← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 138

Sashe 70

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Yana tsaye aka sakawa hajiya bututun zukar numfashi, don alamar hawan da jininta yayi ya tab'a mata zuciya, shi yasa suka saka mata oxygen din, ko zai taimaka mata wurin zukar numfashinta, fitowa yayi daga dakin ya tsaya yana sauke numfashi. Sakatariyar Hajiya wato Salamatu, tana tsaye jingine da bangon dakin, kamar zata yi kuka. "Ya Hajiya da jikinta?" "Da sauki" ya furta a sanyayye, "Alhaji me ya faru ne?" D'ago farareen idanunshi yayi, ya zuba mata. Kafin ya sauke gwauron numfashi, lashe bakinshi yayi yana faɗin. "Ban san kome ba." Ya faɗa yana kallon ƙasa, "Amma taya haka ya faru?" Inji Salamatu, bakiɗaya hankalinshi baya tare da shi, sama sama ya tsinkaye muryan Anisah. Tana ihu kamar mahaukaciya, d'ago kai yayi ya zuba mata idanu, a hankali ta rage sautin kukanta. Daga nan ya maida hankalin shi kan nazarin shi.
Bayan awa guda, hankalin mutane ya koma kansu Familyn Ba'are, musamman labarin Amaan da abin da ya faru, kafin kace kwabo an shiga rubuce rubuce akansu da nuna su, kamar wutar daji labarin ya karad'e ko ina, sai da ta kai babu wanda yake shiga asibitin da sunan Familyn Ba'are, sannan wani abin mamaki yadda yan jarida suke ta zarya asibitin.
Karfe sha biyu na dare, Aryan ya farka cikin tsannanin ciwo da wahala. "Hammayo!" Ya kira sunan Majid. Kallon Aryan yayi yana duba na'urar da yake kanshi. "Anisah tana cikin tarkon Shaidaniyar Tani."
Bai kula shi ba, domin gani yake kamar magagin ciwo ne. "Hammayo ka bincika Anisah." Jan allura yayi ya mishi a cikin drip ɗinshi. Rike hannun Majid, "Na rantse da Allah, tana cikin damuwa kayi wani abu." Daga haka barci yayi gaba da shi. *Anisha kuma?* Ya faɗa a ranshi, a hankali ya fito yana jin wani tashin sense. Bai tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba.
A hankali ya fita tare da nufar office din da bai tab'a shiga ba, ya zauna yana me jin kamar ya fasa ihu. Wayarshi ya ciro yana saka a kunne. "Kayi tracking number Anisah ina jiranka." Kashe wayarshi yayi yana nazarin irin matakin da zai dauka.
-----
Marad'i
Bikin sallah, anyi shi cikin farinciki duk da bani da kowa a marad'i, amma kuma Maman Barakatu da Yaranta, sun saka ni farinciki. Haka muka kwashe wunin ranar muna yawo,koda muka dawo sallah muka yi. Akwai wani abu da na fahimta a rayuwa, shine duk inda zaka shiga matukar naka yana tare da kai zaka ji kamar ka samu duk wani farincikin da kake nima, haka nake ji a duk lokacin da na kalli Amirah sugrah, uwa uba Yazid da ya maida ni mutum, bawan Allahn nan ban san da me zan saka mishi ba. Bawan Allahn nan yayi hidima dani ko nace yana hidima da ni, domin taimakon da yayi min hár abada nake jin babu wanda zai min irin shi. Bugun kofar falon da nake kwance ya katse min tunanina, tashi nayi naga Barakatu ne da Amirah. "Wai zata zo wurinki ne har da kukanta."
"Mirah me yasa kike da halin rashin kirki, tow ai sai ki shigo." Da sauri ta miko min hannu na amshe ta. "Tante kiyi hakuri, kawai bata son nisa dake ne." "Kyaleta kiuya ce kawai, amma ina wani nisa sai tazo ai."
