← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 138

Sashe 84

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nana kin ga abin da yasa nace miki bana son kina gayawa Zaytoonah magana ko? " Ya faɗa ranshi a b'ace. Ita kanta Nana jikinta yayi sanyi, domin bata taɓa kawowa yarinyar zata mata rashin kunya haka ba, sai gashi ta silleta tass sannan ta fita wani irin kunya ne ya kama Nana ta mike dakyar da sandarta ta nufi waje. A kasa ta taraddasu Aryan suna hiranru. Kamar munafuka haka ta bar gidan. Babu wanda ya damu da hakan, tana fita sai ga Zaytoonah da akwatinta dauke da goyon Yarta. "Ke ina zaki?" Inji Aryan, "Zan koma Kamaru ne akwai wani abu ne?" Ta fada a fusace. Saukowa yayi yana, mika mata hannu tayi banza da shi, bayanta ya je ya amshi goyan Mimi. "Ki tafi gaba da Kamaru if you want, babu me dakatar dake kin ji ko." Jan akwatin tayi kiiiiiii, "da dai kinyi hakuri Nana ba fasa halinta zata yi ba, kamar yadda take da baki kema sai ki koyawa kanki kwatar kanki ba ta rashin kunya ba, ban ji dadin yadda kika gaya mata magana ba, ko babu kome kakarmu ce. Idan da akwai wanda yafi wahala da Nana Majid ne, kuma har yau shi yake ɗaukar wahalarta da fitinarta, kin ga ko Yaranta ta damu da su?" "Amaan kyaleta don Allah ta tafi." Inji Aryan da yake cike da takaici. "Matar nan ba don ina da hakuri ba, da babu dalilin da zai saka na kyaleta cewa tayi duk abinda ya faru ni ne nake kokarin kashe yan uwana, waye zai ji wannan abin bai zarge ni ba, gara ki hakura idan tayi miki babu rashin." Make kanshi Hajiya tayi, ta bi na Amaan ta make. Ita kan Mimi ta ga Babanta sai ta kwanta luff a kirjinshi. "Ku da zaku mata fadar rashin kunyar da tayi, shine kuke gaya mata yadda zata ji da Nana?" "Kyale su Hajiya na!" Inji Majid yana amsar akwatinta ya wuce dakinta da shi. "Ki bishi ku daidai ta kanku." Cikin kuka da bori ta zauna a falon tana kuka, can ta mike ta nufi dakin. "Wai da Yaji zaki yi?" Share shi tayi zata wuce ya ce mata. "Nana kakata, ke kanwata ce ina son ki fahimci wani abu, ni Abdul Majid ban ajiye ki don ina sonki ba, ke kanwata ce idan kika samu wanda ya fini ki aure shi." A gigice ta juya tana kallonshi....... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 +2347035133148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB243 Kura mishi idanu tayi kuka ya kwace mata, tana kallonshi. "Hammayo da kaunarka na taso, na kasa zama da Baban Mimi ne don ina kaunarka. " "Kiyi hakuri!" Ya furta a hankali, sannan ya ajiye mata Mimi. "Tun fil azal babu wannan batun a raina, amatsayin kanwata na dauke ki idan nace zan yi shiru kamar yaudararki nayi, Ni bana cikin jerin mazajen da zasu yaudari mace, sannan idan na yaudareki meye ribata? Ban tab'a kaunarki da aure ba, soyayyar zumunci da kasancewarki kanwata kuma abokiyata nake yi maki." "Hamma Abdul ina sonka." Zauna da ita yayi tare da durkusawa a gabanta. "Ni ban ce bana sonki ba, kaunar aure ne bana yi miki, ni na gaya miki gaskiya tsakanina da Ubangijin da ya halicce ni." "Hammayo." "Shiiii! Na gaya miki gaskiya." Kura mishi idanu tayi tana faɗin. "Ina