Sashe 50
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Nace kina da saurayi?" Ya juyo yana kallona." Zare idanuwa na fara, da wasa da ya bakin mayafina. A hankali yake takowa na juya bayana naga ko wani abu yasa yake biyo ni, sai naga haka kawai koda na juya ya matso kusa dani sosai. "Baki da saurayin ne?" Hadiye yawu nayi na gyada kai na, a hankali ya sunkuyo da kanshi a tunanina sumbatar bakina zai yi, da sauri na kawar da kaina. A hankali ya kai hannunshi gefen wuyata ta wurin mayafina ya kad'e min gizo-gizon da yake kaina.
"Ki kula." Ya fada yana kallon kwaron. Hadiye yawun bakina nayi ina kara jin kamar zan saki fitsari.
---
Cikin larabcin da bai gama rike bakinta ba, Addah ta kara gyara zamanta ta ce mata. "Idan nayi miki karya, ki saka a kashe ni a binne gawata, amma yarinyar da Yallabai yake fita da ita yata ce, kuma zaki iya zuwa gidan mu, ki ga irin kyawawan kyaututtukar da yake kawo mata." Mikewa tayi tana faɗin. "Muje!" Haka Addah ta mike jikinta yana rawa ta ce mata. "Tow!" Suka tawo har gidan, wato ita Yazid zai ci amanarta. Ita zai tsallaka yana bin karuwa da ta gama yawon karuwancin kafin ta fado hannunshi, bata kara sarewa namiji ba dan goyo da zani ba ne, sai da ta ga katon akwatin kayan da ya kawowa uwar da yar, ciwon bakinta tayi sannan ta juya ta fita cikin nutsuwa Addah kuwa murna kamar zata daka tsalle.
Haka Reshmah ta koma gida, ta zauna tana tunanin me zai faru, me zata aikata da zai bawa Yazid tsoro ita ba kalar Matar da zai ci amana bane . Bai isa ya ci amanarta ba.
---Sai dare muka dawo tun a hanya aka tare shi, ana gaya mishi abin da ya faru cikin wani irin yare, murmushi yayi ya ce musu. "Suwa laula!" (Shi kenan naji) kallonshi nayi domin ban tab'a zatan yana jin wani harshe bayan Hausa da larabci ba.
"Wani yare ne haka?" Murmushi yayi ya ce min. "Harshen darsa, yana da saukin amfani.". "zan koya!" "Zaki iya kuwa?" "Hmm!" Haka ya rako ni gidan sai da na shiga ya ce min. " Za a kawo miki abinci." "Tow na gode!" Daura yatsar hannunshi yayi a baki ya ce min. "Shiiii" hadiye yawu nayi. "Kada ki b'ata min alakata da godiya." "Shi kenan!" Haka ya bani Babyn muka shiga cikin gidan, yana fita yayi waya aka kawo min abinci, muna kwance aka buga kofar kallona Addah tayi na mike na bude kofar na amso abincin na fara ci, tashi tayi zata saka hannu Ummi da take gefen gadona ta doke hannun da wani sanda, sai da kashin hannun yayi ƙara. "Kika sake wani abu ya shiga bakinki sai na shakeki har lahira munafukar banza." Daga haka bata ci ba na kalli ummi ta dauke kai. "Me yasa kika hanata!" "Ba zata ci ba wallahi." Shiru nayi ina kallon Addah da ta koma ta kwanta. Ban kuma musu magana ba, sai da zan fita Addah ta ce min. "Bani Aminatu na taya ki goyanta." "Ba zata baki ba, duk abinda zai faru sai dai ya faru!" Inji Ummi. Fita muka yi, nima na nufi gidan Yallabai. A falon kasa na same ta a hankali naji jikina ya bani akwai matsala. Haka na wuce na fara aiki har na gama. Tana zaune sai da na gama zan fita ta ce min. "Ke jira ni!" Daidai shima yana saukowa daga sama, kenan ta shiga kitchen, kamar ya san nufinta, tana fitowa kawai ta watsa min soyayyen mangyad'a da ta dauko a fry pan.
Rumfa yayi min ta zuba mishi a bayanshi, bata san lokacin da ta saki fry pan din ba, "Yazid!" Ta kwalla mishi kira, bude idanu yayi a kaina."Yallabai!" Na kira sunanshi. "Jeki gida lafiya ta lau." "Yallabai bayanka fa?" "Ba kome, jeki"
Ya fada min da wata irin murya, da sauri na fita tana rufe da fuskarta tsoro ya kamata, hadiye yawu tayi tana kallonshi. "Me kike nufi?" Jikinta ne ya fara rawa, "don Allah kayi hakuri." Jan iskar bakinshi yayi ya yaga rigar tare da zama a bakin kujerar falon, da gudu ta fita ta kira Aseem ta gaya mishi, shi ya tafi har wurin likitan ya tawo dashi, suna shiga suka same shi a falon. "Garin yaya?" "Nice na zuba mishi ba da gangan ba." Bai ce uffan ba har likitan da Aseem suka yi ta cire mishi rigar da ya hadu da fatar bayanshi, ya zuba mata idanu. Cikin wani irin Imagining da Zahrah zata zubawa man gyadar nan a fuska. Sai lokacin ya iya bude baki ya ce Mata. "Nufinki Zeehra zaki zubawa?" Zubewa tayi tare da rufe fuskarta ta fashe da kuka. "Kayi hakuri sharrin iblis ne." Ta fada tana shasshekar kuka, haka ya cigaba da kallonta tana kuka. Yana wondering yadda zuciyarta ta mutu da tunanin ta nakasa mace yar uwarta, murmushi ya saki a hankali yana kallonta. "Sultan kayi hakuri don Allah!" Ta fada tana waiwayen bayanta. "Aseem!" Da rarrafe ta kama kafarshi. "Don Allah ka rufa min asiri Sultan kishinka ne ya saka na aikata haka, Sultan ba zan kara ba." " A bata abinci dare da rana, ta zauna a wurin sai na warke." Fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita,
"Sultan afuwa!" "Aseem!!" Zubewa yayi akan gwiwarshi. "Uwar Yaranka ce, kuma mace mai daraja a gare ka, kasan haka kuma kai da kanka ka gaya mana babu mace mai darajasama da Reshmah."
"Zeehrah tana da daraja, darajarta me girma ne!" Ya fada yana kauda kai. "Matar da nake aure idan bata ji magana ta ba nawa zata ji? Idan wani abu ne ya had'ata da yarinyar waye zata tinkara? Dole sai ni, wato shine aka gaya mata xata kona musu yar mutane. Idan ta lalata mata fuska fa? Fisabilillahi ace mangyad'a zata zuba a fuskar Zeehrah...
#Mai_Dambu
[2/25, 7:57 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*Muna da stone Veils da plain,sai hular Yara, masu kyau akwai veil na Yaran shima.*