Haka na amshe ta, Barakatu itama ta shigo muka zauna. "Mama" ta kira sunana, tana rike hannuna, "Ko kina jin yunwa ne?" Kallonmu Barakatu tayi, kuma na bata abinci taki ci fa."
"Yau tana jin rikici ne." Haka na wuce kitchen na hada mata shayi na kawo mata, ta fara sha tana gamawa kamar wasa yarinyar nan ta koma gefe sai barci. "Halin Amirah sai ke Tante kada ki ce ban bata abinci ba, amma taki ci." Ta fada tana mita, ita nan Amirah ta bata takaici, tashi nayi na kawo mana abincin na ajiye mana, "Ga abinci." "Ni kan ba zan ci ba, tunda aka yi na jiya naci nayi ta yawon ban daki, na haƙura kunu nake ta sha kawai."
"Da dai kin ci abincin." Na fada mata, tura baki tayi tana mikewa, "ina gaya miki, cikina baya son abinci yanzu sai dai ki hada min shayin Amirah shi kan zan sha."
"Lallai cikin nan naki, kwadayayye ne tow ki shiga kitchen ki haɗa."
Dariya ta saka tana tafiya, "Tante na gode, Allah a koshe nake kawai zolaye ce." Tana faɗar haka ta bar falon, ajiyar zuciya na sauke, sau dayawa rowa yana rage kima, kyauta kuwa yana kara daraja da girma. Da nace mata ba zan bata ba, da ba zata ji dadi ba amma da nace taje ta haɗa gashi don kanta tace a'a, kuma abin da na lura kamar tarbiyyar mahaifiyarsu ce.
Yaran basu da kwadayi, sannan duk abin da zan basu basa rawar jiki a kai, asalima tsoron karba suke kada iyayensu, su musu faɗa kaga inda ake tarbiyya da adalci, a wannan zamanin da son kai da son zuciya, wani yaron baka isa ka shiga gidansu ba, idan ka shiga ma yayi ta maka rashin kunya iyayenshi na dariya wai ai yaro ne, wani kuma kana zuwa da shi wani wurin yayi ta kunyata ka kenan, duk ƙoƙarinka akanshi kuwa, irin wadan nan Yaran iyayensu ba karamin kokari suke wurin tarbiyyar su ba, sai dai muce Allah ya shirya mana zuri'a amma Iyaye na kokari akan Yaransu, domin wata zaki sha mamaki idan da zaka ga yadda take fama da Yaran.
Ban haifa ba, amma bana jin zan yiwa Amirah irin rikon uwar wani, saboda Amirah tawa ce ni ɗaya na. Shi yasa nake sonta da dukkan zuciyata, kuma bana jin har abada wani zai fini son Amirah, koda kuwa uwarta ne, sai dai ta gaya min ita ta haifi Yarta amma ba zata gaya min soyayyar yarinyar ba. Daukarta nayi zuwa banɗaki na mata wanka, sannan na sauya mata kaya, kafin na fito ni ma na nime ruwan zafi na zubawa cikina da yake cike, ina tsaye rike da kofin a jikin window.
Saboda iskar da ake yi, nake tsaye a wurin. "Ko wani hali Zuzu take ciki? Wani hali Munaisah take ciki ina suke yanzu?"
"Taya zan fara nimo su? Ina zan shiga ina zan fara nimansu?" Waɗannan sune manyan damuwata, ta ina zan nimo Yan uwana an samu shekara daya da wani abu kenan amma babu labarinsu. Jikina yaki amsar sun mutu yadda wani bangare na zuciyata take gayamin, nafi jin a jikina suna raye, a duk inda suke a fadin duniya sai na nimo su, "Amma taya?" Ajiye kofin hannuna nayi, kafin na cusa hannu a cikin sumar kaina. Taya zan nemo su? Ta ina zan fara? Babu shakka ina cikin damuwa. Allah ya kawo min mafita,. Amma dole na binciko yan uwana. *Mahaifiyarki fa?* Gabana ne ya fadi wanda yasa kofin hannuna faduwa niman wuri nayi na zauna, ina kallon duhun wajen. Mahaifiyata ya kamata na fara nemowa amma ta ina? Hawaye ne suka zubo min wanda ban san zan iya kukan ba, kuka nake sosai kamar raina zai fita domin ina cikin wani irin kewa, ina kewar Mahaifiyata sosai. Sai da nayi kuka me yawan gaske, sannan na mike zuwa ban daki nayi wanka nazo na kwanta a gefen Amirah.
