Sashe 130
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin kyauta amma ni ba zan iya abinda kika yi ba, wallahi da kunya." Kura min idanu tayi kafin ta ce min. "Allah matar Hamma Majid, ina cewa kika yi bakya sonshi." "Ke tafi can, kin san daga inda muka fara soyayyar mu? A duniya babu mutumin da na sani da kaunar duhu kamar Baban Alfah. Har cewa nake Aminin duhu." A hankali na kai hannu gefen cikina ina shafa wurin na kalleta. "wannan ita ce tambarin haduwarmu, daga nan ya bani jininshi. Ke kina da lovestory irin namu?". Girgiza kai tayi tana dariya ta ce min. "Wai love story manya, ni ma zance auta ya zo mu kafa namu Titanic din don na lura lamarin na soyayya ne!"
"Zaytoonah kin raina ni!"
"Taya zan raina ki, nima irin soyayyarku nake son koya."
"Ai ba zaki iya ba" na tashi na tafi ban daki nayi Alola, na kan raba dare ina sallah tare da niman Allah ya dawo min da shi a duk inda yaƙe. Nasan bani da tsimi bani da dabara, amma iya wannan ita ce dabarata . Itama ganin ina sallah itama ta fara muna yi tare. Al'amarin Ubangiji ba wani abu ba ne da yake bukatar gaggawa, hakuri juriya, naci da nima a wurinshi. Nasan ban isa in dawo da mamaci ba, amma nayi imani da Allah da Majid ya mutu babu yadda za ayi jikina bai bani ba, kamar yadda aka ce ba a ga ko gawarshi ba.
Haka nayi ta fafutukar ganin na tsaya da kafata, ta hanyar rokon Allah. Allah sarki Nana har kullum tana zuwa tayi min hira, da sayawa Alfah kayan zak'i. Ni kuma na dauke abinda Majid yaƙe mata, na shiga saya mata nama, duk sati. Ba wai ina da mahaukacin kudi ba ne, amma nasan Majid ya bar min hanyar samun kuɗi, domin albashinsa da hannayen jarin shi ta account dina yake shiga, shi yasa nake samun kuɗi kamar yadda ba a zata ba.
Sannan Hajiya da Aryan suna kaina, idan wani abu ya taso kafin na maida hankali nayi sun min, ga Yazid da shima baya kasa a gwiwa bai zo ya duba ni ba. Haka dai na lura da yawan tambayar da yake min akan bani da ra'ayin aure ne, tuni nake shiga b'acin rai, na haɗe rai kamar bani ba dole ya daina min wannan tambayar renin hankalin. Amma ba karamin hidima yake mana ba.
Don ko da lokacin bikin Munaisah yazo,muka tafi aka yi shagalin biki a can muka dawo marad'i, anan da ga marad'i kuwa maza suka min caa, don ma mun haɗu da Aryan shi ya tsare min aurena kuma ba wai shigar banza nayi ba, kawai farin jini ne zan ce ko fitina irinta mazan zamani. Haka aka gama bikin muka dawo gida bayan mun kaita gidan ta da yake jekadir. An sha biki ba na wasa ba. Daga nan muka dawo gida, a matukar gajiye. Bayan bikin da sati biyu aka fara azumi, tunda aka fara Ibada ban tab'a fashin dare daya ko wuni daya ba, abincin sadaka Nana da kanta take rabawa, na yarda Majid shine zuciyar gidan, domin da baya nan hatta masu faɗa akan dukiya kowa damuwa yayi, duk bala'in yan uwanshi da suke uba daya sai da takai su da kansu suna begen shi bayan ya mutu.. sannan wani abin da na rasa fahimta Abdul B tunda Mamarshi ta hana shi niman Munaisah Mahdi na zuwa ta amshe shi sai ya zama yaki ya kuma mai da hankali akan aure.
Ni nasan tunda na mika al'amarina ga oga kwata-kwata, nayi imani ba zan ji kunya ba, a goman karshe kuwa sai da Hajiya tayi ta min fada, wai na takura kaina da yawan ibada, a lokacin murmushi nake yi domin na san ibadar ce abin da ya dace dani, kuma Alhamdulilahi na samu sauki da sukunin da nake jin rashinsa a raina. Naji wata irin nutsuwa da babu irinta, haka muka sha bikin sallah, bayan sauke azumi, sallah da sati biyu Zuzu ta haihu daidai za mu tafi Kamaru.
Ai babu shiri muka wuce Nigeria, anyi bikin suna da ban tab'a ganin irinsa ba, sai da naji hawaye ya zuba min domin bikin sunan yazo da wani irin bazata, sunan Yaron da ta haifa Abdulmajid, basu faɗa min ba sai da muka zo wurin walimar naga Abdulmajid, nayi.
