← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 138

Sashe 36

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka koma jikin Alhaji Mamman Ba'are ya ki,asalima jinya ya kwanta inda aka kwantar da shi asibitin da ya ginawa Majid a can yake kwance. A hankali jinya tayi jinya domin ya kai sama da shekaru biyu a kwance, har wannan lokacin bakin shi bai daina kiran Majid ba, yazo ya yafe mishi. Dakyar Hajiya ta samo shi A Lagos yazo ya ganshi a ranar da yazo yake gayawa Lauyan shi. "Kuri'ata na barwa Abdul Majid Mamman Ba'are, akwai wasu kamfanoni na guda uku da asibiti duk da sunan Majid Mamman Ba'are na ajiye su, lauya ka rubuta a matsayin wasiyyar da na bari, Abdul Majid Mamman Ba'are, ka yafe min." Dauke kai yayi yana latsa wayarshi ya ce mishi. "ai ban kullace ka ba, don haka Allah ya baka lafiya " daga wannan ranar Majid ya bar Nijar dama kwana uku aka bashi, ya bar musu kome nasu kai ko ruwan gidansu baya sha, sannan ya gayawa Hajiya matukar ba ita zata yi girki ba, kada ta sake Yaran su ci abinci daga wani waje don kashe su za ayi.

Daga lagos tura shi cotonou aka yi, a lokacin jikin Alhaji Mamman Ba'are ya kara rikicewa sannan ana ta nimanshi, a lokacin yana can teku Hajiya tayi sintiri ya kai sau uku. Babu labarinshi. Bata jima da dawowa ba, Allah ya amshi rayuwar Alhaji Mamman Ba'are, ya rasu ya bar wani irin tukekken rikici, domin bayan rasuwarsa, yan uwanshi da Hajiya Tani suka ce da kason su a cikin dukiyarshi.. sannan wasu suna jin haushin Majid domin gani suke saboda son da Alhaji Mamman Ba'are yake mishi ya mutu domin an ki fadar asalin abin da ya kashe Mamman Ba'are.

Ana cikin wannan tashin hankalin har aka kai shi makwancinsa ana rikici. Bayan anyi Addu'ar bakwai sannan aka fara batun gado, domin sai da aka kira Alhaji Abubakar Abzin, sannan aka fara rabon matanshi da suka mishi takaba aka ware musu nasu, sannan aka koma kan Yaranshi mata da maza aka raba, wasa wasa sai ga Hajiya ta tashi da wani irin kaso saboda ita Yaranta maza ne, sai Hajiya Rabi da itama ta samu ba laifi amma ina gani ake kamar da gayya aka tulawa Hajiya Sa'adatu.

A hankali Lauya ya fitar da kuri'ar kowa ya bashi, da sunanshi sannan ya cire na Alhaji Mamman Ba'are ya ajiye a gabansu. Wannan na Abdul Majid Mamman Abdul Majid ba'are ne, har aka gama raba kome ba a kira sunan Tani ba, nan tayi tsalle ta ce musu. "Shi Sajjid bai da kaso ne?" "Saurin me kike? Akwai kamfanin da take shigo da man fetur kasar nan, ita ce Alhaji Mamman ba'are ya bashi gashi nan." Ya tura mata. "Ban gane ba asibiti da mattan man fetur da ya gina fa?"
"Mallakar Majid Mamman Ba'are ne?" Sakin baki tayi tana kallon kowa. "Sajjid shima fa jinin shi ne." "Ta ina ya zama jininsa? Mamman Ba'are yana da yara talatin da biyar, biyar din kai sune Yaran Sa'adatu, sauran ashirin Yaran, Rabi, Fauziya, Harirah. Yaran rabi goma sha daya, Hajiya Fauziya goma sha biyu, ashirin da uku sun tafi, Yaran Harirah bakwai da dan karami auta. Lissafi ya fito?"
"Eh!"
"Tow bamu ji labarin ya kuma aure ba, domin ko Sa'adatu da ya aureta ya faɗa ke kuma a ina kuka yi auren?"
"Bai gaya muku Ni dadiron shi ba ne?"
"Eh koma meye Muslunci ba zata bawa danki gadon shi ba, domin duk wanda suka ci gado ya halatta a gare su."
"Ban gane ba?"
"Su aure ya basu uba, ke kuma dadiro kuka yi aka same shi, ba dan shi ba ne danki ne ke ɗaya "
Wani irin abu taji ya dake ta, tun daga ranar ta hana kanta sukuni ta saka masifa da bala'i a ranta, ta hada kai da wannan ta hada kai da wannan burinsu ace za a sake raba gadon, sannan har bincikan jini sai da taso a ciro gawar Alhaji Mamman Ba'are ayi domin a halatta Sajjid Mamman Ba'are akan dan shi ne Amma abu yaci tura. Don haka ta samu mutanen gidan ta basu shawarar saka hannun jari a kamfanin idan kudinsu yafi na Hajiya da Yaranta yawa, sai su kwace kamfanin. Haka aka yi har Nana da take kan gangara ta zuba hannun jarinta.dukda dai tsufa ba shine mutuwa ba.

