Sashe 124
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kullum ina kwance a dakin Hajiya, gashi a lokacin ya jarabtu da son lallai sai ya tab'a ni, haka zai fakaici idanun Hajiya ya sakawa dakin Key, sai yayi yadda yake so da ni yake kyale ni.
Da yamma abin ya ciyo shi, yazo ya samu Nana a dakin tayi bake-bake tana mitan. "Alhajin Allah taya zaka barta a dakin Sa'a matar da itama bata kula da kanta ba balle majinyaciyar da take dauke da karamin cikinka? Gaskiya ka mai da ta dakinka idan ta kama ma na dawo nan da zaman jinya xan yi."
"A'a Nana!" Ya faɗa yana kallona, nasan kalar mijin da Allah ya bani, shi yasa na mike a hankali nace mishi. "Muje kaci abinci!" Tausayina da kaunata na gani a idanunshi. Haka muka tafi har zuwa falon na dibi abinci muka haura sama, tun daga ranar jinyar kasa ya kare domin na ga yana takura don haka na bashi duk wats kulawar da ya dace, sannan na rungume mijina hannu bibbiyu.
Ana haka Mama tazo, naga hidima daga kakanni na da Mamanmu tsayayyar mace ce da bata son wasa, ita tayi ta gaya min yadda xan kula da shi, muna falon Hajiya kafafuna na kan cinyarshi yana matsa min, don bana iya zama sai kwanciya. Tunda muka dawo Zaytoonah bata taɓa tambaya ta ya jiki ba, haka zata wuce abinta tana harkar gabanta. Shigowa tayi ta samu yana matsa min kafa. Ta gaida kowa amma ko inda nake bata kalla ba, "Mama kina nan ne?" "Eh!" Babu wanda ya ce mata cikanki. Shigowa Nana tayi da katon kula. Ta bude min kamshin farfesun kan rago tashi nayi zan zauna ya rike ni.
"Sannu kin ji!" Haɗiye yawu nayi dadin abin duk wannan ciwon baya hanani cin abu, zuba min Mama tayi, ya tashi ya kawo min ruwa. Sai da na sha Nana ta ce.
"Hajiya Aminatu don Allah ku kawowa Zahrah da a bin cikinta maganin kambun baka da na idanu, da rubutun tsari kada a shammace mu a nakasa mana yaro kafin yazo duniya."
"Nana an kawo mata, tana sha kullum kuma nasan tana addu'a akan cikinta da azkar."
"Assalamu Alaikum!"
"Wa'alaikimun Salam," Amaan wanda ya kara zubewa bai da lafiya gayen nan haka muka yi ta hira sama sama, ina gama sha barci yayi gaba da ni, ya gyara min kwanciya, "Ka maida ta sama kawai." Daukata yayi bayan ya cire min drip din, muka wuce sama, sai da ya kwantar dani ya dawo ya dauki drip din ya wuce da shi sama.
Kwanciya yayi a bayana muka yi barci tare, kwanan Mama goma ta koma gida cikin farin ciki da jin dadi, haka abubuwan suka cigaba da tafiya. Idan ka ganni zaka dauka mutuwa zan yi tsabar laulayi. Wata na biyu da dawowa Zuzu da Munaisah suka zo, tun daga haduwar Munaisah da Zaytoonah, Munaisah ta ce mata. "Ke zo nan dan Ubanki!" "Kin Sanni?" "Zahra sa'arki ce? Zanci bu... Ubanki yar iska da kike ganin mutane kina dauke kai, me kika taka? Me kika sani na rayuwa shegiya har kin isa ki jera kafada da Zahrah, kika sake na bar garin nan baki zuwa kullum kina gaida Zahra sai na miki diban albarka." Yadda ta ga Munaisah bata da mutunci yasa bata mata fitsara ba, ke Munaisah har da cewa. "Shegiya don kinyi aure sai ki nuna mata rashin kunya."
Ashe bayan ta gama a gabana, ta kuma sakata a gaba tayi mata tass kuma tace wallahi wani abu ya samu cikin jikina sai ta daure ta, kada taga suna uba daya zata rufeta har igiya yayi saura. Tsoron haka yasa ta cire kudirinta na ganin Bayana. Kai jama'a. Satinsu daya na warware kamar bani ba, muka je marad'i bikin Zainab kanwar Baraka,. Dake da Majid muka je Munaisah tana nan ita da Zuzu, kawai Mahdi Abubakar Abzin ya ga Munaisah, tuni ya susucew, ita kuwa sai fada take yana faɗin me zan yi da shi, dube shi fa da uwar wuya a wurin. Mu kan me za mu yi banda dariya.
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB269
Da gaske ta dauki fushi ita Mahdi ya mata dogo, ita ta saba saurayinta na baya katon namiji ne, iskanci kala kala haka tayi ta mana har aka gama bikin. Muka dawo su Kuma suka wuce naija daga can.
Munafuka ashe ya bita sun hade kai, sai da ta kira ni muna waya take ce min." Kashe don Allah Babyn baby yana kirana." "Waye muka samu babyn baby?" Dariya ta saka min tana rokon na kashe kiran na kashe.