***
Niamey
Wannan sallah bata zo da alkhairi ba, lokacin da Majid ya saka bayanan da aka turo mishi akan Anisah, sai da jikinshi yayi sanyi. Duba agogon hannun shi yayi ya mike tare da ɗaukar keyn mota. Bai tsaya ba sai gidan Anisah, kiran mijinta yayi ya ɗauka. "Gani a kofar gidanka."
"Tow gani." Can dai gashi ya zo ya buɗe, cikin gidan suka shiga. "Ina Anisah?"
"Tana dakinta taki bude mana kofa da yara."
"Muje!" Gaba mijinta yayi Majid yana bayanshi har kofar ɗakinta. "Anisah! Bude min kofar Abdul Majid Mamman Ba'are ne."
"Hammayo!" Ta kira sunanshi da karfi, "Na'am Autar Hajiya bude min na shigo." Ya faɗa da tausassshen murya. Kuka ta saka sosai, "Ka tafi idan suka san kazo zasu cutar da kowa don Allah." "Babu wanda zasu cutar miki da shi, fito ina tare dake." "A'a Hamma!" "Bana ce ki yarda da ni ba, kin san halin da Amaan da Jamilah suke ciki kuwa? Tow kowani lokaci mutuwa zasu yi, Aryan ya farka dazun nan kin ga yanzu dare yayi. Bude min kofar don Allah." Rufe bakinta tayi tana kuka kamar ranta zai fita.
"Ki kunna wayarki, ki duba abin da yake faruwa. Idan har kika san baki da hannu a cikin wannan abin da ake fada tow ina jiranki A falonki."
Mikewa yayi ya bar kofar ɗakinta ya dawo falon, a can dakin tayi kuka har ta godewa Allah, kunna wayar tayi tana ganin sakwannin mutane. *A yau muka samu labarin hatsarin da Yaran marigayi Mamman Ba'are suka yi, wanda aka ce daya daga cikin Yaran yake da hannu a cikinshi*
*An saki faife videon Amaan Mamman Ba'are wata majiya tace yar uwarshi tana da hannu wurin sakin faifen videon domin kada ya kalubalence ta akan mukamin shi da aka karba aka bata* sake wayar tayi da karfi, ta fito da gudu. "Wallahi Hamma ban san kome ba, na rantse da Allah ban san kome ba."
"Nutsu ki gaya min me ya faru?" Ya faɗa yana kallon mijinta, da ya mike tare da nufar kitchen ya kawo mata ruwa. Amsa Majid yayi ya bude mata, domin ya lura a firgice take, sai da ya sha ruwan sannan ya mika mata, da sauri ta amsa ta sha dayawan gaske. Sannan ta sauke Ajiyar zuciya.
"Mutuwar Babban sakataren kamfanin Alhaji Ahmed Ya'u, yana da nasaba da Sajjid Mamman Ba'are da Amaan, abin da ya faru a ranar da zai mutu. Amaan yaje Office din shi akan ya saka mishi hannu ya cire wani kudi ya turawa Sajjid yayi amfani da shi, amma Alhaji Ahmed Ya'u yaki, ya ce mishi ya je ya nimo amincewar hajiya ko Aryan ko kai."
