Sashe 38
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dilla baya shan ruwa haka kawai sai da wutsiyar shi, idan har zai ajiye wani abu nashi tow duk yadda akayi ina iya jiyo kamshinsa domin yana nan kaɗan damu."
"Kana nufin yana kusa kenan?"
"Kin san waye Dilla?" Girgiza kai tayi ya ce mata. "Dilla ita ce dabbar da bata kwana a ko ina sai a tsakiyar busashen ganye, domin ko fara ne ya fada kan ganyen zata farka, Dilla bata kamuwa ta dadi sai da tarko. Don haka maharba basu iya kamata sai sun saka mata tarko."
"Tarko kuma?"
"Eh tarko ita ba a kamata da nama, ko abinci duk abinda tasan baya samuwa a daji bata cin shi, tarkon dilla na musamman ne domin raga ake watsa mata."
"Na gamsu Yallabai, amma taya zamu iya kama shi?" "Ai shi baya buƙatar tarko."."ban fahimta ba?" Mikewa yayi ya nufi dakin, ya watsa ruwa ya fito yana me zama ya ci abinci, bai kara magana ba kuma ita Uwar mugu tana son jin shirin Yallabai akan Dilla ne, tasan su basa shiri amma kuma bata zata al'amarin zai kai har haka ba.
-----
Lokacin da na iso tantin mu, tsayawa nayi a waje ina jin shewar Munaisah da Addah, d'aga labulen nayi muka yi ido biyu da ita, gimtse dariyar tayi tana faɗin. "Allah sarki Nennena." " Ba sai kin yi min wasan kwaikwayo ba!" Na fada ina kallonta, shiru tayi tana kallona. "Wacce ta tsare miki gaba ta tafi, sai me? Daga nan sai ki daura daga inda aka tsaya." Na fahimci abu daya, daga Addah har Munaisah babu ruwansu matukar kudi zai zo musu wallahi zasu bada kome suka mallaka, kai hatta rayuwarsu da zasu iya sallama ta, tow kuwa zasu samu kudi da ita.
Sannan wani abin mamaki shine kudin nan gashi nan amma ban san me suke da su ba, zuzu tana kwance nace mata. "Yan mata kina jin yunwa ko?" "Jiranki nake ai ki zo kaina, Zahra'u yunwa nake ji." Mikewa nayi na hada wuta, sannan na yan yanka kayan miya, na soya shi sama sama."
"Zahra'u a saka kifi!" Duba wurin kayan nayi naga babu kifi."Zuzu bari na amso mana kifin!" Na karbi jakar kudina na dauki abinda nake da bukata, na fito waje. Gidan Uwar mugu na nufa, har na isa ban hadu da kowa ba, sannan kowani tanti shiru ya dauka, buga kofar nayi, ta bude. "Zahra'u me ya dawo dake?" "Kifi nazo saya." " Kin ga kuwa jiya da daddare Addah ta kawo min shi na bata kuɗi!"
"Ta kyautawa kanta!" Na mika mata kudin iya wanda nake so, ina jin Muryar shi me cike da Amo ya ce mata. "A maida mata wanda aka kawo a sayar a hada mata da kayan abincin."
"An gama Yallabai!"
"Kuma kada ki sake ki kara amsar kayan kowa inji ni!".
"Tow yallabai, maza ki mishi godiya." Ta ce min, "iya na kudina nazo saya." Na fada ina juya fuskata. "Ba zaki mishi godiya ba!" "Ni ba rokonshi nayi ba, shi yayi niyya kuma nace bana so dole ne?" Na fada Ina kallonta. "Yallabai!" "Bata abin da take so!"
Ya fada yana me juyowa yana kallona, nima kallonshi nayi na dauke kaina. Ban san yadda zan muku bayanin yadda yake ba, amma Kyakyawa ne dai-dai misali, sannan yana da sura irinta sadaukan maza. Amma abu daya da kwakwalwata taki mantawa shine yanayin surar Aminin duhu, har yau ina jin haka a raina. Domin kirjinshi a wani murde yake, tsokokin da suka cika kwanjin shi kadai abin burgewa ne. Dafe kaina nayi sakamakon jin kaina yana wani irin kuwwa. Sai yau na tuna da shi sosai, duk da zuciyata bata samu zarafin hasasho min shi ba, sai yau. "Baki da lafiya ne?" D'ago kai nayi na kalle shi, kafin na dauke kai ina amsar kayan hannunshi. "Mai kyau!" Ya faɗa kamar rad'a.
Juyawa nayi na bar wurin, ko ina da kyau Allah ya min tsari da hada shirgi da wannan abin kamar dodo. "Amma kada ki sake fitowa, domin tsarina ne." Shiru nayi ban ce kome ba, domin kuwa ba zan iya cewa komen ba, don naga yadda sansanin yayi kamar an yi shara. Haka yana nufin yana da karfin faɗa aji, ina isa tantin mu na ce musu. "Ashe yau ba a fita?" Sai lokacin Addah ta ce min. "Eh an gaya min jiya doka ce idan yana nan ba a fita." "Kuma Adda sai kika barta ta fita?" Zuzu ta mike dakyar cikin takaici. "Waye ya sani ko an shirya haka ne don a dauke Zahra din tunda yanzu anyi walkiya kowa yasan kowa."
