← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 138

Sashe 77

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmushi tayi tana ci da shi, "Hamma kai zaka ajiye ni yau a makaranta don Allah." Ta fada tana miƙewa, "Salele zai kai ki, ni bana son gulma haba don Allah idan ba munafurci ba, taya za'ayi ki maida min jika direba, idan ba munafurci aka hada don a cuce min shi ba." "Nana kanwata ce fa." "Hmmm! Na dai ji wannan." Da gangan Nana ta hana shi tashi, sai zai mike ta kawo mishi wani labari mara kan gado, ita nan don kada ya dauki Zaytoonah. Karshe Aryan yana shigowa Zaytoonah ta mike. "Hamma Aryan muje ka ajiye ni school." Ta fada fuskarta a had'e, "oho dai sai dai ariyan din ya kai ki, amma ban da jikallena ba." Don bakinciki sai da Zaytoon ta ji kwalla yana zubo mata, a gurguje Aryan ya sallami Hajiya da take kallon rigimar Nana da Zaytoonah. "Nana me yasa kike mata haka?" Ya tambayeta. "Haka kawai zata mai da kai bawanta." Ta fada tana zumburo baki , "Nana ai duk namiji bawan mace ce, matukar ya san ciwon kanshi. Koda bai bautawa Matarshi ba, dole zai bautawa kanwarshi da Yarshi, Nana Zaytoonah marainiya ce, sannan ta baro Cameroon tazo nan domin mu, ina ga ita ai kamar jikarki ce."
"Ni ba jikata ba ce." Ta faɗa tana wani b'ata rai. "Na ji ba jikarki ba ce, shi kenan ki daina ci mata fuska akan idanuna, na roke ki."
"Haba Alhajin Allah, sai ka roke ni ne? Kawai kace min Nana ki daina sai na daina, meye a cikin idanu banda ruwa." Daga haka ya kashe bakin Nana, daga nan ya mike ya musu sai ya dawo.

Hidimar kasuwancin ne ya kai su, har Poland don ba karamin ci-gaba za a samu ba, don haka sai yayi amfani da wannan damar tare da ganin likita, wanda yayi nasarar gano matsalarshi, sannan ya ɗaura shi akan magani. Kwanakin shi goma sha daya, gobara ta kama wani part na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES.

Zahrah Buba.
Karatun da ya sako ni gaba, yasa bani da lokacin kowa sai na kaina. Sai wani dan ajinmu me suna Sauban yana da matukar kirki. Yau ma daga dakin karatu muka fito, ya ce min. "Fatimah zaki iya tafiya don ni zan shiga cikin makaranta, kuma kin ga yamma tayi."
"Haka ne, sai gobe kawai." Anan muka yi sallama na wuce gida, a bakin get din makaranta na hadu da wasu yan department ɗinmu, dauke kai nayi domin daya daga cikinsu mai suna Abdullahi ya saka min idanu, Abdullahi yana masters ne amma irin yaran nan ne marasa jin magana, a bakin Sauban nake jin babanshi mai kudine kuma dan siyasa ne, haka yasa yake yadda yake so, duk da wannan abin bai taɓa burge ni ba, domin ni karatu ya kawo ni ba shashancin ba, kodon na cikawa Yazid alkawarin shi,zan tsaya nayi karatu.
Har na tsayar da abin hawa, iskanci da rainin hankali Abdullahi yake min, ina shiga na sauke ajiyar zuciya. Ina jin wani abu yana sauka a raina, don ba ƙaramin abu ba ne, Abdullahi ya kunyata mace a gaban jama'a. Haka yasa Sauban ya gaya min nayi a hankali da shi. Sannan ganin yadda ake shakkarshi yasa shi jin shi wani jan wuya ne.

Mun hadu ne ana sallah layya saura kwana biyar lokacin da aka bada hutu, ranar da mota na shiga makarantar, nazo zan fita kawai ya tare hanya, kuma ya hana kowa fita, haka muka zauna a cikin makaranta har sai da Den na makarantar ta fito da kanta, shine ya bada hanya amma tabbas bamu ji da dadi ba, domin bai da mutunci. Haka yasa yana bada hanya muka fita, ina cikin waɗanda suka fita da mugun gudu, tow ko me ya gani ya ke bibiyar rayuwata oho, ya dai turo min wani yaro na bawa Yaron hakuri akan cewa ni matar aure ce, mijina yana nan. Amma mutumin nan bai kyale ni ba, sai ma kara adabbar rayuwata yake, don ko da aka dawo hutun sallah, bai daina bibiyata ba. Zuwa yanzu kan sai hamdala kome yana zuwa min Cikin sauki da nasara. Bayan ya turo yaron sai da ya kuma tare Sauban da maganar banza, haka yasa Sauban ya gaya min abin da yake nufi, shi damuwar shi na zama budurwar shi na wucin gadi, sai kace wacce bata san ciwon kanta ba, don Allah ya zanyi?....
*Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta.......*
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400, 07035133148
#Mai_Dambu ce
[4/21, 7:33 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*039*
*Wannan shafin domin ki Maman Husnah 😍🥰❤️*

