Sashe 86
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400 +2347035133148
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB244
Ni dai na koma gida, sannan sauran ranakun ban je aiki ba. Duk da ina gudun Ya Amaan. Amma kuma akwai gaskiyar da na kasa yarda na tsaya na ji, sai da nayi kwana uku a gida, sai naji na takura kamar an daure ni. Amirah da Ya Amaan ya sakata makaranta, ana zuwa ɗaukarta kuma a dawo da ita. Tana dawowa na shirya bayan la'asar muka tafi yawo, haka yasa muka dawo wurin Magariba, na samu yana tsaye shida dan uwanshi. Shima naga kamar bai da yawan sakewa ba kamar Ya Amaan ba.
"Ba!" Amirah ta kira sunanshi. Mika mata hannu yayi ta isa wurin shi. "Ba me yasa baka zo ba? Yau ma jini ya fito a bakinka ne?" Cikin shashantar da zancen ya ce mata "ga sweet ɗinki."
"Fadima ya zaman gida?" Sai kunya ta kama ni na gaishe su, "yawwa naga kamar ba zai miki magana ba, ko zaki bani laptop da tap din?"
"Ok bari na kawo." Amma kuma wallahi ban ji dadin haka ba, amma.kuma ba Yadda na iya tunda na kamfani ne. Haka na shiga na kawo musu, ina kallo ya shiga motar ya fito da manyan kwalaye ya mika mata, ni kuma ya mika min wani kwalin. "Na rigada nayi niyya, don haka ga wannan Hp ne."
"Hmmm!" Nace xan mishi musu, zuba min idanu yayi sai ya cika min ido, haka na amsa ina godiya. Ina gani ya tafi ni kuma muka wuce ciki. Ban san me yasa yake yi min hidima har haka ba, sannan Ni dai na kasa sakin jiki da shi. Domin lamarin abin da na gani dole ya bani tsoro, sannan kuma da hujja ta na kare kaina da mu'amala da shi.
Ranar Lahadi ina zaune sai gashi nan, ya zo yana ta haki. Bayan na bude mishi kofar ya shiga kallon juna muka yi, fuskata a daure, zama yayi ya ce min. "You hate me?" Zuba mishi idanu nayi kafin na ce mishi. "Ni."
"Zahra kin tsane ni!"
"Ni ba haka nake nufi ba, alakata da kai wani sai ya dauka nima haka nake don Allah ka tafi ka daina shiga rayuwarmu."
"Tun ranar da na ganki a marad'i kina magana da yaron nan, da yadda kika tsaya domin kare kanki. Naji a jikina na samu kanwa. Zahrah"
"Dama kace ka sanni shi yasa kake bibiyata."
"Ba iya ke ba, hatta inda kike zaune na sani na san baki da kowa a marad'i da nan Nijar. Amma ba ina nufin na wulakantaki ba ne. Kawai naji a raina akwai wata nasaba da take haɗe a tsakaninmu."
Zama yayi ya fara magana a hankali, yana yi yana rike hancinsa. Ni da nake tsaye sai gani a zaune, ina sheshekar kuka. "Majid yafi mu wahala, tun yana Yaro rayuwarshi ta lalace, sannan yana nan domin shine Chairman na kamfaninmu. Wannan kaɗan daga cikin labarinmu kenan, ban sani ba ko zaki yarda dani amma ki sani na gaya miki gaskiya, don na lura babu me gaya miki gaskiya a kaina, kowa abin da yayi mishi yake gaya miki."
Hawayen da suke zubowa kamar famfo yasa ni kasa magana, "Yanzu daga ina kake?" Ajiyar zuciya ya sauke ba a san na fito ba, shine wasu suka biyo ni." Kura mishi idanu nayi, "Me yasa kake wasa da rayuwarka?"
"Saboda na goge videon da kika gani ne, eh na aikata abin da kika gani, amma wallahi dare daya na tsinci kaina da son bin maza, tun daga ranar na zama haka. Amma tunda aka min aikin na daina tunda dama ba dabi'ata ba ce. Ki yarda dani."
"Yanzu ka kira Aryan yazo ya dauke ka."
"A'a xan koma da kaina."
"Allah ba zaka bar gidan nan ba, sai da wani naka."
Haka muka shiga rigima, dakyar ya kira Chairman. Ko minti biyar ba ayi ba ya ce maza ya fito yana jiranshi. Bayan tafiyarshi da dare muna barci aka yi ta buga min kofa, tashi nayi ban kunna wuta ba. Na nufi bakin kofar na ce. "Waye?"
"Ki bude kofar."
"A'a waye dai."
"Dazun Amaan Mamman Ba'are yazo, kuma nasan da abin da ya gaya miki."
"Ni?"
"Ki bude ko mu fasa kanki da bindiga." Wani irin rudewa cikina yayi, na juya dakina da gudu, na rufe kofar. Ihun su da buge buge yasa na kara kame Amira hawaye na zuba min. Can naji wani irin kaara daga nan ban kuma jin kome ba, sai na ihun mutane, kai naga tashin hankali a rayuwata. Sai gashi duk abinda suka faru suna yawo a cikin idanuna kuka na saka ina kallon ikon Allah.
