Sashe 14
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin wani irin yanayi mara daɗi, nake barcin nan, make min cinya aka yi na bude idanuna. "Ya?" "Kawu na kiranmu." "Karfe nawa yanzu?" "Tara da rabi." Tashi nayi ta mika min kofi da dafafen madara."sha ki hada da magani sai mu tafi." Yatsina fuska nayi domin bana son shan madara, haka Allah yayi ni bana son madara idan ba dole ba, haka kuwa na sha, ina tsaki sannan na mike muka fito zuwa dakin Baffa'm, bayan na sha kayan sanyi. Koda muka isa yana bakin kofarshi yana zuba ma Yaran Baffa Modibo shayinsa. D'ago kai yayi ya kalle ni sannan ya saki murmushi, yana faɗin . "Innawuro sai yanzu kika farka?" "Eh Baffa." "Zulaihah kema shigo." Haka muka shiga dakinshi, zama muka yi ga dadi da dumi. "Kun iso lafiya?" "Alhamdulillahi, mun same muku lafiya?" "Masha Allah, Alhamdulillahi. Ya jikin naki?" Sai a lokacin fuskarshi ta sauya kaɗan. Zuba min Idanu yayi kafin ya gyara zama ya kira sunana. "Fadimah Zahrah!" Gabana ne ya fadi, na kalle shi kafin nayi kasa da kaina. "Na'am!" "Idan aure kike so, me yasa baki gaya min ba?" Girgiza kai nayi, a hankali ya shiga min nasiha, Baffa'm yana da matukar hakuri da sanyin hali, haka yasa ba zaka tab'a jin shi yana faɗa da wani ba. Sai da ya gama ya zuba mana idanu yana son jin me zamu ce. "Kawu shad'ari!" Kallon Zulaihah yayi zata magana na rike hannunta. "Meye kike son hana ni magana?" "Ya wuce, a barshi ya wuce har gaban Ubangiji ya wuce." "Kawu laifi ne don ta kare kanta daga dattin zina? Yar uwarka azzaluma ce, bata da imani."
"Kuyi hakuri nasan Allah yana tare da ku, kuma me yasa baku gaya min zaku zo ba? Garin jenuwa babu lafiya, ai da ban barku kunzo ba. Muma zaman dar-dar muke."
"Lafiya kawu?"
"Lafiyar kenan, sai dai wasu daga cikin yan uwa Makiyaya kuma abin da na fahimta baƙin haure aka samu suka shiga gonar mutanen suka musu barna sannan suka kashe musu mutane kusan goma. Haɗe da yiwa matansu fyade, tun ranar juma'a suke son daukar fansa, hukumar tsaro suka shiga cikin lamarin, yanzu haka babu dad'i garin baki daya, shi yasa nake son idan da hali gobe ku bar garin nan."
"Baffa'm na dawo kenan fa." Kura min idanu yayi na wasu dakikai kafin ya ce min. "Kiyi hakuri ki koma can, idan kin samu miji maza ki kirani ki gaya min."
"Baffa'm Sabiru fa?" Kaina a sunkuye."Allah bai nufa shi ne abokin rayuwarki ba, yayi aure suna jalingo da Matarshi da yake yana aiki a can." Wani irin sanyi ya shige ni daga waje har cikin jikina, na hadiye wani irin yawu me daci. "Baffa." Kura min idanu yayi sannan ya ce min. " Allah yana sane dake, ga wannan takardun, ki tabbatar kin nime Mahaifiyarki, domin duk inda take tana cike da kewarki."
