Sashe 117
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kafin wani lokaci yan'uwa da abokan arziki sun taru, Ni dai tunda ya farka na koma gida, nayi abinci ashe bayan na dawo yake tambayarsu ina nake, aka ce ina gida ban sani ba sai da Mama ta kira ni wai nayi maza na tawo Majid yana nima na. Haka na gama girkin na tafi asibitin don na bar Zuzu a can, ina shiga harabar asibitin muka hadu da Hajiya. "Sannunku da zuwa." Cikin farinciki da sakewa ta riko basket din Hannuna tana faɗin. "Yawwa sannu Binta. Kawai sai aka bar ni da yake sunan yayi min banbarakwai. "Ya Hanya!" "Alhamdulilahi, sannunku da kokari sannu Allah ya shiga lamarinku. Ubangiji ya duba al'amarin nan ya dawwamar da shi, albarkacin nabiyun rahamati!"
"Amin!" Muka shiga cikin asibitin tare, ina shiga Zuzu ta rungume ni cikin farinciki da jin dadi. "Ina jin wani irin farinciki ne!" Wucewa nayi na shiga dakin, na samu ana ta hira. Kafe ni yayi da idanunshi, lokaci guda na takura kamar yadda yake bina da tsumammun Idanunshi masu dan karen kaifi da tasiri.
"Ya jikin?" Na fada ina kumbura baki, Kin amsa min yayi,Malamijo ya ce min. "Da sauki Amarya, ya kike ya kika ji da haukar kanwarki?" Sake fuska nayi zuciyata daya, na ce mishi. "Ai haukarta da dalili take, kuma shine dalilin haukar nata. Idan har ana son tayi hankali a bata shi sai a zauna lafiya tunda kowa yasan tana son shi, babu amfanin tsayawa bata lokaci,idan ya warke sai a daura musu aure." Kallona suke baki daya, babu wanda ya ce min cikanki, murmushi Malamijo yayi ya ce min.
"Idan Allah bai ƙaddara ita matar shi ba ce fa?" "Amma kullum cikin addu'a muke,Allah ya kawo mana ƙaddarar da zamu iya amsar ta. Idan aka saka musu albarka auren zai zauna."
"An daura mishi aure da matar da yake so, ruwanta ne tayi biyayya ko kuma tayi akasin haka."
"Ba sai ya aure ta a na biyu ba,don Allah Malam tana cikin wani hali shi kawai take so." Shiru dakin ya dauka Goggo Sume ta riko hannuna ta kai ni har gaban gadon Majid. "Zauna Fadime!" Zama nayi domin na kasa magana. "Idan kika duba lamarin me sauki ne, amma ki nutsu da kyau zan gaya miki wani labarin da bai zama dole ya miki kyau ba."
"Hmm!" Na ce ina kallon Mama da take antaya min harara. "Jiya da dare Aminatu ta nime a daura aurenki da Majid..." Iya abinda na ji kenan sauran ban san yadda aka yi ba, ashe tuni na suma musu a wurin shi da kanshi ya sauka yana jinyar shi ya gyara min kwanciya tare zama ya zuba min idanu. Har likita da nurse suka shigo aka fara duba lafiyata. Maganar ne kamar saukar aradu wallahi. Sai da na kwana uku a yadda Zuzu ta gaya min wai ai basu zata zan farka ba, lokacin da na farka kuwa abu daya na faɗa, wanda ya dagula lissafin kowa har da shi Majid ɗin. "wallahi bana sonshi ban tab'a son shi ba. Don Allah ku raba ni da shi."
Kura min idanu yayi yana kallona kafin ya ce min. "Kiyi hakuri kin ji."
"Ba zan yi hakuri ba, kai ne bana so kai ne bana kauna, bana kaunar zama da kai" a yadda nake kuka da ihu yasa shi daukar alluran barci ya dankara min. "Allah zai saka min. Ka kyale ni nace ka kyale ni, bana son haka." A hankali barci yayi gaba da ni.
Allah ya takaita duk borin babu kowa a dakin, haka na kwana uku a cikin wannan yanayin ranar ta hudu na farka babu bori da rikici. Bai kula ni ba ya wuce ban daki yayi abinda zai yi ya fito sanye da wani wando. Kallon dakin nayi naga kamar an canza mana dakinmu. Dauke kai nayi ina kokarin sauka a gadon ya karaso ya tare ni na fada a jikinshi, ni a tunanina karfi ne da ni, sai gani na kasa ture shi, ina huci ina tutture shi amma ina ya kasa motsawa kuka na saka mishi, a hankali ya zuba min idanu." Tow ya isa haka, wuce toilet kiyi abin da zaki yi " haka na mike ya matsa min, ina saka kafafuwa ta a kasa, na yanki jiki zan fadi ya kuma tare ni. "You see!" Ture hannun shi nayi cikin tsiwar da ban san ina da ita ba."kyale ni nace bana sonka!" Murmushi yayi ya bani hanya da rarrafe na nufi hanyar ban dakin, ganin yadda nake tafiya kaɗan na huta, sai ji nayi anyi sama da ni. Ban dakin ya kai ni, nayi wanka na gyara jikina, sai lokacin na samu karfin jikina na fito ina jin wani irin karfi ba me yawa ba. Abin sallah ya ajiye min na fara sallah, sai da na sauke wanda ake bina kafin na shiga addu'a wanda rabin addu'a duk akan ya sake ni ne, Allah yasa ya sake ni ma.
