Sashe 46
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136
#Mai_Dambu
[2/23, 4:28 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*022*
"AURE!!" ya furta da karfi, yana me toshe bakinshi. "Eh aure zaka yi, aure nace zaka yi ko ba zaka yi min biyayya ba ne?" Idanuwanshi suka yi jawur ya kalli Aryan da Mahdi, mikewa Aryan yayi ya cewa Nabeeha. "Tashi muje cikin gida." Shima Amaan tashi yayi da Matarshi, domin kuwa ya fahimci maganar ta manya ce. Yadda fuskar Majid ya koma kamar zai nufi filin yaki, yasa kowa ya mike suka fita daga falon. "Hajiya ba zan iya aure ba." Cikin fushi ta ce mishi. "Wacce karyan kake tunanin zaka min kuma? Duk duniya kowa gani yake nice na rike maka kan maciji kake wasa da jelarshi, karewa har cewa ake ina zaune zaka kwaso min abin kunya duk wannan bai isa ka fahimci yadda nake rayuwa akanku bane? Majid ina son rayuwa ina son farinciki, amma na zabi na zauna da ku domin kuyi farinciki. Domin ku rayu cikin salama sannan ku zame min ribar hakurina na zauna daku, Ashe ban cancanci ka kyautata min ta hanyar yin auren ba?" Ta fada muryarta na rawa, kanshi a matukar sunkuye duk maganar da take yasan gaskiya ce kuma duk abinda ta faɗa gaskiya ne, amma kuma shi ba zai iya faɗa mata cewa bai da lafiya ba, ba zai iya cewa ga halin da ya tsinci kanshi ba, sai dai a shekarun baya .
A banɗakin gidan horan yara marasa jin magana, wannan tashin hankalin ya same shi. Jikinshi ya tafi baya da wani amfani sai fitsari, bata wani motsin sai dai yayi fitsari kawai. Sannan yanayin rayuwarsa bai bashi damar kallon wata mace da sunan soyayya ba, ya kasa sakin jiki ya yi soyayya domin idan ya ce zai yi soyayya me zai bawa mace? Saduwa tana daga cikin shika -shikan aure, shi tashi tazugen bazata iya amfanar shi ba balle wata. Sannan har yau baya jin zuciyarshi tana da wata shauki akan mace, abin da ya sani ko aiki ne ya haɗasu da mata yana tsayawa yaga sun yi nasara, haka yasa Umaima ta makale mishi. "Kuna gani ina magana ya bawa iska ajiyata? Abdul Majid ba zan kunshi bakin cikin mahaifinku na kunshi naka ba." Mikewa yayi zuwa gabanta. "Hajiya ki min uzuri, don Allah." "Na maka uzuri fa kace min? Na hana kaina farinciki na gina ku shine zan maka uzuri? Gaya min Meye matsalarka?" Hadiye yawu yayi yana kallon yadda take cikin b'acin rai. "Hajiya duk matar da zaki aura min, karshe wahala zata sha, domin idan ta zauna dani."
"Maza kake so kenan?" Inji Alhaji Abubakar Abzin, da sauri ya juya kanshi yana kallon Alhaji Abubakar Abzin, idanunshi har wani shekin kwalla yake tsabar tashin hankali. "Abba da ace zan so mazan da nayi farinciki,tunda a karshe dai na fahimci inda zuciyata take amma abin bakinciki babu maza da matan da suke iya burge ni ko shiga rayuwata. Duk wanda na zauna da shi don aiki ne da wani halin rayuwa"
"Ita yarinyar da kace a nimo maka fa?" Hajiya ta kara watsa mishi tambaya. "Yarinyar nan hatsari ne ya had'a mu, domin na bugeta da motana ne, kuma nayi mata jinya Hajiya ki fahimta auren idan nayi karshe."
"Abba ka zama shaidana idan Abdul Majid bai yi aure ba, tow kuwa sai dai ya zab'a ya hakura ya ajiye aikin shi ya zauna anan." Da sauri ya kalleta yana jin kamar kanshi zai buɗe wani irin sara mishi yake yana jin jiri. Harshensa yayi wani irin nauyi, so yake ya fada musu ba zai iya rike mace har ya mata kome ba, haka yasa shi jin wani irin jiri-jiri kafin ya ankara duhu ya mamaye mishi idanu, haka ya zube a gaban Hajiya a sume. Sai gashi ita tafi kowa shiga damuwa.
Salatinta ya shigo da Amaan, da yake makale. Lauya Sulaiman ya watsa mishi ruwa yana kwance jikin Alhaji Abubakar Abzin da ya rike shi yana tofa mishi addu'a. "Ba zance lallai kada kiyi yadda kike so ba, amma yana da kyau mu hakura da al'amarin auren nan." Wani irin kuka ne ya kwacewa Hajiya tayi ta yi ta kuma yi, muryarta yana rawa ta ce. "Abba don Allah kada ka hana ni yimishi aure, domin kuwa ina matuƙar son yayi aure. Duk wannan shiri ne."
"Ba shiri bane, tun ranar da Mamman ya gaya min ya bar shi a gidan horan kangararun Yara, ban kara yarda na zauna ba. Lokaci zuwa lokacin ina kai ziyara naji halin da yake ciki. Yaron nan ya sha wahalar rayuwa, idan kika ji abinda ya same shi ba zaki kara barci ba. Don Allah ki kyale shi ki mishi fatan Allah ya bashi lafiya."
Wani irin sanyi ta ji ya lullubeta, bata taɓa kawowa da gaske bai da lafiyan ba, domin a tunaninta zai tsarewa auren da zata kakaba mishi ne, amma kuma anya zata yarda da su? Tunda ya iya ajiye mata takardar sallama, babu abinda ba zai aikata ba don kada Alhaji Abubakar Abzin yaga kamar tana da bala'in taurin kai ta share hawayenta, amma a kasan ranta sai anyi auren nan ko zai mutu ne idan aka yi auren don ubanshi ba zata yarda ta ganshi haka babu aure ba, don haka ta dauke kai tana share hawayen da yake zubo mata.