← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 138

Sashe 123

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan dawo anjima Baby me zaki bani?" Murmushi nayi mishi nace . "Ka dawo da wuri don zan baka dadi ni dumi nake so, sanyi ya dame ni!" Kallona yayi ga rigar sanyi har da nashi, ga safar hannu ga ta kafa. Kaina lullube da mayafin abaya. "Ok Nur zan mana booking din masauki." "Yawwa katona ni da Nana da Hajiya."
Dariya yayi yana jan hancina, mikewa nayi na sumbaci bakinshi, rike harshena yayi mun jima har aka fara yayyafi, ya sake ni ya fita. Dakin na koma muka kara gaisawa, sai niman bargo nake. "Munai! Bani bargon can,.kunna min room heater." Na shige cikin bargon sama-sama muka gaisa dasu, jin dumi yasa barci yayi gaba da ni.
"Yau ga ni ga Zahrah ga Ummi, ina Zuzu?" Cikin barci na bude idanu. "Ku kira shegiya tayi aure ai."
"Haba?"
"Bata gaya muku ba ne? Sati Uku kenan anyi auren da sati daya muka tawo gembu satin mu biyu kenan muka zo nan"
Ai kuwa suka fara magana. "Ku cewa shegiya ta tawo min da yarinyata ba xan bar mata ba." Barci yayi gaba dani, Munaisah zata kuma magana Nenne ta ce mata. "Barta tayi barci, Allah ya bata lafiya ya raba lafiya." Ita tun da taga ta Shigo tana niman wurin dumi, ta fahimci shigar ciki ne, domin haka Aminatu tayi lokacin cikin da suka korata da shi, tayi ta bin hantsi da duk inda aka hura wuta, ko ta shige dakin Malam wato Baffa'm, idan kuma ta shige ɗakinta har wuta take kaiwa, tayi ta niman bargo tana rufawa da shi.
Hawaye ne ya zubo mata, waya Ummi ta dauka ta kira Zuzu sama sama suka gaisa don tunda ta bar gidan zumuncin ya yanke....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB268
"Dama Zahra ce ta ce na gaya miki, sun zo amma tana barci kamar bata jin dadi ne, idan da hali Kizo mata da Princess."
"In sha Allah!" Ta kashe wayar, tana kallon Munaisah. "Abin gwanin ban sha'awa, dukkanmu mun haɗu. Don Allah Nenne ku roka min Zulaihah ta yafe min na cutar da ita gashi Allah da yaga zuciyarta har anyi aurenta da Baban Aamirah."
Kukanta ya tashe ni, na tashi zaune ina jan bargo. "Sadiq dan Babangida ya shigo min da wasu manyan ledoji shi da wasu Yara, bude jakar nayi naga kayan kwadayi ne.
*I forgot to tell you I love you, and now a said I love you*
Murmushi nayi na bude ɗaya ledar me zafi. Roasted chicken ne.
"Ki ci sosai, ina sonki." Ya rubuta a jikin takardar.
Bude Jakata nayi na dauki yar karamar memo na rubuta mishi.
"Ina sonka sosai, Allah ya tashe ka cikin Asahabul kahfi "
Da gudu yaran suka fita.
"Wannan shiririnta fa?"
Kaji uku ne a ciki na mika musu biyu da rabi, na dauki rabi, yaran da suka kawo aka basu, sai da naci na koshi sannan nayi sallolin da ke kaina na kuma kwanciya sai barci.
"Allah ya hada Zahra da aiki!"
Wurin shida da rabi Zuzu ta shigo, dake ana ruwa. "Barci har ana kiran sallah." Tashi nayi na kalli Aamirah ta sha kyau ga kibar da tayi. Tashi nayi na bude mata hannu, ta shiga da sauri har tana tuntube. "I miss you Mami!" Rungume ta nayi ina faɗin. "Me too love!" Mikawa Zuzu hannu nayi, ina fadin. "Annurin amarci ba wasa ba."
"Kema kin ga yadda kika yi kiba?"
"Hmmm ina kiba anan" na mike tare da nufar waje nayi Alola na dawo dakin nayi sallah, itama ta gaya min tayi sallah a gida. Abinci ta kawo mana, tuwon semo miyar kuka ya ji kayan kamshi ga nama. Ga pepper meat da tayi. Sai manshanun.

"Sannu zuzu!" Dibawa mijina nayi, na karbi wayarta na saka number shi naga ta saka Abban Aamirah, kira daya ya dauka. "Auntyn Aamirah!"
"A'a Uwar Amirah ce, ga abinci kazo kaci kada ya huce."
"Tow uwar Aamirah da sauran yara!"
Haka yazo na kai har falon yaya Babangida na ajiye ya zauna muka ci tare, shiga jikinshi nayi ina faɗin. "Sanyi nake ji!"
"Muje ma sauki!"
"Idan muka gama hira sai mu ajiye Zuzu, mu wuce masaukin ko?"
"Duk yadda kika ce matar kirki"
Sumbatar bakinshi nayi, shi kuma ya rungume ni dakyar muka rabu. Ya tafi ni kuma na kwashe kayan, na koma wurinsu.aka bude shafin hira kamar me, duk wannan hirar ta rayuwar baya ce babu wanda ya sako Addah, domin mutunta Zuzu. Itama bata da yadda ta iya da Mahaifiyarta kuma bata da wacce ta fita. Haka muka yi ta hira har sha biyu saura aka zo kiranmu, haka muka fita ina dauke da Aamirah.