Ban yarda nayi wani abun da zai janyo shi jikina ba, domin kuwa cikin shigar kamala da mutunci nake, sannan a yadda nake jin labarin abin da ya faru a can baya. Babu dad'i domin idan yarinya bata yi mishi ba, a gaban jama'a zai kunyatata, sannan yayi mata sanadin barin makarantar, ni idan na bar makarantar ina zan ni? Waye zai tsaya min. A hankali naji zuciyata tana gaya min Allah yana sane da lamarina ban da Allah waye ya raba ni da fitinar Addah? Ban da Allah waye zai min nisan kwana har yau na zo nan, nasan ko a mafarki ba xan tab'a kawo kaina nan ba, amma sai ga shi Allah ya kawo ni, ya saka min da wasu abubuwan da ban roka ba,
Tuna wannan abin da nayi yasa na fara niman agajin Allah, akan Abdullahi don bana son dalilin da zai saka a ce min nima wani abu mara dadi ya faru da ni a makaranta. Haka yasa na yawaita addua, ba dare ba rana, yawan addu'a yawan sab'ani da nisan da ke tsakanin mu, haka yasa kowa yake kallon kamar ya kasa min kome, ni nasan Allah ne ya shiga tsakanina da shi, ba iyawata ba ne kuma ba wai don nafi kowa ba ne, a'a Allah ne yaso haka.
Haka lokaci yayi ta tafiya har muka kammala aji daya, muka shiga biyu abin ba wuya fa. Koda yake kana naka Allah yana na shi, na Allah shi ne gaskiya amma tabbas rayuwarmu karewa take, a lokacin Amira tana da shekaru biyu a duniya, ga ta da farin jini, haka yasa nake kara boye ta gudun kada bakin jama'a ya tasirantu akanta, don idan baki yayi yawa akan Yaro ana iya samu nakasu, sosai na ke boye ta.
Nima Babba ban da ina saka Hijab da dogayen riguna dayawa cewa suke ni somalians ce, domin yanayin fata ta da jikina. Koda nace musu fulani ce ni ba yarda suke ba, na sha gaya musu ni Daga Nigeria nake amma sai su ce eh ai haka kowa ma yake boye Asalinsa. Haka yasa bakiɗaya nake jan bakina nayi shiru ina kallon ikon Allah

Somewhere in south Carolina.
Babban gidan rawa ne, da yake tashin sautittuka. Dauke take da tire izuwa gaban wasu gungun matasa, maza da mata. Ajiye musu tiren tayi tana cire kofi nan glass din kan tiren. Sanye take da farin shirt da top akan rigar, sai skirt iya gwiwarta. Cikakkiyar bafulatana Zulaihah tsaye ta tufke kanta, da yake sanye da katon Black bam. Sannan ta ɗauki tiren zata juya, wani matashi a cikin matasan ya mari mazaunanta, bata kula shi ba haka ta wuce inda suke ɗaukar kayan, ta tsaya. "Zully ya dai?" Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Ba kome Ra'if." Ta faɗa tana shafa bracelet din hannunta. "Ko kin tuna da Baby da Zeehrah ne?" Juyawa tayi tare da washe hakori, "Eh kusan haka ne, amma a yanzu basu ne a tunani na ba, yadda zan bar wannan aikin nake."
Murmushi yayi ya karkad'a haɗin da yake sannan ya ce mata. "Dala talatin ake biyanki duk sati biyu, sannan kina sane da cewa Mr Williams ba zai kyale ki ba sai kin biya shi dukkan kuɗin shi da ya saka akanki sannan zai barki ki tafi, bazan baki shawarar sabawa Allah ba, amma ki nemi yadda zaki yi, ki biya shi kudin shi in sha Allah akwai aikin da ya fi na shi." Murmushi me ciwo tayi, tana wasa da bracelet din hannunta, kafin wasu gungun mata suka shigo, suka ce ayi musu hadi na musamman a kai musu, ita ta kai musu.
Chapter 77 · 0% Book details