** A can Yola kuwa zuzu tana sauka Sk Lamido ya wuce da su gidanshi. Ashe gagarumin tashin hankali aka yi a family wanda ya zakulo wani alamarin da ba a san da shi ba, Maman Sk Lamido ashe ba ita ya haife shi ba, dan kishiya ne ta rike domin sai da rigimar auren ya fito Yaranta suka ce ai ta so kanta taya xata hana shi auren wacce yake so duk matanshi ita ta saka ya aura, karshe daga can garin Numan dangin mahaifiyarshi suka ji labari suka yi tsalle suka ce basu san da haka ba, ya ga matar da Allah ya haɗa halittarsu zata ce bata ji ba, ko don ba ita ta haife shi ba? Kuma ita tunaninta idan ya fara haihuwa bai zama dole ya kula da su ba, sai daga baya yake fitar da wahalar da ya sha a hannunta, abin yana tsaye a ranshi. Amma kamar an rufe mishi baki, dangin mahaifiyarshi suka dauki Zuzu da Yarta aka tafi garin Mamarshi aka sha biki, anan ya hadu da yayun shi da suke ciki daya, amma ba uba daya ba, anan ya fahimci Hajiya ta raba shi da kowa ne don kanta.
Bikin da aka yi dangin Uwa suka nuna mishi kara, aka yiwa Aamirah hidima kamar zasu maidata ciki. Ga wani cikin da Zuzu ta samu. Hajiya bata hakura ba sai da tazo har numam ta gaya musu wacece Zuzu suka ce sun yarda suna sonta sirkarsu. Dake itama Zuzun taga Rayuwa kama dangin shi tayi ta rike gam, kayanta da na shi da na Aamirah ta saka suka barwa dangin Mamanshi wasu kayansu sabi ne dal, wayyo Allah sai gashi an hada mata kwaryar tsaraba, kifi, dafaffen madara, man shanu, kayan miya kayan lambu. Da Hajiya uwar goyan shi tayi magana akan rayuwar Zuzu cewa suka yi..
"Ba kome, ai Aminatu ta tabbatar mana da Lamido shi ya fara ta'adin uwarta tunda gani ya kori ji."
Wannan abin ya kara rufe bakinta, amarya da ango da yarsu suka bar dangi cikin so da kauna, haka suka dawo Yola,aka bude sabon amarci kamar a cinye juna, wannan al'amarin yafi kome dad'i, kuma shima yadda ta rike danginshi haka ya dauko Aaddah ya ware mata part har da yan aikinta, ga wani cikin a gaba don ma laulayin me sauki ne kawai abu kad'an bata so. Haka suka yi ta rayuwarsu, ya kwashe su suka tafi Umara daga can suka tafi China aka.akayi sayayyar kayan haihuwa, sai da ta fara yi ma Zahrah sannan tayi nata, sai kayan kitchen da ta sayawa Munaisah da Ummi.
Aka kawo duk da Ummi har lokacin bata samu miji ba, amma kuma duk abinda ta saya har da ita. Shima mijin lokaci ne da sauran.
**
Duk da ban tab'a daukar ciki ba, sai yanzu a yanzu na fahimci dalilin da yasa Zuzu ta ce na bata yarta, domin wata soyayyar sai uwa da d'anta. Tunda Munaisah ta ci Uban Zaytoonah na samu sauki Aunty sama Aunty kasa. Ga uwa uba duk wani aiki sai dai na samu tayi min. Kallona tayi tare da yanka min kankana ina sha. Ta ce min. "Ashe duk abinda ya faru baki tab'a gayawa kowa irin wahalar da kika sha da su Munaisah ba." Ina tauna na ciro kwallon na ajiye ina faɗin. "Ba kowane lokaci ake tanka rikicin dangi ba, kayi iya yinka kada ka sake zumunci ya nime hakkin shi a wurinka a ranar gobe kiyama, a gaban Allah."
"Me yasa kike da hakuri akan naki?" Dariya nayi ina kallon yadda take share hawaye. "Saboda bayan su bani da wasu dangin, su din sune dole na, kuma kwarin gwiwata. Idan na rasa tallafi daga gare su ni ba kome ba ce."
"Aunty Zahra kina rike da ni ko?" Ta fada tana kuka. "A'a bana rike dake, amma nasan har abada ba zan bar miki Majid ba, domin ni aka yi shi."
"Ni kuwa kin ga zan karo mata uku russss kwailaye kuwa!" Wurga mishi filo nayi ina faɗin. "kwailaye for my foot shoes." Dariya yayi yana faɗin. "Yarinya kwailaye masu kananun!" Kura mishi idanu nayi, ina nuna mishi Zaytoonah. Zuwa bayanta yayi ya toshe mata kunne. Dafe goshi nayi na ce mishi. "Wallahi Bawan Allah yana jinka kana fadar batsa shima zai ɗauka."
"Ayi haka na fasa, ke, tafi wurin Hajiya mijin yarta ya dawo atow maza mai tumbi duba lamarin mijinki" ya fada yana bude kofa. "Maza sai da safe kada a kuma zuwa sai na fita."
Juyawa yayi ya ganni a bayanshi. "Me yasa xaka tab'a ta? Kasan yadda na.ji kuwa?" Na fashe da kuka, ina dukan kirjinshi. "Ji nayi kamar xan mutu. "Yarinyar nan ko mutuwa kika yi wallahi ba xan tab'a aurenta ba, ni idan na mutu zan so ki rayu da kowa amma ban da jinina wato kannena, don Allah ina tayaki kishin kanmu a kanwa na dauke ta."
Tunda ya fahimci kishina yake takatsantsan dani, Nima kuma sai na sayi wata irin girma na azawa kaina, bana wasan kannen miji da yan uwanshi, kuma sun fahimci haka sai suka bi bayan Baraka tante sama tante kasa, yan uwanshi da suke uba daya suma suka shiga girmamani musamman Ya'yan Harira.