← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 138

Sashe 35

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin ko barci neman gagararta yake, wata irin wahala take sha da kamfanin Mamman Ba'are, gashi yadda ta tsaya ba ƙaramin bunƙasa kamfanin tayi ba, domin idan har kana son gane yadda kamfanin ya cigaba tow ka shiga office dinta, ita da Aryan suke tsara duk wani cigaba dake Allah ya taimaka shi mutum ne mai kwazo kamar Abdul sai gashi ya hada karatu da aikin da yake taya mahaifiyarshi, duk da wannan jigilar bai hana idan ta koma Nana ta sauko ta shiga gaya mata magana marasa dadi ba, ana cewa idan duka yayi yawa na kai ake karewa tow ita Hajiya baki daya da ta ko ina kare dukan take, sannan Yaranta tsayawa tayi akansu, domin idan ba haka tayi ba Yaran so ake a lalata mata rayuwarsu.
A cikin shekaru bakwai din nan, suka tafi bikin gama makarantar Abdul Majid, wanda kana ganinshi kaga babban mutum, sai dai har yau yana nan babu sakewa kamar baya, ga shi nan dai amma yanayinshi zai nuna maka yadda yake jin babu dad'i a cikin mutane. Haka aka gama a hanyarsu ta komawa gida ne, Hajiya ta amshi takardarshi. "First class, Alhaji ka fito da shi amma baka farinciki." Yake yayi ya ce mata. "Ya Amaan yake?" Ajiyar zuciya tayi tana kallon Aryan da Jamilah da kowannensu yayi tsaki. "Yana lafiya." Ta fada tana son ta manta da abinda Amaan din yake mata. "Hammayo yaushe zaka dawo gida?" Shafa kan Anisah yayi yana faɗin. "Zan dawo." "Ka dawo ko Hamma Amaan zai daina saka Hajiya magana, shi ba karatun ba, shi ba aiki yake ba. Sai dai kullum a bashi kuɗi. Hajiya tayi magana har ta gaji "
Bai ce mata kome ba, shi dai ba zai je Nijar ba, wallahi ko a kai za a kai shi ba zai je ba. "Hmm tayi hakuri ta cigaba da addu'a."
"Ba zaka dawo gida ba!" Shiru yayi bai ce mata kome ba, zata kuma Magana Aryan ya ce mata. "Nisah ya isa haka, Hammayo ya gaji." Ya faɗa yana kallon Abdul Majid din, dake su sun iya turanci duk haka suka juya harshen turanci. A hankali Aryan yake tambayarshi me yasa ba zai dawo gida ba.
"Kawai ba kome, zan tafi karatun sanin makaman aiki a Nijeriya ne "
"Amma.". "bana son hayaniya don Allah." Hajiya tasan halin Yaranta, kowa da irin nashi hakurin, amma hakurin Majid daban ne, haka fushinsa daban ne kuma zai iya hakura da kome musamman idan akwai wulakanci da cin mutuncin. Haka suka iso gida, Innarsu kanwar Hajiya wato Kabo wacce aurenta ya mutu take gida dauke da karamar yarta mai suna Zaytoonah. Yarinyar suna shiri sosai da shi, yana shiga ta tare shi da kyaututtuka masu yawan gaske. Tana murmushi ta ce mishi." Hammana ina tayaka murnar kammala karatun ka!"
Amsa yayi yana faɗin. "Na gode dear!" Daga haka suka wuce ta tsaya tana kallon Aryan da yake mata dariya. "Hamma Aryan dariyarka kamar gwalo kake min"
"Tow Allah ya baƙi hakuri, ina Nabeeha?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Ka bani cin hanci dai na kira maka ita."
"Ok idan na shawo miki kan shi fa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Karya kenan domin kuwa zuciyarshi da kiyayya ta ginu, duk macen da zata samu damar kutsa kai cikin zuciyarshi mace mai Sa'a ce, mu shiga ciki zankirata."
