← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 138

Sashe 110

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Lokacin da aka sallame su, ma tana ganinta babban burinta shine yarta, kuma ta ganta amma tana son lallai ta amshi abinta ta koma U.S don ba zata iya rayuwa a nan Afrika ba, ta saba da rayuwar can har ta gina kanta da Yarta. Don haka ta je makarantar daidai anyi break ta samu damar fitar da yarinyar daga makarantar, kuma dalilin yadda aka yi ta dauke ta, don kwallonsu Amirah ya fito waje ne, ita kuma tazo dauka, shine ta ce mata."zo gashi a mota ta!" Da gudu yarinyar ta shiga, tana shiga ita kuma ta rufe motar ta fisgeta da gudu. "Ina za muje?" "Zan kai ki wurin Maminki ne?" Ta mika mata Bunny Bunny, wanda ta shaka mata iskar da ya sumar da ita. Daga hakan ta wuce da ita wani gidan da Nawwas ya ajiye mata, tun da ta kai yarinyar ta farka bata da wani aiki sai kuka bata cin abinci a tsawon kwanaki biyu nan, yarinyar bata barci duk yadda Zuzu taso ta daina damuwa, amma taki don haka ta rasa yadda zata yi da ita. Kawai ta dura mata maganin mura, ta sayo mata kaya kamar hauka, amma haka Yarinyar nan taki kulawa ita Maminta kawai, ganin ga Zahra a can asibiti haka yasa ta hakura ta kai mata ita asibitin ta ajiye ta, sannan ta kai sauran kayan gidan Zahra.
..............
A lokacin da aka sallame ni muka dawo gida, a daren na tura takardar barina aiki, da sassafe sai ga Majid. Yadda yake buga kofar gidan yasa ni fitowa waje, na bude kofar kamar zai fada kaina ya shigo.
"Me yasa?"
"Aure zan yi kuma na ajiye aikin zan bar kasar, zan koma ƙasata."
Na faɗa mishi cikin magagin barci da na farka,"Zahrah!" Naji Muryar Hajiya. "Na'am!" Na ce ina kallonta, "zauna mu yi magana." Zama nayi a hankali ina kallonta.
"Abdul ya ce min kin ajiye aiki. Wani abu aka miki barazana ne?"
"A'a kawai zan tafi garinmu ne, sannan zan yi aure a algeria ne."
"Aure!" Ta tambaye ni a mamakance, wato tayi mamaki. "Kina nufin kin samu mijin aure ne?" Murmushi nayi nace mata, "Hajiya mace bata rasa mijin aure, sai dai idan lokacinta bai yi ba."
"Majid din fa?"
"Ban gane ba?"
"Yana sonki?"
"Hajiya kin manta yadda kika bukata ne?"
"Don Allah ki...."
"A'a Chairwoman, ba ayiwa mace dole kuma taya zata auri mutumin da bata sonshi. " Inji Yazid. Ya faɗa yana shigowa daga bakin kofar. Cin kwalarshi Majid yayi. "Kai meye haka?" Inji Yazid yana cire hannun Majid a wuyarshi, "Ni namiji ne sai da na share fagen fama kafin na samu Zahrah don haka ba zan yi faɗa da kai ba, a gaban matata."
Sake wuyar Yazid yayi yana me barin gidan, "Idan kudi kike so."
"Hajiya an wuce wurin, kiyi hakuri."na faɗa ina me juyawa zuwa dakina, sai yanzu nake iya tuna abin da ta gaya min, ban da ina ganin girmanta da yau na gaya mata magana, amma ina tana da wani irin girma a idanuna wanda ba zan iya mata fitsara ba, na kira Iyayen Barakatu na gaya musu zan tafi garin mu suka ce ai su Barakatu tawa ce duk inda naso nayi da ita don haka na gayawa Yazid shiga da fita yayi ina karyawa sai gashi da wasu takardun.
"Marwa zan kai ki da kaina." Haka muka shirya cikin shigar alfarma muka bar gidan sannan muka wuce kasuwa muka yi sayayya. Kafin mukayi ta yawo sai dare muka wuce airport.
Karfe bakwai muka bar Nijar, sai da na sauke ajiyar zuciya. Domin nasan nayi nisa da Zuzu, sai dai ina ji a raina kamar na gwada son kai. Kallon shi nayi ina faɗin. "Amma banso kai na ba ko? Yarinyar nan ban rabata da uwarta ba ko?" Jan hancina yayi yana faɗin. "Duk ranar da na mallake ki, a ranar zan gaya miki me kika yi amma yanzu ban da amsar baki." Juyar da kaina nayi, "Yawwa nayi magana da Babangida, ya ce idan naje Marwa zai zo shima sati me zuwa sai na tura magabatana, su zo nima min." Kashe min idanu yayi. Tunda maganar aure ya shigo na fahimci Yazid kwarkwar ne. Kasa yayi da kanshi ya rad'a min magana a kunnne rufe bakina nayi da kunnen duka.
Haka yayi ta zuba min rashin kunya, kamar nayi kuka,.har muka isa da asuban fari. A airport din muka karasa kwana ya ce min. "Yanzu don Allah idan da kin zama matata ba sai dai ki lullube ni da bargon kauna ba."
"Kai ka sani wallahi" na fada ina sauya wurin zama, zama yayi a kusa dani yana dariya. "Allah bargon kaunarki zaki lullube ni." "Yazid ka fita idanuna dama haka kake?"
" Eh wallahi har na wuce haka, baki san wani abu ba, nifa..." Wucewa wurin sallah nayi na bar shi awurin yana min dariya, haka kawai yake jin nishadi a ranshi.
Chapter 110 · 0% Book details