Har wurin asuba kafin na daina jin ihu da kakari. Washegari tun asuba yan sanda suka buga min kofa, ga bindigarsu, alamarsu uku ne, ga yadda aka jasu a wurin bayan an ji musu ciwo. "Ko kin san me ya faru?" Girgixa kai nayi, don ina matuƙar tsoro.
"Baki ce kome ba." Kuka na saka musu, ina jin kamar zuciyata zata buga. "Ban san kome ba."
"Ku kyaleta."
Aka fada musu, daga bayansu. Shiga dakin nayi na had'a kayanmu zan bar garin nan, ban ga dalilin zamana a zo a kashe mu a banza ba, haka na hada kayanmu na fito. "Zahra ina zaki?"
"Marad'i mana, zan je a sauya min wani wurin."
"Kina tsammanin zasu daina bibiyarki ne? Meye Amaan ya gaya miki?" Kallonshi nayi, dogo ne, kamar wani Superman. Yanayinshi kamar Lee dong wook, ga tsawo ga jiki, irin na zaratan sojoji.
Haɗiye yawu nayi tare da yin baya, ana cewa ina da tsawo wallahi ina ganin shi sai naga ashe ni yar tsako ce, domin ya ninka ni tsawo, a tsakanin hannunshi nake tsaye. Daure fuska yayi yana faɗin. "Magana nake kina kallona."
"Ni dai zan tafi!" Na fada kasa -kasa. "Allah ya tsare." Ya fada yana barin falon. Kamar an wurgo shi ya shigo falon, ganin ina jan kwatinmu ya rike "Zahra."
"Me yasa ka jefa rayuwata a hatsari?"
"Kiyi hakuri ban san zasu biyo ni har wurin ki ba."
"Shine ka saka kowa yake tambayata, meye ka gaya min?"
Idanunshi ne ya kad'a jajjur. "Kiyi hakuri, amma kin ga mutanen ne?" Girgixa kai nayi ina shashekar kuka, "tow ina suke ga kayansu nan, amma babu alamarsu."
"Ban gane ba?"
"Eh kowa a cikin apartment din nan, sun tabbatar da zuwan su wurinki. Amma kuma ance babu su, an ji muryoyin su sai dai babu su babu labarinsu."
Zubewa nayi a kasa, na fasa ihu domin haka shine ya dace dani.
Tun daga ranar aka saka tsaro a apartment din, tare da sanin fitana da dawowa ta.
•
"Hajiya kice ya rabu da yar mutane, domin kuwa zai jefa rayuwarta a cikin hatsari ko Hamma." Inji Aryan, kura mishi idanu Hajiya tayi yadda yayi shiru, alamar akwai abinda yake damunshi.
"Amaan!"
"Na'am Hajiya."
"Kana son yarinyar ne?" Girgza mata kai yayi, "Tow ka kyale musu yar mutane, kada ka cilla ta cikin wahala."
"Hajiya ni taimakonta nake son yi, sannan ni." A zuciye Majid ya bar musu falon, "Dawo nan Alhaji " kamar ba zai dawo ba, ya dawo ya zauna yana me saurarenta. "Tun wancan satin da ta fidda rahoton nan, na ce ya dakatar da ita, domin shi kanshi jagwal din yake ciki bai fita ba, zai saka yar mutane." Ya faɗa da fushi, don yasan dayawan makiyansu, suna board ne shi yasa yake ganin gara ya dakatar da ita.
Shi yasa ya goge rubutun da tayi, ya kuma bada hakuri. Sannan ya san a bangaren abincin kamfanin sun ji babu dad'i. Baya so a fahimci cewa zai shiga rigimar da bata da farko ɓalle karshe, hidimar kamfanin ya barwa kanshi ne. Sannan tun fil azal abin da tayi, shima yana tsarinshi, amma fito na fito da partner na kamfanin kamar yaƙin duniya na uku ne. Shi yasa ya zuba idanu yana aikinshi ba tare da ya tab'a su ba.
Haka suka yiwa Amaan caa, da fada wanda shi yasan cewa a wannan ɓangaren Zahra ce zata iya futar da abinda yake boyewa, koda yake ai bai yi mamaki ba.
Tashi yayi ya nufi dakinshi, ya shiga ban daki ya cire kayanshi. Zama yayi akan wata ƙaramar po, a hankali yake nishi tare da rike cikinshi. Tattaunawar da suka yi da Zahra ne ya dawo mishi.
_Eh ni dan luwadi ne, amma a da can nayi ba yanzu ba. Zahra ina son na gaya miki gaskiya mahaifiyarmu ta sha wahala da mahaifinmu, bayan nan kuma na fada wannan harkar a lokacin da na tsani dan uwana Majid. Zahra a yanzu akwai wasu da suke min barazanar zasu kashe ni a cikin kamfaninmu suke. Don Allah ko da kin ji labarin mutuwata ki gayawa Majid waɗanda suke da hannu a cikin mutuwa. Sannan rahoton da kika fitar, Majid ya ce kada ki kara shigar da kanki cikin lamarin kamfanin kiyi abin da ya kawo ki. Zahra ga wannan ki bawa Majid ko Aryan. Ki tabbatar ya shiga hannunsu_