[5/29, 07:48] Hlm: BHB274
Wai na rasa me zance, kuma sai nayi ta kuka Allah yaso tun basu fadi sunan da zasu saka ba, na yi akwati biyu. Na kayan uwar da yaron Zuzu ce fa, a duniya idan ban yiwa Zuzu hidima ba wa zan ma wa? Danginsu na Numan sun zo, ni da ita muka yi ta musu hidima. Sannan duk wanda yazo a cikin dangin Mamanshi sai da muka ware musu turamen atamfa chiganvy me kyan da tarkacen suna domin saniya da raguna biyu ya yanka, daya rago na dangin Mamanshi, daya rago na mai jego. Saniya kuma aka cire na wurin hajiya uwar rikon shi da dangin Babanshi, sauran muka saka a hidima. Mun sha hidima sosai kamar me kafin muka nutsu na kara bata shawarar ta kula da dangin mahaifiyarshi ba sai sun bukaci wani abu ba, idan da hali ta saka yayi musu, ai yiwa kanta ne da yarta da. Kuma taji dadin hakan da nace mata. Sati daya muka wuce kamaru bikin Zaytoonah koda yake shegiya ta ce kome ni ce. Haka muka yi hidimar dangin mijinta har da sabon kayan aure ita da yarta, wannan lamarin ya min dad'i. Wato tunda na ga Mamata naki komawa Nijar, ni da Alfah wacce yanzu take kokarin tashi tsaye wata goma, Hajiya tayi waya ta kira Malamijo amma naki dawowa, ina ganin kiranta zan fara dariya kawai.
Yau ma muna aikin dambun tafiya ta kira na dauka ina dariya. "Hajiyata!" "Don Allah ku dawo wallahi babu kowa a gidan?"
"Hajiya ina Anisah?"
"Ke tafi can, wacce kuma haka dalla ki kawo min alfa!" Inji Nana tana mita, "Yanzu banda Allah ya nufa Alhajin Allah ya haifa min Alfa ya zan yi? Ina sai dai nayi ta bada labarinshi ana ƙaryata ni, Zahra'u ban san lokacin da kika zama munafika ba, don Allah ki kawo min yar y'ata."
"In sha Allah Hajiya Nana matar Abdul Majid Mamman Ba'are, matar ƙarfen Majidu angon Nana da Nana!" Sai ta fashe da kuka wiwi. "Allah ya miki Albarka, kin saka ni jin kewar Alhajin Allah"
Murmushi nayi ina faɗin . "In sha Allah duk inda yake yana cikin Amincin Allah kuma zai dawo gare mu!"
Haka muka gama wayar ina jin kwalla na cika min idanu. "Ki cigaba da addu'a, kada ki saka ran ba zai dawo ba."
Murmushi nayi ina kallon Mama, "Mama nasan Allah yana tare damu, kuma shi yafi mu sanin gaibu. Don haka ba xan tab'a kauce hanyar da ba tashi ba, na san ina cikin damuwa da kewarshi, matsayin mijina ba matsayin dan uwana ba, hakikanin gaskiya ina kewar shi." Na fada muryata na rawa, a hankali na fashe da kuka. Don nasan ina matuƙar son ganinshi, sannan idan nace bana buƙatarshi nayi karya, barin aikin dambun nayi na koma gefe ina sharbar kuka, murmushi Mama tayi tana faɗin. "Allah yana gani bana jin dadin ganinki a haka, ki cire damuwar Baban Alfah a ranki, ki fara tsayuwa da kafarki. Kudin da ya tara wata rana zai kare amma idan kika tashi kina nima Allah zai dafa miki, sannan damuwar zata zo miki da sauki duk wanda kika gani a wannan lokacin kokari yake ya tsaya da kanshi ko aikin kamfanin ki koma zaki ji sauki da sassauci , a ranki."
Akwai wani sirrin da Allah ya bawa Uwa, wanda duk duniya babu na biyunta, kuma nasan Mama tana cikin Wadannan iyayen, Mama bata barmu haka ba don mun girma muna da aure ai mun san ciwon kanmu a'a ita kanta ta gaya min na yawaita mika lamarina ga Allah, sannan ta gaya min duk halin da nake ciki kada na manta nayi wanda ya fi shi zafi da muni, sannan bata bar mu hakaba sadaka da azkar tana yi akanmu mu biyu, don na mata magana kwanaki ta ce ai ita babu wani damuwar namiji a ranta sannan ita ai ba zata zama damuwa ga Addini ba, tunda Muslunci ya bata damar idan ba zata yi aure ba ta kame kanta tayi ta ibada ta zaɓi wannan mazahabar, sannan idan zata yi aure mai mata zata aura, na farko Matarshi idan bata da hakuri ta hana ta sakat, idan ta samu mara mutunci ya sakata a gaba akan dan abinda take, dake ta karanci dabi'un dan adam, shi yasa ta zabi kula da Yaranta.
Haka ya kara min kaunarta, domin ta hakura da farincikinta don mu kada wasu su raba mata hankali, kuma na san har da tsoron fitinar abun da ya faru lokacin aurenta da Baffa'm. Shi ne gaskiyar maganar da zan iya faɗa.
Bayan kwanaki tara, muka bar kasar Kamaru zuwa Nijar, tare da alƙawarin daukar shawarar da ta bani, ina dawowa farinciki kamar me, kwana na sha daya da dawowa aka yi layya, yawon sallah muka je har marad'i, na samu Munaisah tana laulayi, ita ke tambayata Addah. "Tana nan lafiya sai godiyar Ubangiji Kawai amma Adda tana cikin jarabawa, Allah ya bata lafiya." Da gaske ganin Adda yasani kin tunota, Addah ta wani irin malkwadewa kamar wacce tayi hatsari. Yawu na zuba ga wuyarta yayi wani irin karkacewa kai ni wallahi sai na ga kamar an sauya mata halitta ne. Kuma tana magana sai dai bai fita sosai burinta bai wuce ta samu yadda zata cutar damu ba.