Shi kan Aryan tausayinta yake ji, duk da ba bata wuce sha uku ba, yarinyar tana da hankali da nutsuwa, kuma kowa yana musu kwadayin zama ma'aurata, domin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, suna da nutsuwa da hankali uwa uba Ilimi idan Yaro yayi magana ba zaka dauka shi yayi ba, domin an samar mishi nutsuwa tuntuni.
Bayan isha Nabeeha tazo suka sha hira, sannan ya rakata bangarensu, waye zai ce wannan haɗin bai mishi ba? Ai babu kaf gidan domin soyayyar da sukewa Sa'a na musamman ne, shi yasa suka dorawa Abdul Majid wata irin kauna.
Bayan sati suka koma Nijar, suka cigaba da abinda yake gabansu. Shi kuma Abdul ya gama abinda zai yi ya dawo Nijeriya domin a can Nsukka yayi course ɗin shi na likitanci, wani ikon Allah sai gashi ya dace. Ana yaye shi aka tura shi asibitin Malam Aminu Kano, anan ya fara Internship ɗinshi. Yana tsaka da aikin ne aka fara diban sojojin sama. Yayi join amma suka ki amsarshi. Saboda wasu takardun shi, sau uku yana gwadawa amma baya samu karshe sai suka makale a bayan matsalarshi na cewa idan ya shiga damuwa zai iya kawo musu matsala a yanayin mental health din shi. Haka ya hakura da sojan sama, yayi apply na kasa shima ya makara, haka ya hakura wata shekara kamar wanda aka ingiza shi ya cika sojan ruwa, wani ikon Allah yana tura takadunshi, suka yi approved.

Amma a lokacin suka bukaci suga iyayenshi, kamar ba zai je Nijar ba. Amma haka ya tafi wurin Alhaji Abubakar Abzin, ya gaya mishi. Shiru yayi sannan ya ce mishi. "Dole Mamman ya tsaya maka." "A'a ni bana bukatar taimakon shi, kawai kai ai ka wadatar."
"A'a dole ya ga matsayin da ka taka, duk da nasan wata rana haka zai faru dole a bashi matsayinshi na uba."
Haka Alhaji Abubakar Abzin ya tawo har Niamey, ya gayawa Alhaji Mamman Ba'are abinda yake faruwa. "Amma har na kusan gama.aikin asibitin yaron nan zai dauko wani zance?" Ya fada a harzuke, wai ma girma ya cimma shi. "Baka da iko akan karatun shi, lokacin da nake gaya maka ka janyo danka a jiki ki kayi, yanzu kuwa ya tsaya da kafaffunshi kace ya dawo jikinka, shi wancan da kake hidima dashi har yau babu cigaba jikinka ne?" Shiru yayi, Alhaji Abubakar Abzin ya mishi tass, haka yasa bayan kwanaki ya tawo har kano shi da Hajiya, duk yadda Hajiya taso ta janyo ra'ayinshi ya dawo ga asibiti ki yayi ya ce mata. "Babu dukiyata a cikin asibitin, ni nawa zan nima don Allah ki kyale ni na cika mafarkina." Alhaji Mamman Ba'are yana jin shi, amma bai ce kome ba dukiyarshi ce wato Majid yake kyama? Wani irin kuskure yayi ne haka? Lallai Majid shine magajin GOLDEN EMPIRES, shi daya zai rike da zuciya daya domin babu buri ko kwadayi a ranshi.
"Zan biya ka miliyan goma duk wata kazo ka taya mahaifiyarka aiki." Juyawa yayi ya kalli Alhaji Mamman Ba'are, ya saki murmushi ya ce mishi. "A'a bana bukata na gode."