**
Daren da Zaytoonah ta mare ni, a daren Mama ta gayawa Malam, a daren ta roke shi a daura auren. Majid da Zahra haka zai saka Zaytoonah ta huta da tashin hankalin lallai sai ta auri Majid. Suna gama waya Ya kira Babangida, ya gaya mishi domin shi kamar Uba yake a wurin Zahrar. Ai kuwa ya bashi hakuri ya ce kada ya gayawa Zahrah da Zulaihah Addah ce ta gamu da yan fashi a hanyarta na barin garin, suka mata dukan mutuwa don taki basu kudin al'amarin kamar wacce aka mata cune. Dukan da suka mata ne ya tab'a kugunta don kamar sun karya mata kugu, bayan sun kwace kudin.
Asalin ba wani wurin zata ba, an bata labarin wani boka ne, a can Benue shine xata ya raba Zahra da duk wani farincikin rayuwa ya dasa mata bakin ciki har ta mutu, ya saka mata bakinciki ta rasa kowa a duniyarta danginta kowa ya gujeta, Zuzu kuma ta zama under control dinta, sai yadda tayi da ita, tasan a yadda taken nan ba karamin cin kudin maza zasu yi ba. Haba sai gashi ba a je ko ina ba, Allah ya wargaza shirinta, ya hada ta da su da'u. Suka wulantata suka kwace kudin shine aka kawota asibiti akayi ta yayatata a gidan radiyo. Shine Babangida ya ji aka duba aka ga ita din ce, haka yasa shi jin tausayinta, yasan addah ba ƙaramar Shaidaniyar mace ba ce.
Dalilin da yasa bai nemi zuwa auren Zahra ba kenan, washe gari aka daura auren bayan sallar asuba, Malamijo ya sanar mishi ya ce ayi duk abinda ya dace kada a jira shi.
.... A asibitin da Addah take kuwa tunda ta farka ta ganta a gadon asibiti bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,domin wannan ba shine tsarinta ba, wannan baya cikin shirinta, sai gata a gadon asibitin, tana tunowa zata fashe da kuka, kamar ranta zai fita, sau biyu tana yunkurin tashi tana kasawa, shigowar Ummi ta kalleta tana faɗin. "Karshen sharri ya kare, babu kafafun zuwa kulla shi, Zahra ta zama matar Abdul Majid Mamman Ba'are, shugaban kamfanin Ba'are golden EMPIRES, saura ki mutu."
"Ummi, don ku nake kome!" Ta fada cikin matsanancin kuka, "fadi gaskiya Addah, keda iskancinki.har Saudiya kina tsammanin Allah zai barki da hakkin mu ne? Don haka bari na tuna miki, yadda kika lalata.mana alaka da Zahra yau da alamun Zahra ta zama bishiyar gamji, Allah ya wanke ta ya bata miji daidai da hakurinta, mu kuma kin saka ana mana kallon karuwai, Yarki daya tal zaki kashe ta tir da halinki Addah. Yanzu ma naji labarin SK Lamido wai zai tura danginsa su tambayo mishi auren Zulaihah idan naso sai na lalata auren amma.nasan idan nayi hakan a dadinki tunda karuwa kike son ta zama ba zan tab'a mata sanadin lalacewar rayuwarta ba, amma ke zan yi fatar ki dawamma a nan, kashi a kwance fitsari a kwance. Kuma babu me miki jinya sai ni kamar yadda kika kashe Innar Munaisah har yau babu labarin Munaisah haka zan zauna nayi ta gana miki azaba na dare daban na safe daban yadda zaki gane cewa Allah da girma yaƙe, kin cuci mutane." Haka tayi ta gaya mata magana tana cusa mata bakin ciki da takaici, haka yasa Addah fashewa da sabon kuka, dakyar Ummi ta bar dakin, kuma ta saka a ranta sai ta muzantawa Addah zata ji sauki a ranta.
•
Duk yadda nake bore mutumin nan yaki kula ni, domin har barazana nayi zan sha guba na mutu. "Idan kin mutu ai da aurena kika mutu, kuma muje gaban Allah nace a min hisabi dake!"
"Wallahi sha zanyi" na fada cikin kuka da takaici. "wace irin guba kike so ta ganye ko ta dabbobi wanda ake sakawa bera da jab'a xan nemo miki?"
"Wallahi ka daina tsokanata;"
"Tow! Na daina!"
Haka na cigaba da kukana, ina jin bakinciki kamar ya kar ni. Haka yayi ta manna min hauka ya ce min. "Za a sallame mu cikin satin nan, zaki Najeriya ayi wani buki ne ko zaki zauna a nan?" "Ni na gaya maka gaskiya bana sonka" kura min idanu yayi alamar maganar tana mishi zafi ......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB264