Sashe 12
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe biyar na asuba ya farka, ya nufi ban daki yayi wanka da alola ya fito falon suka yi sallah,a lokacin an fara ruwan sama. Kitchen Aryan Mamman Ba'are ya wuce ya hada musu abin karyawa. "Kasan yau zamu bar garin nan." "Eh! Amma ai ana ruwa." Kallonshi Aryan yayi kafin ya ce mishi. "Zamu wuce Enugu a can muke da jirgi zuwa kano."
Haka ya zauna ya ci abinci, suna hira sama-sama. "Ya Amaan?" Tab'e baki yayi yana faɗin." Yana nan." Daga haka dukkansu babu wanda ya kara cewa Uffan. Har suka gama, Aryan ya shiga dakin Majeed yayi wanka ya shirya sannan ya zo ya kwashi kayansu, yafita da su. "kana nufin kwana biyu da kayi baka fita ko ina ba?" Tab'e baki yayi irin abin ya zame mishi jiki ya ce mishi. "Ina zan leka? Gari kullum ruwa, da nasan haka ne, ai da na tawo da Sanayah!" Shiru yayi yana kallon yadda yake shirya kome. Bayan ya gama shima ya koma ya shirya tsaf cikin Kananun kaya, suka rufe gidan bayan ya kwashe kayan abincin ya rubutawa Emmanuel, yayi amfani da shi. Sai da suka fara zuwa headquarter yayi sign sannan ya leka asibiti ya duba Magaji Abba Chindo, da yake zaune ana wanke mishi ciwon shi, zama yayi bayan an gama nurse din suka fita ya amshi sauran kayan aikin ya cigaba da gyara mishi ciwon. "Ba na son na kuma maimaita maka abin da ya wuce, amma zan gaya maka gaskiya yarinyar nan da ka saka a bi sawunta ni na taimaka mata, ba don kome ba sai don na kubutar da kai daga sharrin zina. Nasan kayi nisa amma ka gwada barin shi zaka fahimci abin da nake nufi. Ni zan wuce ƙasarmu, ka sani ba wai bamu da inda zan yi aiki ba ne, sai dai wannan karon idan na tafi ba zan dawo ba,na bar maka ƙasarku na koma aiki a babban headquarter Naval na French." Daga haka ya mike zai fita daga cikin dakin. " tow sai me? Bayan sai da na zama nakasashe zaka gaya min na daina zina? Sun kashe min gaba wadancan karnukan."
"Zina ya janyo maka haka." Daga haka ya juya ya fita, bai samu Dr Umaima ba, sako ya bar mata tare da tura mata kuɗi, sannan ya fita daga asibitin suka bar garin ma baki daya.
***
Ranar da na cika kwana shida, aka sallame, Doctor Umaima tazo tare da mika min jaka. "Gashi akwai ticket na jirgi zuwa Yola, daga can zaki samu motar taraba. Don Allah ki koma gaban Iyayenki ga wannan kuɗin inji Captain ya ce a baki kuma yana bada hakuri da abinda ya faru. Shima ba a son ranshi ba ne."
Murmushi na sakar mata, ina faɗin. "Duk wannan kuɗin?" "Akwai matsala ne?" Girgiza kai nayi, sannan na ce mata. "Ko zamu je banki a tura min kuɗin." "Wani bank ne?" "Ecow bank!" "Me yasa sai bank din?" Saboda idan na koma zan tafi niman Mamana ne ne a Kamaru.". "ok muje!" "Gaskiya kin yi dabara, yadda Adda ta shirya wulakanci tana ganin kudin nan zata raba ki da su."
Murmushi nayi na wuce muka fita, da taimakon Aunty Umaimah muka tura kudin account dina, sannan suka sa ni lallai sai na yi welcome back din layina. Bayan nayi na sayi wata yar ƙaramar wayar bani da buri akan babbar waya. Haka yasa nake rayuwata da yar karamar waya abina.
Lokacin da muka zo gida, na samu su Addah sun gama shirin tafiya. Koda na gaya musu ni jirgi zan bi sai suka yi shiru, Zulaihah itama ta kira wani sugar daddy dinta ya tura mata kudin ticket, sai gashi baki ɗaya sun biya har da Addah da Ummi. A daren muka bar garin fatakwal. Muka wuce garin Yola. Mun isa wurin ƙarfe daya na dare, don haka muka kwana a masallacin da yake cikin airport din, gari na wayewa muka fito tare shiga kasuwa muka yi sayayyar tsaraba, sannan muka dauki hanyar taraba.
A hankali muke tafiya, hankalina yana kan wayar hannuna, na turawa Sabiru sakon gamu nan muna hanya, amma shiru bai dawo min da ansa ba. "Ya dai Zahrah?" Tsaki nayi ina yatsina fuska."Sabiru bai kira ni ba." Juyawa Addah tayi tana kallonmu, fuskarta dauke da murmushi. "Allah ya sa ba halin yan maza zai miki ba." Shiru nayi ban iya magana ba, amma tabbas akwai wani abu a kasa, haka kawai Sabiru baya kin daukar kirana ko sakona ya gani.
Wai ma kun san wacece Ni?
Fadimah Zahrah Buba Shad'ari, shine cikakken sunana. Mahaifina Bafulatanin taraba ne daga karamar hukumar Takum. Gari ne da ya hada makiyaya da manoma.
Alhaji Shu'aibu Jauro shine kakanmu dattijon arziki, mutumin kirki da babu biyun shi, Allah ya mishi rahama. Domin ya rasu tun ina da shekara shida a duniya, amma ba zan manta alkhairinshi ba.