"Allah ya tsare mana ita." Inji Zuzu, ina ga cikin nan ya karawa Zuzu masifa, domin faɗa tayi ta cigaba da yi, tana hararar Addah. "Na gaya miki ban da fada." "Ke kyale ni nayi magana, me aka yi aka yi son zuciya."
"Tow Allah ya baki hakuri!" Daga haka na tafasa mana taliyar da miya, na zubama kowa zan zauna uwar mugu ta shigo ita da Balali. Ajiye mana kayan yayi ya juya ya fita. "Daga yau kada wani ya kara kawo mana kayan Abincinsa."
"Hmmmm!"
"Inji yallabai ne, ba inji ba!"
"Tow ai bin na gaba bin Allah, ina zamu samu wannan kayan dadin naga har da madara."
"Na Zahra'u ce, ba na ku bane."
"Ikon Allah Zahrah an fara dan waken zaga ye ne?" "Ita ba haka take ba, domin har yau bata dagula kuruciyarta da sabon Allah ba " inji Ummi tana tattara kayan, wato na fahimci a dakinmu akwai wani irin yaƙi dake tsakanin Ummi da Addah, tsakanin Adda da Zuzu, sai suka saka ni a tsakiya, duk yadda aka kawo min duka zasu kare min, "kinji dadi Zahra sai ki saka idanu akan yan uwanki. Domin kada su kawo mana hayaniya."
Ta fada tana kallon Zuzu da Ummi da Munaisah da addah, ban san me yasa take yawan gaya min haka ba. "Na yarda da yan uwana, don haka ba zan sakawa kowa idanu ba. Kawai duk abinda kika ga ya faru tun can rubutacciyar al'amari ne."
"Gaskiya kan!" Inji Addah tana kasa da kanta, domin wani lokaci idan addah tayi wani abu yadda kasan mutuniyar kirki. Fita tayi ta barmu a wurin, na zauna naci abinci nima,
Haka muka ci muka koshi,bamu fita ba sai can yamma da aka ce mana zamu iya fita wanka, Zuzu da Ummi da Addah suka tafi, ya rage daga ni sai Munaisah, yadda bata ce min kome ba nima kuma ban saka ran xan yi mata magana ba, yadda take rayuwarta cikin nutsuwarta ba zaka ce uwarta ta mutu a ranar ba, domin ta warware kamar ba ita ba. Lashe bakina nayi ina gyarawa Yakumbo kwanciyar ta.
"Zahra'u!" Na juya a hankali ina kallonta. A hankali ta matso kusa dani. "Don Allah idan kin samu damar fita daga nan, ki nemi wannan number please Zahrah." Cike da Mamaki nake kallonta. "Murmushi tayi tana faɗin. "Zan fita mana, zan tafi nesa dake idan ina ganinki zan iya aikata mugun abu akan ki. A wannan wurin ba uwa ba d'a, kowa ta kanshi yake kuma zaka iya aikata kome saboda kuɗi. Fatana daya ki fita daga nan sansanin domin ba sansani ba ne, wuri ne na biyan buƙatar kai."
Baki daya sai ta kara min rud'ani, sama da wanda nake ciki ina muka kawo kanmu? Ina muke raye? "Munaisah me yasa ba zaki min bayani a nutse na fahimta ba?"
"Idan na miki ma ba zaki gane ba!" Muna zaune a wurin har su Addah suka dawo, Nima da ita muka fita, muka je wurin wankan, baki daya sai na kasa wanka na saba sai dare nake wanka,.don haka na juya ina faɗin. "Ke bani iya wanka sai dare yayi." "Tow ai shikenan, ki je abinki." Haka na dawo na barta a hanya na hadu da Aina'u. "Naji ance yallabai ya tura miki da abinci, tow wallahi na rantse da Allah ba zan dauka ba, itama wancan me kama da zabiyar sai naci B... Ubanta, domin ba zata kwace min masoyi ba, shegu Mayun kudi. Ki saka idanu ki ga abinda zai faru."
Rab'ewa nayi na wuce ina xan iya da haushin ta, don haka na koma tanti na kwanta. "Baki yi wankan ba!" "Wurin cike yake da mutane ba zan iya wanka a gabansu ba."
"Kuma dai!" Inji Addah.
Haka na kwanta muka yi ta hira har lokacin sallah yayi, sai lokacin Munaisah ta dawo. Kusan ma rikota akayi . "Me ya faru?" "Ita da Aina'u suka yi faɗa suka fada wuri me zurfi, ita kan ba a same ta ba. Sai Munaisah aka samu." Hadiye yawu nayi cike da tsoro domin nasan karshen mu yazo. Ihun Tumba muka ji tana faɗin. "Wayyo Allah na, kun kashe min fitilar dake haska min gabana wayyo Allah ka dawo min da Yarinya ta. Me tayi muku." Yadda take ihu yasa kowa jikinshi yayi sanyi.