← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 138

Sashe 20

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu na farko da muka fara fuskanta a camp din, shine rashin matsuguni da kuma kayan amfani, wai a haka dai an kawo mu nan saboda akwai inda zamu zauna, sai dai tunda aka yasar damu a asibitin wanda ba laifi an gwada mana kulawa da duk wani abun da ya dace, sai dai kuma babu wanda ya kuma zuwa da zancen ga yadda zamu yi, kwanan mu goma duk da haka mun samu lafiya daidai gwargwado. Idan ka cire Nenne da Yakumbo lantana da kullum jininsu yake hawa. Ita kan Yakumbo idan ta zauna sai ajiyar zuciya tana kiran sunan Sa'idu. "Ayya ayya akan idanuna suka kashe min shi. Ko tausayin rai basu ji ba, suka kashe min Abubakar yaron da bai gama koshi da nono ba." Sai ta fashe da kuka, ita kan Nenne bata hummm bata hmmm, hasalima tsayuwa mai kyau bata iyawa, domin a bakin Munaisah nake ji wai an mata ɗinki ciki da waje, sakamakon yadda suka mata kaca-kaca. Ashe wani lokacin kuka ma rahama ce, har yau ina son nayi kuka amma ko da wasa ban zubda hawaye ba, sai dai idan na tuna mutuwar Baffa'm sai naji har zuciyata tana wani irin bugawa, can kuma naji kirjina yana min ciwo, dole sai na kwanta. Lokacin da likita yazo na gaya mishi, kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Kina son ki mutu ne da kuruciyarki? Me yasa kike tuna abin da ya faru?" Sunkuyar da kai nayi, ina wasa da yatsun hannuna. "Zan bada test a miki, kada ki sake na ga wani abu domin zan na miki allura kullum." Murmushi nayi nace mishi. "Ni." "Ke ke! Meye?" "Ina son nayi kuka ne?" Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "shi kuka yana zuwa ne idan lokacin bukatar shi yazo, lokaci na zuwa zaki yi kuka kin ji." Gyada mishi kai nayi, ina faɗin. "Nagode!" "Ba kome yar fillo!" Daga haka na fito daga office din, na fita daga cikin asibitin can harabar asibitin na nufa na tsaya ina shakar kamshin ƙasa, domin ina son na samu nutsuwa. Idan nace ina jin dadin rayuwa nayi karya, ko dariyar da nake a dole nake yin shi ba wai yana kaiwa zuciyata ba ne. "Nan kika fito?" Juyawa nayi na kalli Addah ko daga ina take oho. "Hmm!" Nace mata, gyara tsayuwa tayi domin itama har yanzu bata gama jin dadin jikinta ba. "Zahra babu wani abu ne, kin ga saboda Lantana da Matar Babanki anki sallamar mu, balle har mu samu damar barin asibitin nan." Shiru nayi ina nazarin wace irin zuciya ce da Addah haka. "Naji Zulaihah tana cewa akwai wani abu a wurinki." Sai lokacin na samu zarafin mata magana. "Zuzu ba zata gaya miki akwai wani abu a hannuna ba, sai dai idan Munaisah ta gaya miki." Na fadi haka ina kallonta, sai kuma ta fara kame-kame. "Yauwa ashe." "Addah don Allah bana son damuwa, ki je kice ta baki kudin ki kyale ni." "Hmmm! Ai kin san dai zuzunki ba zata tab'a bani wani abu ba." Ta fada tana hararata, na ga karfin hali a wurin Adda. Haka ta taso ni a gaba, har dakin da aka kwantar damu, na nufi wurin Zuzu nace mata. "Bani jakar nan" a hankali ta d'ago kai ta kalle ni, bari na gaya muku wani