"Abdul Majid ka manta da kome, ka dawo zan bar maka kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES " juyar da kai yayi yana murmushi. "Da kake gabar mutuwa ko? Hmmm wallahi idan na cire ahalina mahaifiyata da yan uwana har duniya ta nad'e bana fatan had'a alaka da dukiyarka, rayuwarka ka saka ka nimo dukiyarka nima rayuwata zan saka na nimo tawa. Hajiya ki gayawa Mijinki ya daina shiga rayuwata." Daga haka ya mike, ya nufi can wurin da aka saka water dispenser, ya dibi ruwan ya sha, sannan akan lokacin aka ce su shiga, koda suka shiga cikin dakin. Suka tattauna a lokacin da ake gaya musu sharudan aikin da sauransu, sannan sunan da yake jikin takardunshi yasa masu daukar sojoji a matakin farko yasa yake son ganin da gaske ne shi ɗin, family mahukuntan kasar nijar ne. Takaici yasa Majid cewa. "Sir ban nemi aiki a matsayin dan Mamman Ba'are ba, na nima ne a matsayina na dan Nijeriya kuma farar hula, bani da alaka da nijar." Juyawa hajiya tayi ta rufe mishi baki. "Me yasa baka jin magana ne?" Kwafa yayi cikin fushi ya ce. "Na fasa aikin ma." Ya juya zai fita, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mishi. "Asibiti ko kamfani ina zaka yi aiki da su." A fusace ya juya zai magana Hajiya ta tsinke shi da mari, rike kunci yayi yana kallonta. "Wannan rayuwarka ce, va zan maka dole ka san daidai ba, amma ba zan matsa maka kayi aiki a ko daya daga cikin kamfanin Ba'are ba, ka tsaya akan ra'ayinka anji kai jinin ba'are ne, so what? Duniyarka zaka gina sai kayi fushi da damarka? Waye kai? Oya wuce kayi sign kai ba bawa bane, mutum ne mai ra'ayin kanshi don haka ka tafi aikinka Allah ya baka sa'a."
Haka yasa shi amsar kome cikin dadin rai, Hajiya tana tare da shi bayan sun fito, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mata. "kin nuna min bani da iko da d'ana kenan?"
"Me yasa lokacin da yake bukatarka baka damu da shi ba? Sai yanzu da kasan iya shi zai iya rike sauran abubuwanka. Nima ajiye maka aikinka zan yi na gaji zan koma wurin dangina."
A matukar tsorace yake kallonta, bayan Majid ya fito. "Kina nufin zaki juya min baya kenan?" "Hajiya muje!" Uffan bata ce mishi ba, haka suka tafi gidan da yake haya shi kuma Alhaji Mamman Ba'are ya wuce hotel, tunda ya isa can ya fadi rike da gefen kirjinshi, a kayanshi aka samu passport dinshi da hoton Majid da wasu abubuwan, haka aka wuce da shi asibiti. Sannan a nan suka shiga niman Abdul Majid a cikin asibitin, dakyar duka samo shi, koda ya zo kanshi bai wani girgiza ba, kawai dai ya tsaya duba wasu daga cikin tests din da aka bashi, anan suka yi magana da daya daga cikin likitocin. Ya ce mishi."Doctor kasan ya auna arziki?" Sosa kanshi yayi yana kallon Likita. "Ban gane ba?" "Hmm guba ne a cikin jininshi, wanda yayi yawan da." "Bar zancen haka, Allah ya bashi lafiya." Daga haka yaki yarda ya amince da sauran bayanan amma tabbas yasan abin da Alhaji Mamman Ba'are ya shuka shi ne zai girba. Ya je har gidan shi ya tawo da Hajiya ko ita bai yarda ya gaya mata ba, sai a bakin likitan taji. Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Tow Yaranta da suke can waye zai kare mata su. "kina tunanin su Anisah da Jamilah ko? Ai su ba za a musu kome ba, koda za'a yi sai don a kuntatta miki ta hanyar niman wani abu, amma ba wai don tab'a ki ba." Kwanan shi uku aka sallame shi, suka wuce nijar.
Chapter 35 · 0% Book details