"Baffa'm me yasa ka bani?" Na tambaye shi lokacin wani irin sanyi da zazzaɓin sun rufe ni. "Akwai rayuwa akwai mutuwa idan na kasance araye zan tayaki nimanta, idan muka bana raye zaki tsayawa kanki, Zulaihah ku rike amanar juna,kada ku sake wani abu ya raba tsakaninku, ita duniyar ba kome sai rud'i da karya, ba kome zaka bashi damar fushi ba, na horeku da zumunci, kuma duk abinda Addah zata muku, kada ku sake ku yi fushi Allah yana tare da masu hakuri." Nasihar Baffa'm yake mana, sai da ya gama sannan ya shiga tsokanarmu. "Kun tuna kuna yara kuke damben wace ce zata sha furar Alhajijo." Ya dauki wani allon karfe, ya shiga rubutu yana kallona. "wannan zamanin dole ka nimawa kanka mafita, idan ba haka ba, sharrin zamani sai ya hada da zuri'arka." "Haka ne Kawu " murmushi yayi sannan ya cigaba da rubutun,yana jan mu da hira har ya gama ya wanke a kwanon shan, ya dauko wani saiwa ya jefa yana faɗin. "ku dai rike gaskiya da Amana, ban da cuta da cinAmana, zalunci bai da tsawo domin idan alkadarin ya karye sai an tozarta."
"Haka ne!" Suka ci gaba da hirarsu da Zalaihah ina jin su, har ya gama.ya bawa kowacce ta sha. "Idan kun fita ku bawa Ummi da Munaisah, su sha." "In sha Allah!" Muka fada, "Baffa'm rubutun me ka bamu?" Murmushi yayi ya ce min. "Tsarin jiki ne?" Gyada kai nayi, har zan fita ya ce min. "Innawuro!" Juyawa nayi, "zo nan!" Komawa nayi na zauna, bude wani ƙunshin takarda yayi ya mika min. "Ina ta ajiyewa kafin aurenki, ki saka a wannan abin me kama da lalita, wata rana zai miki amfani kada yunwa ko talauci ya sa ki.aikata Zina don Allah ki rufa min asiri kinji. Duk inda zaki kada ki zauna babu sana'a wannan gwal ce na Mahaifiyarki."gyad'a Kai nayi, a hankali na mike ina mishi godiya, har zan fita ya mika min wasu leda. "Shi wannan abubuwan masu mahimmanci ne, na yaran Harirah ne nasan..." Burr muka ga shigowar Nenne, fisge ledar tayi, "wato ga yar so, ni kuma nawa yaran da baka so su mutu da bakinciki da yunwa bani. Ai keda ganin uwarki sai a lahira."
"Harirah kenan. Allah ya bamu sa'a." Daga haka na fita na barsu, tana saukewa Baffa'm tijara. Ni kan cikin gidan na nufa duk da wani irin zazzaɓin da nake ji, bai hanani zuwa sassan Baffa Modibo na gaishe su ba,har dama-dama Yakumbo bata da matsala, sai Amaryarta ce ma Bama shiri. Yakumbo wacce sunanta Sarai tana da yara hudu, Shu'aibu shine babba yana yola a can yake karatu shine yaron da ya fita Zakka a bangaren Baffa Modibo. Sai Jamilu yana nan domin yayi aure yana garin takum, sai Sa'idu kafin Ummi.
Amaryar Baffa Modibo kuwa, tana da Yara kusan shida duk maza ne, sannan irin haihuwar nan na kunika. Yaran kamar kwarkwata.
Aminu shine babba, sai Zakaria, Amadu, Adamu, Abdullahi, Abubakar dan karaminsu, wucewa dakin mu nayi na kwanta, ina ganin Zuzu tana dafa mana abinci,domin doya ce take dafawa zata mana miyar kwai. Zulaihah akwai kokari domin duk inda zata, tafi da gidanka take yi, har indomie tazo mana da shi, ga kifin gwangwani irin me Mai din nan. Tana gama dafa doyar take bani labarin yadda tayi da ruwan rubutu,ta ce min. "ke nabasu suka ki sha, ai kuwa na sha rabi na bar miki rabi."
