Sashe 22
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba alfahari ba, haduwa da mutanen kwarai a jinina yake, duk inda na shiga sai na hadu da mutanen arziki, haka muka fito baki ɗaya, a lokacin da zamu bar Asibitin Dr Moses yaga Yakumbo ya dubata da kyau, sannan ya bamu magani akan muna bata idan ya kare muzo da ita taga likita. Gyada mishi kai nayi, muka tafi inda Nenne take, dake zamu bar Munaisah a wurin. Rike hannunta nayi. "Don Allah ki kula kin ji." Gyada min kai tayi, ban san wani irin zuciya nake da shi ba, ni fa bana iya rike ka idan kayi min, ina ji a raina babu amfanin rike mutum araina domin haka ba zai amfane ni da kome ba, sai ciwon rai.
Ni kuma bana son hassada da kyashi ya shiga, zuciyata saboda kai.
Haka muka isa camp din, cikin wani irin yanayi, muna isa Office din shugaban da yake kula da camp din aka kai mu, aka saka sunanmu, da inda muka fito da dalilin fitowarmu. Ana gamawa muka fito daga office din, Mutanen da suka kawo mu, suka raka mu har wani tanti, shiga muka yi baki dayanmu. Ba laifi cikin a rufe yake kasar kuma an lailaye shi da leda, alamar waɗanda suka zauna a cikin tantin suna da tsafta. Zubewa muka yi, daya matar ta ce min. "Fillo zamu je ki fara dauko muku kayan shimfidarku." Gyada kai nayi, muka fita da ita,haka nayi ta jido kayanmu. Har da kayan Abincin. Cikin sakin fuska matar ta ce min. "Akwai kayan abinci ku nawa ne?" "Mu bakwai ne." Na fada a sanyayye. "To shi kenan kai kayan ki dawo."
"Amma me yasa za a bamu danyen abinci?" Murmushi tayi tace min. "Danyen abinci shine zamu iya baku, idan muka ce dafaffe ne, a wurin bayarwa aka fara dambe sai an zubda abinciin baki daya."
"Subhanalillahi!" Na fada ina ɗaukar katifa da ta daura min, har tantin mu ga nisa. Ina kaiwa na kuma juyowa zan koma muka hadu da wata yarinya. Itama budurwa ce. "Barka mai kyau!"
Murmushi nayi mata sannan na ce mata. "Ai kema mai kyau ce." Juya idanu tayi, "Hmm!" Ai ban tsaya bin nata ba, na wuce abina domin ina da abin yi. Tass na kwaso kayan har da kayan abinci, ina tsaye ina haki Zuzu ta ce min. "Yanzu ya zamu yi idan aka fara ruwan sama?" Juyawa nayi na kalleta. "Kamar ya?" "Wurin girki. "Ok na fahimta. Kamar an wurgo ta,ta shigo cikin ba sallama. "Batun girki kuke? Akwai inda ake sayar da itaccen da gawayi, har gas akwai me sayarwa." Ta fada tana rangwad'i da yauki. Da fulatanci Zuzu ta ce min "Zahra a ina kuka kwaso mana Zee yauki?"
"Ande!" Ita kuwa sai yauki take, wato ko Allah ya shirya zuzu. "Dukkanku masu kyau ne, wow." "Yanzu ya zamu yi kenan mu sayi gawayi kawai domin zai fi gas din nan, ko?" Na tambayi Zuzu. "Tow ya zamu yi da kudin nan na naija ne da" "ai duk suna amsa, kasancewar garin nan yana kusa da boda, zaku iya sayayyarku da shima."
"Mun gode amma meye sunanki?" ."Aina'u suna na!" Gyada kai mukayi, muna kallonta kafin Zuzu ta ce . "Kina da kyau!" Ai kuwa kamar an kunna radiyo, ta fara zuba. "Zahra'u dauke kawarki ta rakaki, ku nimo mana abinda zamu ci bamu isa da surutun ta ba." Inji Addah ta faɗa da fulatanci, haka na jata muka tafi har inda zamu sayi kome,, dake a cikin kayan da aka bamu har da kayan miyar gwangwani kifin gwangwani, da sauran tarkacen irinsu garin kunu, shinkafar ci da ta tuwo garin madara, burabisko, mangyad'a da man ja, magi ma ban tab'a ganin irinshi ba, sai a wurinsu, haka muka siya har da tukunyar hannu da kwanuka. Anan wurin take cewa. "idan ba zaku yi amfani da kayanku ba, ku bamu zamu baku kuɗi." Murmushi nayi mata nace mata. "Bamu koshin da zamu sayar da abinci ba, ki jira idan mun koshi zamu kawo mu sayar."
........