Dake ana bada na Abdul Majid Hajiya ta zuba nashi bakiɗaya, sannan kamfanin sa biyu ana aiki ana tura kuɗin, asibiti ma haka, duk bayan wata sai ayi rigima a board meeting. Dakyar ake shayo kan rigimar, bayan shekara daya da rasuwa Alhaji Mamman Ba'are Aryan yayi aure ya auro Nabeeha, aka sha biki a lokacin Nana ta ce kada Hajiya ta kuma shiga harkar jikokinta har ta yanke hukunci bata gaya mata ba, ita da aka ciyo a caca. Dake sun san Aryan bai da kunya, tass yaje har sama wurin Nana yace mata. "Hammayo bai wurgo ki ba, wallahi kika kuma shiga harkarmu sai na turo ki daga sama." Ya janyota har bakin matakalar. "Sake ni mara mutunci, idan kace na fita Harkar uwarka zan fita ba sai ka kashe ni ba." Tun daga lokacin suka samu salama.
***
Bayan shekaru biyu da rasuwar Alhaji Mamman Ba'are, kamar wanda aka mishi kiranye, kuma ai kusan haka ne domin Hajiya ta hana idanunta barci akan Yaranta. Addu'a ba dare ba rana ga kome ta samu amma kuma kan Yaranta a watse, sannan a wannan lokacin ita ce me yara kanana, sannan tana cikin wani irin tashin hankali Sajjid ya saka Anisah a gaba. Ta rasa me yake nufi da ita, tayi mishi magana ya ce ta sa a dakatar da shi, da ta gayawa Amaan budar bakinshi ya ce mata. "Hajiya ki saka idanu akan Yaranki mata, kada kina can kina niman kudi da barci wasu su lalata musu rayuwa " sai da ta shiga tsakaninsu domin dambe suka so yi da Aryan abin ya mishi ciwo.
Wata laraba kwatsam sai ga Majid, lokacin Sajjid ya biyo Anisah wacce ta fito wanka daga ita sai towel, tana ihun niman ceto sai dariya ake mata, shi kuma da abokanshi sai ihu suke. Ranar da kayan shi na aiki ya shigo yaga yadda Sajjid yake kokarin jan towel din. Jan get din gidan yayi ya rufe, sannan ya dauki wani dutse ya jefi Sajjid din sai da ya fadi can gefe. Juyawa tayi ta hango Hammayo, da gudu ta rike towel din ta nufe shi. Rungumeta yayi yana faɗin. "ya isa haka." Ya janye ta, tare da cire rigar jikinshi na kakin soja ya saka mata.
"Wuce part din Hajiya!" A tsorace ta wuce, wato ba zaka san soja wala imani ba, sai da bawan Allah nan ya rufe idanu yayi ta zane su da duk abinda ya zo hannunshi. Ya kwabe Sajjid zigidir ya mishi dukar kawo wuka, Hajiya Tani zubewa tayi tana faɗin. "Idan ka kyale shi wallahi ba zai kuma kulata ba."
"Tani ni bana son ya daina kulata, don Allah ya kulata ni zan kula da lamarinshi."
"Nana ki bashi hakuri don Allah ya yafe mishi ba zai kuma ba." Wato dukar da Majid yayiwa Sajjid yasa baki daya kowa ya shafawa kanshi ruwan sanyi, domin Hajiya ta haifi zaki, shima kuma Sajjid ko ba a ce mishi ya fita harkarta ba, ba zai kuma shiga harkar nata ba. Don haka ya rufawa kanshi asiri bayan ya kyale shi, ya koma part dinsu, ya same ta ta saka kaya. Tana takure a wuri guda sai kuka take. "Me yasa baki tafi makaranta ba?"
"Bani da lafiya ne!"
"Kina da saurayi?" Gyada kai tayi, "Jamilah fa?" Tana da shi." "Kice mishi yazo ya samu Alhaji ayi magana" domin bai san Alhaji ya rasu ba, kuka ta kara sosai sannan ta gaya masa Alhaji ya rasu ana niman shekaru uku kenan. Jikin shi yayi sanyi. Amma kuma sai bai nuna ba, sakata yayi a gaba suka tafi kamfanin, a can suka bude farinciki, bai gayawa Hajiya kome ba domin ya gargad'eta kada ta faɗa.

Daga kamfani gida suka dawo da ake gaya masa abubuwan da aka bar mishi. "Ni dai na yafe dukiyar Mamman Ba'are"
"Baka isa ba!" Haka suka dawo gidan. Kallon gidan yayi sannan ya cewa Aryan. "Gidan a warewa kowa wurinshi baka san me wani yake yi ba haka zai saka kowa ya zauna lafiya babu saka ido ko cin zarafi. A cikin dukiyar da ya bari a ware part din hajiya a zagaye shi ina son ayi aikin nan da kwanaki arba'in."
"Tow ina Hajiyar zata?"
"Zata wuce garinsu, hutu na samu na wata biyu, don haka tafiya zamu yi sannan ka samu me niman Jamilah da Aneesah, su nufi Agadaz, su nime aurensu."
A gaban Hajiya aka yi kome, wani abu da Hajiya tayi ta karawa kanta kima shine, dangin Alhaji Mamman Ba'are, bata yarda ta ki su ba, binsu take har inda suke take takai har Hajiya Latifah mahaifiyar Mohan(Bororoji) tana zumunci da ita, sannan yana zuwa wurin Hajiya Umamata mahaifiyar Khalil Dan Ba'are,. Haka yasa suka tura su wurin Ibrahim Dan Ba'are, mahaifin Khalil Dan Ba'are.

Bayan masu niman auren sun gabatar da kome daga can, Aka kira Aryan aka gaya mishi an kai har da sadaki, ya ce tow ya gayawa Abdul Majid. Daga nan garinsu Hajiya. Basu bi tanka Amaan ba, suka yi tafiyarsu domin Hajiya ta gaya mishi, ya ce ba zai je ko ina ba, wato Amaan shine matsalar dakin Hajiya munafiki. Duk da uzurin da Hajiya take mishi baya gani.
Chapter 36 · 0% Book details