Ni dai bance mata kala ba, na cigaba da kwanciyar da nake, domin idan na bude baki zan yi magana kuka ne zai kwace min. Haka na dauki lalita ta, ina kallo. "Zahrah ya dai?" Idanuwa na da suka cika da kwalla na kalleta."Ashe Sabiru yayi aure bai gaya min ba?" "Mtsew sai kace autan maza." A hankali na fashe da kuka, ina jin wani irin abu yana taso min, kamar kukan nan saka ni ake yi, har sai da nayi na gaji, tana kallona taci abinci ta koshi, ta mike ta daura ruwan zafi, ta fita tayi wanka sannan ta shirya zuwa gidan Babanta, koda ta je can faɗa yayi mata me yasa zata zo, gari ba lafiya. Hakuri ta bashi tare da mishi zancen ta hadu da wani tana son ta turo shi,ta kira saurayin ta hada su, sukayi magana ta roki Babanta kada ya bari Addah ta sani. Ya mata alƙawarin ba zata sani ba.
***
Karfe biyar ina wurin dabobbi, ina taya Baffa'm tatsar madara. Wayarshi tayi ƙara dauka yayi yana me sallama. " Alhaji Abubakar ko?" "Eh ni ne?" "Okay ko zaka fita kai da wani naka, domin mun samu labarin za a."
"Anan aka haife mu, anan muka girma bamu da inda yafi nan, sai dai mu mutu, Yallabai mun gaya musu, bamu ne muka musu barna ba, taya zamu cigaba da amsar laifin da bana mu ba, a matsayinku na jami'an tsaro hakkinku ne kula da rayuka da dukiyoyin mu."
"Shi kenan, kada kace ban sanar maka ba, na gaya maka gaskiya kuma ba a bamu umarnin kare kowa ba, don Allah ka fita daga cikin Jenuwa."
"Shi kenan!" Baffa'm ya faɗa yana kallona, taya zai fara. Haka ya wuce ni ya saka aka kira mishi sauran mutanen rugar ya gaya musu abin da yaƙe faruwa. Shiru suka yi kafin aka samu wasu tsagera suka kama dariya."Baffayo kana nufin Mu bar rugarmu saboda kada mu mutu? Kusan kai ma kana da shanun nan,don haka babu inda zamu ai wannan maganar karya ce wallahi babu wani! Harin da za a kawo mana, da alamu tsufa ya fara kama baffayo." Kiri-kiri matasan nan suka ƙaryata shi, haka yasa shi komawa gida da tarin takaici da bakinciki.
Koda ya dawo ana kiraye-kirayaen sallar Magariba, a masallaci ma yayi magana dayawa suka karya tashi sai yayi shiru, koda ya dawo bayan isha muna cin abincin, ya shalenta abin yake faruwa a cikin gidan, Babangida ya ce mishi. "Baffa taya zasu kiraka su gaya maka, kawai dai wannan zance ne. "Bai fito ya ƙaryata baffa ba, amma maganarshi sak ce da ta sauran mutanen, ban san me yasa ba ko don a gabana aka yi wayar sai naji zuciyata tayi sanyi, kuma wani irin tsoro da fargaba, ya shige ni Zulaihah ma ta shiga haɗa duk wani abu me muhimmanci akan mu bar garin cikin daren nan, amma wani abin mamaki kana naka, Allah yana nashi, wurin karfe tara na dare, muka dinga jin ƙarar harbe-harbe, hankalin Baffanmu ya tashi, yana shigowa dakinmu ya ce min.."taso Fadimah." Tashi nayi a rikice ya cewa Zulaihah. "Kema tawo!" Dakinshi ya wuce damu," kada ku sake ku fito matukar bani na bude muku kofar ba, da izinin Allah babu abinda zai faru." Ashe ya tafi har dakin Nenne ya kwaso yaranshi, Yar matan nan tace ta adana Yaranta, domin mugun nufinsa ya janyo wannan tashin hankalin,da bai fada ba ai da babu abinda zai faru. Bai mata magana ba ya dawo duk inda ya nime su bude kofar ya kwaso yaran sunki,.haka yasa shi dawowa ya dauki addarshi ya tsaya a kofar gidanmu.
Ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba,domin kuwa kana d'aga kai zaka ga yadda garin yayi jajjur da wuta da hayaki. Baka jin kome sai karar bindigu da kukan dabbobi.