abu dukar da aka mana ya haifarwa Zuzu rashin ji da kunnenta daya. Bata ji sosai sai ka mata magana da karfi, ni kuma bana son na sabar mata da yawan magana da karfi. "Me zaki yi da shi?" Ta tambaye ni, tana kallon Addah da ta haɗe rai ita kada ma ta sakata a cikin lissafin ita ta turo ni. Itama kuwa Zuzun tawa haɗe rai tayi ta ce da ƙarfi. "Ban san inda yake ba." Tunda ta fadi haka nasan wallahi ba zata bada ba, kuma duk abin da za ayi sai dai ayi amma ba zata tab'a bada jakar ba. "Ai kin ga irinta, waye ya gaya miki ana mu'amala da irin Zulaihah da tana da jin ta ma ya aka kare balle ta rasa jin." Juyawa nayi na kalli Munaisah tana matsa kafar Nenne, Ummi tana kwance gefen Yakumbo. Ni daya ce bani da uwa anan, ita me uwar ma bata samu tausayi da jin kai ba. "Addah lalurar Zuzu ba siya tayi ba, sannan likitocin kwakwala da kunne sun ce zata dawo da jin ta kamar baya, matukar tana amsar magani, me yasa kike mata gorin ji? Idan tausayi da jin kai bai shiga tsakaninku ba, Addah kada tsangwama da hantara ya shiga tsakaninku domin wata rana ita ce zata tsaya miki." Daga haka na koma wurin Munaisah na ce mata. "Ya jikin Nenne?" Idanunta da suka yi bullu-bullu sakamakon kukan da take yi ta ce min. "Jikin Nenne kara zafi yake, gashi yau bakiɗaya bata ko magana." Wani irin tausayi ne ya cika min zuciya, na ce mata. " Bari na je na ga Dr Moses!" Haka na fita, a hanya na hadu da Nurse rabeka, "yar fillo ina zaki?" "Yawwa Aunty Nurse zo ki duba min Mamanmu." Ba musu ta bi bayana har dakin mu, tana shiga ta fara dubata da sauransu. Kallona tayi ta ce min. "Yar fillo bari na kira Dr Moses!" Haka kuwa ta fita can sai ga su tare da wasu likitoci biyu, haka suka dubata sannan suka saka Nurse Rabeka da Nurse Ali suka dauketa a keken marasa lafiya aka fita da ita, haka muka bi bayansu. Har wani wuri can da aka rubuta ICU da manyan harufa. A wurin muka tsaya aka shiga da ita, tunda muka tsaya a wurin Munaisah ta fashe da kuka, kuka take tana faɗin."me yasa? Me yasa sai mu? An kashe mana iyayenmu, anci zarafin mu da iyayenmu, an kona mana dukiyarmu da muhallinmu me yasa gwamnati ta zama makauniya?" Rungumeta nayi, ina buga bayanta. "Zahrah Nenne kawai ta rage min sai ke, Zahrah idan wani abu ya samu Nenne ba zan tab'a yafewa Gwamnatin Nigeria ba, ko ina ka shiga kome mugun aikin da aka yi, zaka ji ance Fulani me yasa aka tsane mu? Kowa yasan bafulani daga kiwo sai sayar da madara yake, amma a yau duk wani aikin ta'addanci zaki ji sunan bafulani ni ne, me yasa Zahrah me muka yi? Zahrah bamu da yanci anan mu da bakin haure daya ne, babu tausayi, babu tausassawa, babu." Rufe mata baki nayi. "Kowane bawa da yadda rayuwa take zuwa mishi, idan muka kalli yadda tazo mana, sai mu amshe ta da hannu bibbiyu, kada mu zama masu son rai, shi Ubangiji bai tab'a jarabtar bawa akan baya sonshi ba, yana jarabtarshi ne gwargwadon karfin imaninshi. Ki cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya.". Wato ko Munaisah yar gata ce, tunda ga Mahaifiyarta a raye, ni fa? Gani a kasar su