Addah ita ce Babbar yarshi, kuma kangararriya mara jin magana. Wato ana cewa albasa batayi halin ruwa ba, hakan ce ta faru da Addah domin bata dauko halin iyayenta ba dukka biyu, sai Baffa'm wanda shine d'a na biyu da yake bin Addah, mutum ne me hakuri kawaici da Dattaku. Baffa'm yasan darajar kanshi da rayuwarshi. Mutum ne da yake da ilimin addini sosai, sai dai bai samu halin yin ilimin boko ba, sai ya saka a ranshi matukar yana raye Yaranshi sai sun yi karatun boko, wani abin haushi. Nenne Matarshi kuma uwargidansa, babu ruwan ta domin har wurin ardo ta kai Baffa'm don yace sai yaranshi sun yi boko.
Haka ya hakura dake yana tafiya da shanu cirani, musamman yankin Gyambu da yake da yalwataccen yanayi me kyau, yana zuwa yayi watanni sannan ya dawo da su. A irin wannan tafiyar ne ya hadu da Mamana domin tafiyar ta kaishi har kamaru, a can ya aurota ya kawota. Lokacin Munaisah tana da shekaru biyu a duniya.
Tunda Baffa'm ya auri Mamana, mutanen gidan suka sakata a gaba, wai ita Rumada ce wato bayin fulani, duk da kana ganin Mamana kasan yar babban gida ce, domin duk rugar mu babu macen da take sanye da zinari a kunne sai ita, sannan take gaya min ina Yarinya su Mahaifinsu kana cika shekaru goma a duniya kake fara zuwa aikin hajji, daga nan duk Shekara kana tafiya Umara. Wannan yasa duk yan gidansu suka je aikin Hajji.
Baffa Modibo shine ke bin Baffa'm, sai dai mutum ne mara kirki,haka yasa har da shi a cikin masu musgunawa Mamana. Haka tayi ta rayuwa a kuntacce, a lokacin da aka haife ni kuncin yayi yawa, domin a lokacin Addah sun dawo da Mijinta ya saketa, haka ta zo ta saka Mamana a gaba da fitina da tashin hankali. Har zuwa lokacin da ta samu wata kawarta ta kawo mata ziyara daga kano suka tafi tare da Addah, ashe tafiyarta Kano Saudiya ta tafi.
Wato mu yan gidanmu Allah ya zuba mana baiwar kyau, sai ma dai nice da nake da duhun fatar Mamana. Haka yasa yan gidanmu suke yawan min ba'a. Bayan tafiyar Addah Baban Zulaihah yaso ɗaukarta, amma Kakanmu Alhajijo yace ba zai dauketa ba, sai ta kai shekaru bakwai a duniya.
Haka muka taso da Zulaihah duk da ta girme.ni, haka Mamana ta haɗa mu ta riƙe. Tunda Addah tabar Nijeriya ta isa Saudiya, take tukaranci da rashin jin magna, har dai ta samu yadda take so.
A nan kuwa ba zance me ya faru ba, domin a lokacin ban wuce shekaru Biyar ba, aka nime Mamana aka rasa, sama da kasa ta b'ace, wannan al'amarin ya daki babana da Alhajijo a lokacin ya kwanta jinyar da tazama ajalin sa,, haka muka zama marayun dole ni da Zulaihah. A lokacin Baffa'm ya saka ni makaranta, kuma cikin ikon Allah sai Ubangiji ya min baiwa na daukar karatu, domin ina da shekarun goma a duniya na gama primary school. Na shiga secondry school, a gurin a saka sunana a registered din yan jss one aka saka a na yan jss two, haka Baffa ya cika musu kudi domin shi mutum ne mai son yaga kayi abinda yake so.
Ina da yayu maza biyu, Babangida da Habibu, sai Munaisah take bin Habibu. Sai ni nake bin Munaisah, sai Kuluwa take bina, sannan Dizah burin Baffa'm akan mu yayi yawa amma haka Nenne ta kashe mishi burin akan Yaranshi,ni ce kawai yake da iko dani, shi yasa ina shiga jss3 a shekaru goma sha daya na kara riƙe wuta, koda muka shiga Ss1 bana wasa, ina shiga ss2 na nime Baffa'm ya biya min waec da neco, sanin ina kokari yasa shi biya min ikon Allah sai gashi da muka yi jarabawar naci, duk da bani da shekaru amma ina da dan tsawon kafa. Sannan ni siririya ce sosai. Kamar mamata haka nake.
A shekarar da na gama secondary Hajiya Addah ta dawo, ganin mu yasa ta fara shiri akanmu, sannan a gefe guda kuwa burinta ya kusan cika, don haka ta kwana biyu ta sayi shanu ta bawa baffanmu, ta koma ashe a Lagos take da aka kore hausawa masu tuwo-tuwo shi ne ta dawo fatakwal. Ganin mu kawai yasa tana komawa tayi gaggarumin shiri, tana zuwa ta dauko Ummi da Munaisah,suka zo watansu biyar suka dawo. Ni da Zulaihah da zasu koma aka tawo damu,a lokacin Baffa'm ya bani takarduna,nayi kokarin niman cigaba domin ta gaya mishi zan koma makaranta. Da muka zo kuwa kudin da ya bani taso kwacewa ni kuwa na ce ta mai dani gida baki ɗaya shekaruna sha huɗu, ina da wayewa ta ilimi,domin saura izu goma na sauke Kur'ani mai girma.