← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 138

Sashe 54

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da zuciyata ta had'e dake bata yi shawara da ni ba, ni kuma bana jin a raina zan iya rabuwa dake don kawai kin ce na rabu dake, kiyi tunani da kyau." "Babu inda zan yi tunanin kawai ka rabu da ni!" Na faɗa cikin kuka. "Fadimatul Zahra'u, ni fa akan abinda nake so babu abin da ba zan aikata ba. Gaya min me aka miki kike kuka haka.". "ni yaushe nace maka anyi min wani abu, don Allah ka rufa asiri kada ka ja min sabon masifa, kawai ka tafi ka bar ni, idan da hali ka kore ni daga rayuwarka." Rike hannuna yayi yana kallon kantar hannuna, kafin ya ce min."su waɗanda suka miki barazana zasu miki wani abu har suke bautar dake baki gaya musu kina da Sultan Yazid Hamir ba ne?" "Kai ba iyakata ba ne, su kuma kai ne iyakarsu, ina da tawa rayuwar a wani wurin don Allah ka yi hakuri ka barni." Na fada da ƙarfi. Shigowa Aseem yayi d'aga mishi hannu yayi alamar ya tafi ya ce min. "Sun miki barazanar zasu kashe ki ko? Ko sun miki barazanar zasu maki fyade ne? Kai ko sun Miki..." Wani irin zabura nayi tare da kame jikina, da yake rawa sakamakon hada'a idanu da nayi da mutimin da kullum sai ya min kashedi akan Yallabai. Bin inda nake kallo yayi da idanu yaga na sunkuyar da kaina ina kara tattare rigar jikina ina faɗin."don Allah ka tafi kaji ka rabu dani." Kusan ban san fuskar shi ba, amma da safe idan na fita ina yawan had'a idanu da shi, haka yasa na karanci kwayar idanuwanshi, ko bai magana ba, nasan shine . "Darda!" Ya kira sunanshi, "Na'am Sultan!". Wani irin tsalle nayi na koma ƙasar gadon, domin shi din ne fuskarshi da Muryar shi ya tabbatar min da shine, na kame jikina da yake rawa na ce. "Don Allah ka tafi, ka tafi bana son ganinka wallahi bana kaunar ganinka ka rufa min asiri da halin da na shiga." Na fada cikin matsanancin kuka da ihu. Ganin haka ya sashi barin dakin asibitin. Darda ya bi bayanshi. "Aseem ka saka Darda ya gaya maka me suka yiwa Zeehrah!" "Wallahi Sultan Amiratul ta saka mu, mu mata barazana." Shiru yayi yana zare Idanu, ai yasan matuƙar bai magana ba shine a ruwa. Don haka yayi magana da wuri, koda suka isa gidan yarin. Zubewa Darda yayi ya lissafo mishi wadanda suke da hannu a cikin abin da suka mata. Duk a ka tawo dasu. "Me kuka mata?" Da kanshi yayi tambayar. Jikinsu na rawa suka nuna Darda. "Shi yace zai mata fyade bayan ya mata fitsari kai." Ware manyan idanunshi yayi yana tuno yadda tayi ta kame jikinta. "Abin da ka aikata kenan?" Inji Aseem. "Tuba nake a yafe min ba zan kuma ba. Wallahi saka ni aka yi, ba zan kara ba " murmushi yayi sannan ya ce mishi. "ka yanke mishi hukunci daidai da laifinshi. "Sultan ka yafe masa, ba zai kuma ba." "Ita yarinyar bata da gata ko? Babu wanda ya damu da ita tunda uwarta da Ubanta sun watsota duniya basu san dajararta ba ko? Gaya min abin da yayi mata akwai adalci a cikin shi, itama mutum ce fa. " "Bai kyauta ba " "Aseem ina son Yarinyar shi yasa bana kaunar kukanta, idan har ban bata tsaro da kulawa ba, taya zan ji da abinda yake raina " Haka ya mike yana faɗin. "Ka hukunta shi nace." Ya fita, gidansa ya wuce yabar shi ya samu Reshmah. Share ta yayi bai kuma kulata ba, domin idan yayi magana zata kuma fitar da hanyar da zata kuntattawa Zeehrah. Lokaci yayi da zai koma aljeria. Dama rabon ya hadu da ita yasa ya kasa komawa, a yanzu kuwa babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu koda kuwa mutuwa ce sai dai ta dauke su tare. Haka ya gama tsara yadda zai