Haka yasa suka yi sa'in'sa, har ya kira Aryan bai same shi ba." Shiru tayi tana share hawayen da suke zubo mata. "Bayan nan abin da ya faru shine aikin da ya sha kan Alhaji Ahmed yasa bai tafi gida da wuri ba, har aka shiga aka kashe shi ga abinda na samu lokacin da nake binciken Office ɗin shi." Wani dan karamin recorder, ta miƙawa Majid, tun da naji haka na sake saka idanu akan Amaan domin tun da aka bani matsayin nan yake turo min sakon na ajiye mukamina ko ya min rashin mutuncin. Da ya ishe ni ne na kunna mishi recorder din yaji da kunnen shi, ashe na kai kaina ga halaka domin Sajjid yaji labarin ina da shaidar abin da suka aikata.
Tun daga wannan ranar ban kuma barci ba, da fari turo min sakon waya ake na za a kashe ni idan ban sake bawa Amaan bayanan ba, na ki kula su daga baya sai aka fara min barazana da Rayuwar Yarana da Mijina. Bakiɗaya na rasa me ke min dad'i.
Bansan ya aka yi ba Aryan ya san da zancen ba, sai gashi dukkansu sun tawo suka ce min zasu tawo har da kai, ashe kafin su tawo Aryan ya kira Sajjid sun yi faɗa har da sa'in'sa Hammayo shine suka turo mota biyu suka buge su. Sannan suka sake faifen videon Amaan, bayan sun tilasta min na kira Hajiya na gaya mata kun mutu. Wallahi Hammayo ba da gangan nayi ba, Hammayo Yarana suka ce zasu kashe kamar yadda suka buge su Aryan.
"Me yasa baki gaya min ba?" Inji Mijinta.
"Su'ad ba zaka iya kome a kai ba, babban al'amari ne da mu kan mu, dole muke yakin sunkuru, lokaci yayi da zan ajiye aikina na soja, na tsaya akan Dangina. Idan ba haka ba, ina can za a shafe min yan uwa da dangi"
"Amma Majid"!
"Akwai jami'an tsaro, sun zagaye gidan nan babu wanda ya isa ya kuma muku abin da zai d'aga muku hankali. Yaranki kuwa ki kyale su, ba zasu iya miki kome ba. Idan ya kuma kiranki kice ni Abdul Majid Mamman Ba'are idan ya cika namiji ya kira ni." A razane ta kalle shi, share mata hawayen fuskarta yayi yana murmushi ya ce. "Eh ni na gaya miki haka." Sannan ya mike tare da barin falon. "Su'ad ka saka idanu a kanta, ka tabbatar tayi barci."
Daga haka ya musu sai da safe, ya fito ya samu sojoji a harabar gidan, "ku saka idanu akan ko tsintsu ne, idan ya zo giftawa ku sake mishi wuta."
"Sir!"
Barin gidan yayi.
Hajiya Tani tana tsaka da barci, hasken da ya cika dakin yasa ta bude idanunta. Majid ta gani zaune, a razane ta mike tare da cewa. "Uban me ya kawo ka."
"Ba kome sai dai kashedi nazo nayi miki, domin nasan zaki fi dauka sama da yadda kowa zai dauka, d'anki yana wasa da wuta, amma bai san wuta yake wasa da shi ba." Zama yayi a bakin gadon. "Ki ja mishi kunne, idan ya sake aka kama.shi ko tow a gidan Yari zai mutu, domin laifuffukan shi da yawa, sannan idan ya fahimci cewa Raihana ce ta haife shi ba Tani ba, akwai ." Da sauri ta sauka akan gadon ta zube a kasa, "Don Allah ka gaya min me kake so?" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. Mikewa yayi yana zaga dakin. "Me zance miki nake so, ai yaci ace kin gane me nake so."
"In sha Allah ba zan kuma barin shi ya shiga cikin al'amarinkaba, ba iya kai ba hatta yan uwanka."
"Tani kina da lissafi"
Bakiɗaya ta girgiza domin abu ne da bata kawo wani mahaluki zai san wacece ita ba, sai gashi an canko wacece ita. "Ki kula kowane yana.......
*Barka da sallah, ina jiran goran sallah na😹🥰😍😿😹*
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
+2347035133148 or 08130269641.....
#Mai_Dambu ce
[4/16, 8:16 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
Chapter 70 · 0% Book details