← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 138

Sashe 105

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

*
"Bawan Allah ina zahra'u take?" Zama yayi ya kura musu idanu, sanin cewa babu wasa a fuskar shi yasa Addah shan jinin jikinta. "Tana lafiya! Idan ta ganku zaku koma garin ku, kafin na san yadda zaku sake haduwa."
"Haka yafi a yadda take cikin wannan yanayin, kada ka saka lallai mu zauna domin gawarta za a iya samu."
"Ke dai munafuka ce." Inji Addah take gaywa Ummi. "Ke kuma babban Shaidaniya." Ganin zasu fara faɗa, ya tashi ya bar musu gidan, lokacin da ya dawo asibiti ya samu Yazid yayi daidai yana aiki da tap ɗin shi. "Waye ya baka iznin shigowa asibitin nan?" Ko kallonshi bai yi ba ya ce mishi. "Matata Sultanah Zeehrah."
"Karya kake!" Tabe baki yayi yana faɗin. "Ni tun fil azal ban iya hayaniya ba, domin ba a koya min ba, don haka ka daina min ihu." Ya fada yana cigaba da abinda yake yi, duk yadda Majid yaso suyi rigima abin ya ci tura, shi Yazid yasan da haka amma a tsarin shi ba zai tab'a faɗa da namiji akan mace ba, idan tasu ta haɗa su dai zasu yi amma ban da akan mace. Fadar kenan kyautatawa macen idan ka isa kayi fiye da abin da nayi, wato gasa.
Zama yayi sai lokacin sallah duk suka fita, basu dawo ba sai bayan isha, Yazid ne ya fara shigowa ya samu na bude idanu, tura kofar da yayi na juya ina kallon shi. Mika mishi hannu nayi, ya iso wurin da nake. Yana rike da hannun. "Wanda ya mutu yana dawowa ne?" "A'a Zeehrah!" "Me yasa ka min karyar su Addah sun mutu?" Hada hannuna da kaina yayi ya rungume ni.
"Kiyi hakuri!"
Lumshe idanun nayi ina faɗin. "Me yasa baka gaya min suna raye ba?" "Saboda ko na gaya miki suna raye a kullum matar nan cusa miki bakinciki zata yi."
"Sai meye?"
"Sai me? Sai na gaya miki gaskiya bana kaunar ganin wani abu ya same ki, bayan nan babu."
"Kodan ka saye ni ne?" Na fada ina cire kaina daga kirjinshi. "Duk yadda kika ce Zeehrah daya ne." Kuka na saka mishi, ya kuma rungume ni, yana shafa bayana. Tun ina yi da karfi har nayi shiru.
Yana tsaye a bakin kofar yana kallon yadda take kuka, kamar wanda aka zabura, ji yayi kamar wani abu ya motsa a tsakanin cinyarshi, wanda ya haɗa da marar shi da yayi wani irin kullewa, da sauri ya ajiye abin hannun shi ya bar kofar, a daddafe ya koma gida, yana shiga cikin gidan bai tsaya ko ina ba, sai dakin shi ban daki ya wuce yayi ta kwararawa kanshi ruwa. Yana sauke Ajiyar zuciya. Kafin yaji dama-dama. Daki ya dawo ya kwanta yana nishi.
A hankali wayar shi ya dauka ya kira likitanshi. "Dr" "Na'am Mr Mamman lafiya?"
"Dr wani abu naji ya harba amma ban san meye ba." "Thank God, wannan al'amarin yayi kyau, ya kake ji?" Nan ya gaya mishi abin da ya faru. Shiru likitan yayi kafin ya ce mishi. "Ko ita ce yarinyar da kuka hadu shekaru biyar baya?"
"Eh ita ce." Murmusa mishi yayi sannan ya ce mishi. "Kana bukatar yarinyar a rayuwarka, idan baka manta ba a lokacin kayi yunkurin mata fyade amma ka kasa saboda wancan trauma din, yanzu kuma ya motsa ne saboda ka ganta da wani ka isa gare ta, abubuwa dayawa zasu sauya."
Chapter 105 · 0% Book details