mahaifiyata, amma ban san ta inda zan fara nemanta ba. Haka na hadiyi tawa damuwar, domin ba lokacin bayyana tawa bace, haka na cigaba da zama da ita, domin Addah bata biyo mu ba, Zulaihah kuwa bata iya tafiya saboda kafarta da aka mata dauri. Ta samu tsagewar kashi, muna zaune a wurin har suka fito, mikewa nayi na nufe su. "Ya jikin Mamanmu?" "Da sauki!" Dr Moses ya faɗa, yana kallon yadda muke raba idanu. "zamu iya ganinta?" Girgiza min kai yayi yana faɗin. "tana ƙarƙashin kulawar computer ne." Sabon kuka Munaisah ta fashe da shi, tana rike kirjinta. "Wayyo Allah na, Wayyo Allah Nennena. Don Allah ku barni na ganta." Girgiza kai yayi yana faɗin. "zaku kanta amma ba yanzu ba, sai ko zuwa gobe." Rufe bakina nayi, cikin rudani ina kallonshi. Ita kuwa Munaisah kuka take me tab'a rai, baki ɗaya na rasa ina zan saka kaina. "Yar fillo kada ki damu fa, zata ji sauki kawai an dora ta akan kulawar computer ne, ki cewa Fulani ta daina kuka haka. Nenne zata ji sauki." Gyada kai nayi, ina kallon Munaisah, haka suka tafi suka bar mu a wurin. Dakyar naja ta muka koma dakinmu, sallah muka yi. Abincin da ake rabawa na asibitin aka kawo mana, ban iya cin ko loma daya ba, haka Munaisah itama bata iya ci ba. Muna idar da sallar Isha, na mike xan fita Munaisah ma ta biyo ni haka Zulaihah ma ta ce mana. "Ku jira ni." Ummi da take jikin Yakumbo ta ce mana. "Zahrah akwai maganar da Yakumbo tace zata gaya miki don Allah." Kallonsu Zuzu nayi nace musu. "Kuje ina zuwa." Zuwa nayi na zauna a gefen Yakumbo. "Gani Yakumbo!" "Zahra'u!" "Na'am!" Ga Ummi nan na baki amanarta. Ta shiga lallubar hannuna, kallon Ummi nayi da ta dauke kai, tana share hawayen da yake zuba mata. "Sis yaushe yakumbo ta daina gani." Murmushin karfin hali tayi ta ce min. "Zahra'u, don Allah ki taimaka min ki maida Ummi Yola wurin Dan Malam, ina tsoron kada na mutu rayuwar Ummi ta lalace." Wato sai na rasa ya zan kwatanta halin da nake ciki, shin zan fadi ne na mutu ko kuma zan fita ne nace a bude zuciyata a ciro min shi a rage damuwar mutane da yake cike a bar min tawa. Ajiyar zuciya na sauke sannan na rike hannunta. "In sha Allah, zan cika alkawarin da na daukar miki." Itama rike hannuna tayi da kyau ta ce min "Ki yafewa Nenne, don Allah ki yafe mana, don Allah ki yafe mana ko zamu samu rahamar Allah." A wannan lokacin ina son nayi kuka ko zan rage nauyin da yake zuciyata, amma ina zuciyata sai kara zafi take tana kara taurarewa, ina ga ba mamaki an sauya min zuciyata daga tsoka zuwa dutse. A hankali na zubawa Yakumbo idanu. "Duk abinda ya wuce ya wuce abar shi har a wurin Ubangiji ya wuce." Na fada ina kokarin barin dakin, "Kina nufin kin yafe mana?" "Har a gaban Ubangiji bana fatar haka ya tsayar damu a kan wannan abin, na yafe maku." "Ki bari na gaya miki abin da muka aikata mana!" Juyawa nayi na koma wurinta, na saka hannu na rufe mata bakinta. "Nace na yafe, kuma ko kin gaya min ba zai sauya kome ba, sai ma lalata kome da zai yi. Ina fatan nima Ubangiji ya yafe min laifin da nayi
Chapter 20 · 0% Book details