tafi da komin shi Addah kuwa, sakawa yayi aka mata duka, har sai da suka tab'a mata lafiyar idanunta ɗaya. Koda aka dawo da ita kallo ɗaya Ummi ta mata ta ce mata, "Kina tsammanin daga nan zaki kara samun sukuni ne? Kamar yadda kika saka rayuwar wacce bata ji ba bata gani ba a gaba haka zaki rasa kome naki." Addah bata yi Magana ba, sai dai dukarta da tab'a mata idanu ya kara haifar mata da bala'in tsanar Zahrah. Sai ta ga bayan Zahrah, sannan abinda ta fahimta Yazid niman kuɗinshi ba don ya cutar da kowa ba ne, niman kuɗinshi akan kanshi yake daukar kasada, ba kamar wancan mutumin da yake sayan Sassan dan Adam tare da sayan yan mata domin karuwanci ba. *** Sati biyu nayi sannan na dawo, a lokacin naga idanun Addah yayi wani bala'in girma gashi jini ya kwanta a cikinshi. "Addah baki je asibiti ba?" "Na je asibiti kika tambaye ni? Nace na je asibiti fa? Sai na illata rayuwarki Zahra matukar ina numfashi." "Baki illatata ba ma an kashe miki idanu, idan kika lakace ta sai dai lahira tayi bako." "Ban yi dake ba!" "Dama baki isa kiyi dani ba Addah." "Mara kunya kawai " "Marasa kunyar suna dayawa!" "Addah ki kyaleta muyi maganar idanunki." "Kinci Ubanki shegiya munafika." "Kayya da ina nufinki da sharri da kullum kaina zai tsaya, amma dake zuciyata daya ba zan iya nufarki da sharri ba." Na gaya mata, domin zuwa yanzu addah ta fara isata, ban san yadda zan yi da itaba amma na gaji da halin ta, "idan kina son idanunki,ki shirya gobe ki ga likita." D'ago kai tayi tana kallona, "Annamimiya kina min haka ne don na yafe miki!" Inji ta. "Idan kin so kada ki yafe min Addah wallahi babu abinda zai tsaya, bakya gabana asalima tausayi kike bani, daga lokacin da ƙaddarar Allah ta rabamu wallahi billahi azim sai kin yi fatar da ina tare da ke. Ba zan ce Hakkina yayi ta bibiyarki ba, amma nasan zaki so ina tare dake domin ni daya ce kawai. Zan tsaya a gefenki ki tuna da kin haifi Zuzuna, sannan ba zance nayafe muku ba daga ke har ita sai ranar da muka hadu ta gaya min dalilinta na cutar dani babu hujja. Idan yayi miki muje a duba idanun idan bai miki ba, ki zauna da shi Allah ya baƙi lafiya." Daga haka na kyaleta ina zan iya da bakin hali, bakiɗaya bata kanta take ba, hanyar da zata cutar dani kawai take nima sai kace na tare mata wani abu. *** Niamey. "Alhaji gaya min ina ke maka ciwon?" Kasa d'ago kai yayi ya kalleta. Kuma yayi shiru kamar baya wurin. "Kace jibi zaka tafi ko? Idan ka tafi zaka ga likita a can ko?" Duk ta uzirawa kanta, gani take kamar laifinta ne da sakacinta. "Alhaji" can kasan makoshinsa ya ce . "Hajiya lafiyata lau." "Ina lafiya mm, zan zo na ganka." "Assalamu alaikum!" Afiyyah ta shigo cikin nutsuwa domin duk rawar kanta da iyayinta, tana shakkar Majid da Aryan. "Wa'alaikimus Salam!" Hajiya ta amsa tana kallonta cikin kulawa. "Hajiya wai kizo keda Hammayo inji Nana!" "Tow shikenan ki ce mata gamu nan!" A hankali ta fita cikin wani irin taku me tab'a zuciyar yan maza, tunda ta shigo kallo daya yayi mata bai kuma kallon ko inuwarta ba, harkar gabanshi ya ishe shi. "Muje Alhaji." Me yasa Nana ta kira su bayan abinda ya faru kwanakin baya bata kuma shiga harkar su ba. Tashi yayi ya haura sama ya sako wasu kayan shadda ce skyblue, anyi mata ɗinki yar shara. Ta cikin rigar wata farar riga ya saka me dogon hannu, sai hular da ya saka ta amshi fatarshi sosai. Turaren pure oud ya fesa, bakiɗaya dakin ya hargitse da kamshinsa me dad'i...... #Mai_Dambu [2/27, 10:56 AM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
Chapter 54 · 0% Book details