08130269641
*Mai_Dambu*
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*011*
Bige hannuna Aina'u tayi cikin rangwad'a ta ce min. "Ba a fadar haka, Uwar mugu bata lamuntar cika baki" sannan ta kalli matar cikin fara'a ta ce mata. "Uwar mugu muna neman yafiyarki domin bakuwa ce daga Nijeriya bata san kome akan gurin nan ba." Murmushi matar tayi tana kallona cikin wani irin kallo kafin ta juya ga Aina'u tana murmushi ta ce mata. "Ya sunanta?" Cikin kad'adi irin na wanda ya saba ta ce mata. "Zahra!" Rike baki Uwar mugu tayi tana cewa. "Mai Babbar suna kenan, kun ga uwata takaina, maza ku je babu komai ai Uwata ce bata laifi."
Aina'u kamar ta zube kasa, tayi ta godiya har da cewa. "In sha Allah zaki same ta mai biyayya." Idanunta kyam a kaina, ni kuwa ko dar ban ji ba, domin matar asalima kawai bata kwanta min a rai ba, haka muka bar wurin ko inda take ban kuma kalla ba, babbar mace ce amma yanayinta zaka kalla kasan bata da mutunci. "Amma matar nan bata da mutunci ko?" Da sauri Aina'u ta rufe min baki, ta juya tana kara gaida matar, wacce da na juya na kalleta ni take kallo."Uwar mugu bata da matsala, kuma bata da abokin tarayya a cikin sansanin gudun hijirar nan, mace ce da tasan kan duniya idan taso zata iya janyowa a Kore ki, ko kuma a kwace muku kayan abinci. Tana da Yaro ɗaya baya cikin sansanin nan, yana tafiya farauta ne, sai dare ya ke shigowa. Matar tana da matuƙar hatsari idan ka nuna mata kai ma dan duniya ne, idan kuma ka bita a hankali zata iya sakawa kowa ya kaunace ka, idan ka nuna mata baka da mutunci zata iya sakawa a tsane ka. Uwar mugu mace ce da take hada mutum da mutane masu arziki na wajen nan. Nima ba karamin arziki na samu a ta sanadinta ba."
Ware idanu nayi na kalli Aina'u, "yanzu Aina'u harkokin bin maza ta dauraki a kai?" Murmushi tayi irin bai dame ta ba, ta ce min. "Kai ji wata magana sai kace wani saɓo nayi, ai wannan rayuwar idan baka iya d'aga kafa ba, ba zaka huta ba, abincin da aka baku kin zata zai kai wata ne? Bari ki ji, daga zarar kun kai sati biyu nan ne idanku zai raina fata." Baki daya naji hankalina ya tashi, bamu rabu da bukar ba an haifi Habu, wato mun yi gudun gara mun tadda zago. Ban kuma magana ba, haka dai na barta tayi ta surutu domin ban san me take fada ba, haka muka isa, na ajiye kayan na shiga daki na samu wata mata suna ta hira. "Laaa Mamata itama tazo kenan." Ta shigo, "Tumba!" Ta kira sunanta. "Na'am Aina'u." Zama tayi a jikinta tana murmushi. "Kin samu kawa daga zuwa kenan?" Mamar ta tambayeta. Juya idanu tayi tana faɗin. "Eh Tumba." "Dama Yarki ce?" Gyara zama tayi tana murmushi ta ce mata. "Y'ata ce, na tafi Saudiya na barta ina dawowa rikicin boko haram ya koro mu nan Kamaru." Shiru tayi kanta na kasa kafin ta ce. "Sai da muka yi kwana talatin a hannun Yan boko haram, suna gana mana azaba, ga cin zarafi da fyade." Ta rungume Aina'u, itama yarinyar k'amk'ame Mamarta tayi, alamar har yau idan suka tuno abin yana musu zafi da ciwo. "Sun ci zarafinmu." Mikewa nayi na fita waje, kallon sama nayi domin bana son hawayen da ya taru a idanuwa na su zubo. "ku shiga da kayan ciki domin za a sace." D'ago kai nayi muka yi ido biyu da shi. Security ne domin naga sanye yaƙe da Uniform. "Tow!" Nace mishi. Na shiga da kayan cikin tantin mu, "Aina'u a ina zan samo ruwa?" Mikewa zumbur tayi tana faɗin. "Muje!" Ta dauki daya daga cikin langar da ta sani na saya. Muka fito ban ga mutumin ba, haka muka ratsa ta dakinsu, da mutane a ciki. Guga ta dauka, dakin ban da warin sigari baka jin kome. Kafin ta dauki gugar daya daga cikin mazan dakin ya fisgota. Tana dariya ta ce mishi. "Meye haka, Faruq?" Da sauri nayi baya, na tsaya a waje, ina jin mazan dakin suna ta dariya, har da ita ganin xata bata min lokaci na juya na bar wurin, haka kawai naji jikina yana bani kamar ana bina, juyawa nayi naga mutumin dazun ne. Mutanen da na gani a dakin suma irin kayan jikinsu ɗaya, tsayawa nayi naga ko zai wuce, abin mamaki sai naga ya tsaya. A hankali wani sabon tsoro ya kamani na juya . "Me kake so?" ."raka ki kawai zan yi, don naga kina da nutsuwa. " Ya tawo ya amshi bokitin hannuna, yayi gaba ina bayanshi, har bakin inda zamu d'ibi ruwan.