shirya gawar aka fita da ita, ya dawo ya sake kayanshi suka tafi makabarta, wato a lokacin da wasu suke kuka a lokacin wani yake dariya, bayan an gama wanke Yaran. Mama ta ce musu. "Aliyu ya tafi daren jiya, yau da safe Aliyu ya dawo, Allah ya rayaka."
Haka kowa jikinshi yayi sanyi, bayan dawowarsu daga makabarta, ya zo yayiwa Yaran Huduba, ban kawo zai saka sunan Mama ba kasancewar ina da Aamirah. Sai gashi ya musu huduba, Aliyu da Aminatu.

Mutanen Nijar sun zo ta'aziyar da barka, Allah ya takaita, ba suna.
Haka muka yi zaman makoki ni kuwa nayi kyau abuna. Zaman jego ba karamin dadi naji ba, Doctor yana shigowa muyi hira korar shi Mama take, kwananmu talatin da biyar, ya cewa Mma."Innani don Allah ta koma ɗakinta." Hajiya tana jin mu dake rasuwar Amaan bai barta ba.

Watan mu biyar muka je Nijar sallar azumi, daga can muka wuce Nijeriya. Lokacin da muka je kan Addah wacce take kallona. "Zulaihah mijinta yana kasan mijinki, Munaisah mijinta yana kasan naki. Ummi bata yi aure ba. Ke wacce irin mayya ce."
"Itama zata yi aure wanda yace zai auri Munaisah Allah bai yi ba, Abdul Majid shi yake son Ummi har an gama magana. Akwai sauran abu ne?"
"Wato da aka gaya min na zata karya ne, ke Shaidaniya ce a cikin siffar mutane."
Addah ta shiga ihu da tonawa kanta asiri, wannan bakin cikin yasa Zuzu ta kaita gidan Mahaukata, ta ce zata na zuwa dubata. Addah bata mutu ba, amma taga yadda Allah ya daukaka ni ya kuma daukaka rayuwata. Mijina kuma abokin rayuwata yana girmama kome nawa, wacce ta tsaya min mahaifiyata.

Anyi bikin Barakatu da Yazid bikin da aka sha hidima da ni da Majid muka tsaya a hidimar a matsayin iyayenta, yadda Majid yayi ta kafa sharudda na san ko bikin Alfah da Aminatu ne sai haka, mun kaita gidan mijinta da yake cike da sarauta, sai dai kuma na bata hakuri.

Sannan muka dawo, koda yake watan Oktoba aka yi bikin sai gashi sun zo a watan Fabrairu, na sha mamaki da Yazidu yake kaf-kaf da ita ko me zata yi yana faɗin. Tayi a hankali tasan bata da karfi, a bakin Mama nake jin labarin ciki ne da ita, don ni ta dauke ni a matsayin uwa ce bata sakewa ta gaya min kome, kuma yadda na ganta nasan babu matsala, sai da nayi kukan farinciki iyayenta har Kamaru suka zo kamar zasu kwanta na bi ta kansu. Suka gayamin wai mijinta ya saya musu gida a Kamaru su zauna kusa dani, wani irin farinciki nake ji, kome na kalla sai naga ya zame min 100 percent. Anyi bikin Ummi da Abdulmajid dan Hajiya Hadiza Mamman Ba'are, wacce ta sauko domin Aryan ya sauya wa kowa matsayi dan daga karshe Kamfanin Majid na Marad'i ya rike shi Abdul Majid din Hajiya Hadiza.

Sai daga baya kowa yake faɗin Ashe Majid waliyin Allah ne, Aryan tun mutuwar Amaan ya zama karkace aiki kawai da ibada da kula da dangi da Matarshi. Matan Alhaji Mamman Ba'are, Aryan ya maida kowacce garin iyayenta ya saya musu gida madadin na Niamey. Gidan kuwa Hajiya tace a sayar kawai ko a maida makarantar Amaan and Mamman Ba'are Memorial Islamic college. Domin ta haka ne za a cigaba da tunawa da bayin Allahn nan. Har yau Anisah bata yi aure ba, kuma bata da ma niyyar yi da ta fara bin kawaye, Aryan ya mata mugun duka. Kafin ta nutsu Allah ka shirya mu tafarkin addinin Muslunci.

Ummi ma suna maradi, dukkansu an sha gwagwarmayar rayuwa, sannan an kuma dawo ana morar arzikin da Allah ya tsaga mana, wato Zina bata da wata amfani. Duk yadda ka ɗauke ta ba hanyar arziki ba ne, gashi dai dukkansu babu wacce ba ta tab'a rayuwa ba, amma dake Allah ya dubi tubarsu sai ya basu mazaje na gari.

Nasihata ga mata da matasa, zina bata da fa'ida. Sannan a cikin.maza dubu dakyar ake samun ƙalilan da suke sonka domin Allah, kada rayuwar Zuzu ko Munaisah ya burge ki wallahi babu riba a cikinsa. Ga dai karshen Addah bata mutu ba, bata fasa ganin cigaban Zahra ba.

***
Ranar muna hira da Majid nake bashi labarin yar Munaisah, tashi yayi yana kallona. "Zahra kuma kika bar yar a hannun Paul?"
"Tow ya zan yi?"kwanciyarmu muka yi nazata maganar ta kare, bayan sati biyu ya ce na shirya zamu yi tafiya, amma na ajiye yan biyu."salon ka kara dura min ciki!" Murmushi yayi min kawai. Bayan kwanaki muka bar Kamaru sai gamu a Poland, kai tsaye gidan Paul ya kaimu ashe an san juna, anan muka samu kyakkyawar tarbar.
Chapter 137 · 0% Book details