sonka." Miƙewa yayi ya bar dakin. "Kiyi duk yadda kike so, amma Allah ya gani my heart belong to someone." Ya faɗa mata cikin kwarin gwiwa da yarda da kanshi. Eh gaskiya ne zuciyarshi mallakar wata ce, ba ita ba. A da yayi kokarin tsayawa akan lalurar shi, ba tare da ya yarda cewa zuciyarshi wata yake jira ba, amma a shekara daya zuwa biyu ya yarda zuciyarshi wata take jira, sannan bai taɓa kawowa a ranshi yana jiran wata ba ce, sai wannan lokacin da duk yadda ya hadu da mata a wurin mu'amalar kasuwanci, da sauransu. Amma jiya yaji wani irin al'amari me karfin gaske. Wucewa yayi ita kuma Zaytoonah ta fito da gudu zuwa wurin Hajiya. Tana kuka tare da rike hannunta. "Ummati wai Hammayo yana da wacce yake so, Ummati ya ce min zuciyarshi mallakar wata mace ce. Ummati saboda shi nake raye, don Allah Ummati ni ko a Kwarkwarah ne ya aure ni." Ta fada tana zubewa a kasa, tare da rusa kuka kamar ranta zai fita. "Tow ki mutu kawai muci gumba idan yaso sai ki zama fatalwa ki addabi rayuwar yarinyar da yake so. Wai ma tsaya Majid ne ya gaya miki yana son wata?" Ya faɗa yana bushewa da dariya, "Hajiya gaskiya danki ya girma ayiriri Dan Majid zai yi aure, kara faɗa breaker ya kusa aure kara faɗa breaker ya kusa aure." Takaici ne ya ishi Hajiya ta maka mishi ludayin miya. "Kai dai kayi girman kawai." Dariya yayi ya nufi dakinshi yayi wanka ya shirya cikin danye boyel, ya fito ya nufi kitchen ya dauki basket din abinci ya fito da sauri, domin dukkansu mota daya suke fita da shi, tunda suka yi hatsarin nan. Ga Jamilah har ta haifi d'anta namiji da ta sakawa Amaan takwara suna kiranshi da Ajwaad. Aryan ya rigasu fitowa sai shi Amaan da basket."yaushe ka koma dan makaranta?" Aryan ya tambaye shi cikin zolaya. "A'a ni bokon ne bakiɗaya." "Allah ya huci zuciyar Imam Aliyu." A fusace Amaan ya ce mishi. "Bana son iskanci, yau kuma da renin hankali ka tashi." "Ni ba dan iska ba ne." Ya faɗa yana dariya. Fitowar Majid fuskar nan a haɗe kamar hadari dan watan Agusta. Ya wuce gaban motar ya zauna Amaan ya shiga baya, Aryan ya koma gefen mai zaman banza ya zauna. Da wani uban gudu ya ja motar suka bar gidan, yana tuki yana tsaki har suka iso kamfanin, sauka Amaan yayi yana dariya. Ciki ya wuce tare da bude wayarshi yana dubawa. Fara'ar fuskarshi.ce ta dauke. A hankali ya mai da wayar aljuhun wandonshi, bai kuma dubawa Asalima farincikin da yake yi ya dauke, haka ya wuce office ɗin, musamman bangarensu, yana shiga ya hangota tsaye tana tsaye. "Kanwata!" Juyawa nayi ina kallon shi fuskarshi babu walwala. Murmushi nayi mishi."Ina kwana Ya Amaan." Lafiya lau, ya bakunta?" "Alhamdulillahi!" Ya mika min kwandon abincin. " "Baka gajiya ne da dawainiyya?" Na fada ina kallonshi. Zama yayi yana faɗin. "da fatan kin huce gajiyar jiya." Ya faɗa yana kauda wancan maganar da tayi. "Alhamdulillahi!" "Akwai laptop na kamfanin nan, an jima za a baki naki da tap." "Na gode!" "Sannan ga wannan takardun ki duba kudadden da kamfani ta ke kashewa ne, a duk wata, ban sani ba ko kina da abin da zaki iya a matsayinki na daliban tattalin arziki." Amsa