A motar na kwantar da ita, ya kai su har gida, na shiga naga Addah tana barci. "Zan tafi amma gobe anan zamu wuni."
"Na gode sosai Zahra!"
Murmushi nayi muka fita, ta rako mu, wato dakyar muka isa dakinmu domin daukata yayi yana faɗin. "Yau nasan kin gaji muje nayi miki tausa." "Sauke ni na shiga da kafata ." "A'a muje dai na kai ki!" "Aishi kenan!" Na fada ina lumshe idanuna. A daren dai a gajiye nake, amma labarin daren me tsayawa a rai ne, domin barcin mu ƙalilan ne. Sai goshin asuba muka yi barci. Bamu tashi ba sai karfe goma domin mun makara, haka muka yi sallah a kurarren lokaci. Duk jikina ciwo yake duk da yau na ce zan fita amma dumin dakin ya hanani fita ko waje. Haka yasa shima makale min tunda na karya, sai naji dakin yana bani wani irin yanayi na musamman gashi ga dumin dakin, duk ya haukata min lissafi. Bamu bar masaukin ba sai karfe biyu na rana, ya kai ni gidan Zuzu. Yaga Addah a zaune an daura ta a kan wheelchair, an saka mata belt ya riƙe ta.

Kunyar Zuzu yasa shi bai ce mata kome ba. haka ya tafi ya bar mu muka sha hira wurin karfe uku sai ga Ummi da Munaisah. "Jar Uban can, gidan nan ya min!" Inji Munaisah tana bin ko ina da Zuzu ta zuba interior design masu kyau, "amma kayan nan akwai Turkiyya ko?"
"Eh uwar dakina, amma bani na saya ba, Hamma ya turo min,.kayan kitchen Mama daga doula ta aiko min kamar naki, lokacin da muke sayayya naga kome biyu take saya, ashe nawa ne. Ki shiga har kitchen din wasu na zuba su a can gidanshi na Yola domin gado biyu yayi min daya nasaka anan, daya nace akai cen kuma na rigada na saka kayan kitchen din da na saya shine nace a kai min can Yola."
Yadda take maganar sai take karya min zuciya. "Zahra na gode!"
"Allah ya shirya min ke!" Haka muka yi ta hira anan zuzu take bamu labarin Zahra yarta. Rike baki nayi na zuba mata dundun makafi a bayanta. "Wallahi ba zaki bar mishi ba, dole a dauko mana ita."
Murmushi me ciwo tayi tana faɗin. "ba zai bani ba, sai dai idan zan aure shi. Ni kuma bana son aurenshi ina son nayi auren a cikin dangina yan uwa da abokan arziki."

Haka muka ta jajantawa juna, kafin muka dawo case din Zuzu da Ummi, dakyar muka shawo kan Zuzu ta yafe mata, muka ci gaba da hirar mu sallah ke d'aga mu nice nayi abincin dare muka ci muka gyara dakin Addah wacce bakinta yake karkace ta ce min "Allah ya tsine miki albarka, la'annniya munafuka,. Kin saka yaran da suke samo min kuɗi sun daina, karshenki ba zai yi kyau ba."
"Ayya Aaddah karshe me kyau gata har da cikin dan Sunnah." Dafe cikin nayi ina kallon Munaisah, "Yes ciki ne dake, sabo ma don Allah wannan turmusan a rage domin suna har nijar, zamu je ina dalili. Dan albarka kenan. Idan namiji ne Mamman Ba'are za a saka mishi ko? Idan mace ce Aunty Aminah za a samu!" Kunya ce ta sani fita daga dakin.
Haka na zama kamar munafuka can nace musu. "Kai saura kwana uku nayi period!"
"Ko maita kika ci wallahi baki period din nan sai kin haifi Mamman Abdul Majid Mamman Ba'are!" Inji Ummi, suka yi ta cakalata da magana kunya ta hanani magana. Haka yazo ya dauke ni da zamu tafi Munaisah bata da mutumci. "Mr Mamman Ba'are, ayi hakuri da wasan d'aga kafa, kada garin zungura a zunguro min Little Mamman Ba'are." Kifa kaina nayi ina faɗin. "Yarinyar nan ta zama bayahudiya."
"Tow Miss Buba takum, za a kiyaye." Har muka isa sai kallona yaƙe har muka shiga daki yau ma hanani tafiya yayi, da dare kuwa lallabani yayi, akayi kome a takaice. Bayan ya huta ya ce min. "Idan har cikin ne tow zan kai ki Kamaru ina tsoron kada tashin hankalin gidan Mamman Ba'are ya shafi uwa da cikinta."
"Kyalesu karya suke babu ciki!" Na fada ina shigewa jikinshi saboda sanyin da kafafuwa ta sukayi. Nan muka sake bude wata sharholiyar.

Haka muka kwana, da safe na tashi da morning sick. Sai da ya saka min drip, domin zazzaɓi ne har da amai. Fita yayi ya sayo kayan magani ya saka min drip, sai wurin karfe biyu na farka, tunda na tashi nayi sallah, sannan na koma na kwanta. Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un ashe haka laulayi yaƙe? Bawan Allahn nan haka yayi ta rawar kafa a kaina, ya kira Hajiya ya gaya mata, ta ce ya mai dani gida, kwana uku aka mai dani gida wurin Hajiya.
Chapter 123 · 0% Book details