nayi ina me cewa. "In sha Allah zan duba." Na amsa, ina dubawa tare da kallonshi kamar baya cikin nutsuwa. "Ya Amaan akwai wani abu ne?" "A'a, ina abubuwan da na tambaye ki?" Bude jakar da nake yawo da shi nayi, don na makarantar ne, na cire takardun na mika mishi. "Wai wayarki lalacewa tayi ne?" "Hmm! Yarinya ce ta saka a ruwa." Na fada kamar bana son magana. Don ina tsoron kada ya dauka ni mutuniyar banza ce, don duk wanda nace ina da yarinya kallon ta ina na same ta ake fara min. "Kin barta a wurin su Umminki ne?" Gyada kai nayi, ina faɗin. "Eh!" "Amma ya kamata ki kawo ta kusa dake, yau kunyi waya kuwa?" "A'a" na faɗa ina duba takardun da ya bani. "Tow gashi nan ki kirasu, sai ki karya bari naje Office din Majid." Ya ajiye min wayar ya fita, yana futa ko minti daya bai ba, aka turo mishi sako, daidai xan yi kiran kenan. *Ka turo min da Cefa miliyan goma, ko kuma na saki videon da na tura maka.* Sake shigowa videon yayi kamar wacce aka saka na bude nayi Clicking kan videon, wani irin zabura nayi tare da sake wayar a kasa. Da sauri na bi wayar na kashe videon. Jikina yana rawa na ajiye mishi wayarshi na koma kan aikina, wani irin kyamarshi nake ji, abincin da ya kawo min ko kallo basu ishe ni ba, domin hoton fuskar shi baro-baro. Jikina ya dauki rawa hala shi yasa yake rawan jiki a kaina. Haka na tattara takardun da ya bani na bar office, ina futa na fara amai. Sai da nayi sosai, sannan na tafi can karkashin bishiya na zauna ina sauke numfashi. ........ Wunin ranar aiki kawai na nazarin ayyukan kamfaninsu nake, koda aka tashi kin yarda mu hadu nayi da wuri na koma gida, na ajiye mishi yar karamar short not nace mishi. *Allah ya saka da alkhairi, kayi hakuri cikina yana ciwo ban ci kome ba, wayar ma na barta cikin basket din* ........... A lokacin da ya ga sakona, jikinshi har rawa yake, ya dauki abincin ya kaiwa masu tsaron kamfanin. Kamar mara lafiya haka ya dawo gida, abincin dare bai ci ba. Washi gari ma haka yasa aka yi abinci amma wani ikon Allah koda ya isa yau bai ganta ba, abin ya dame shi ko itama wani ya gaya mata waye shi ne? Baya alaka da kowa a kamfanin sai yan uwanshi, haka yasa kowa yake shakkar mishi wani abu, domin Majid da Aryan ba zasu kyale ka ba.. Haka kawai tunda na saka kaina nazarin abin da suke, sai na yanke alaƙar haduwarmu, haka yasa naji sauki sai dai inda gizo ke saka, dayawan ma'aikatan kamfanin nasu shiga harka na, wasu ma wani irin kallo suke min, wato irin ga yar iskan nan. Wannan abin ya min ciwo haka yasa nake lallaba rayuwata, sati na zagayowa na tafi Marad'i ranar Asabar ranar Lahadi da yamma muka dawo, abin mamaki a bakin kofar dakina na same shi, fuskarshi tayi wani irin fari. A dan razane na kalle shi. "Kin ga videon ko?" Ya tambaye ni, hawaye na zuba a Idanunshi. "A'a ni ban ga kome ba" "baby zo nan!" Da sauri ta isa gare shi, ya d'auketa. Sannan ya matsa min na bude kofar, shiga dakin yayi nima na shiga tare da barin kofar a bude. "Ya sunanki?" "Amira" ta faɗa, zama nayi na wuce kitchen. Shi kuma ya juya ya fita da ita can ba jimawa sai
Chapter 84 · 0% Book details