← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 138

Sashe 134

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka nake na tausayin yadda zai ta magana shi daya kafin naji na bashi amsa, kukan yadda Alfah zata yi ta jin haushi idan tayi magana ban amsa mata ba, kukan yadda al'umma zata yi ta kallona a nakashe. "Ya isa haka Matar arziki." Ya faɗa tare da niman wuri ya zauna sannan ya ajiye ni kusa da shi, Alfah tana zaune a cinyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon kowa a falon. "Sannu ku da zullumin b'atar da nayi, ko nace sace ni da suka yi." Sai da ya sauke numfashi ya bude gefen cikinshi dinki ne kato, ya ce mana. "Wannan shi ne abin da suka fara min bayan na shiga hannunsu, wuka aka soka min sai da ya fito ta bayana. Baffa Haladu ya mon wannan aikin a ranar da suka dauke ni."

Kallon Amaan yayi ya cigaba da cewa. "Sun nime Amaan ya kashe yan gidan ko su kashe shi, amma bawan Allah nan ya ce musu sai dai su kashe shi dama shi bai da wani amfani tunda ba amfani zai yi ba, yau fari gobe tsumma, daga nan sun san yadda muke da Aryan basu tab'a tuntubar shi ba, sai da suka saka ya bada motar ta hanyar maganin da ake amsa a hannun Sajjid ina yiwa Amaan. Haka suka cigaba da barazana ga yan uwana, basu tab'a min barazana ba, sai ranar da suka kama turawan nan....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:48] Hlm: BHB277
A ranar suka turo min da sakon na kawo kaina, ko kuma su kashe turawan. Duk yadda na shirya su faɗa tarkona abin ya ci tura, sannan suka tabbatar min asibitin da nake kai Zahra waye ya san iya adadin mutanen da suke cikin asibitin wanda nasu ne. Ga yan uwana ga matar da nake aure, taya zan bar wani ya cutar min da abin da yake cikinta bayan yadda ta kwallafa rai a kan cikinta. Shi yasa na zabi tafiya na basu rayuwata don na tambaye su idan wani abu suke so zan basu har dukiyar da nake da ita, suka gaya min su rayuwata kawai suke bukata. Ya zan yi? Zan ce ina son rayuwata ne don na rayu Dangina kowa ya mutu? Idan na tuna na bar Zahra da ciki sai na ga kamar zata kuma haihuwar wani Yaron da zai zama kamar ni, nasan Zahra zata kula da Hajiya zata kula da kowa, sannan zata bawa kowa farincikin da ya dace.

Haka yasa na tafi, tsawon lokacin da aka dauka ana nima na, an rigada an shigo dani nijar, duk abinda ake suna kallon kowa. Har haihuwar Alfah sai da aka kawo min labarin. " Shiru yayi cikin takaici da damuwa kafin ya cigaba da cewa. "Iya zaman da nayi nasan yadda Zahra take da kwazo, nayi addu'a Allah yasa Zahra ta san inda ma ajiyar bayanan komai.

Amma ina zaune shekara daya ya wuce aka kawo min hoton Alfah, da ta cika shekaru biyu ma haka, tun da aka shiga na uku na fahimci cewa koda na mutu ahalina suna cikin nutsuwa da Amincin Allah. Ban kawo Zahra zata zo nima na ba, sai a daren da suka gaya min an rufe kamfani kuma nasan duk ranar da aka rufe tow nima na za ayi, ko kuma sun san inda nake." A hankali ya cigaba da gaya mana abubuwan al'ajabi, wanda muka sani da wanda bamu sani ba, da dalilin shi na tafiya Algers jinya, duk da na ji dadi amma kuma maganar da Anisah tayi yasa kowa ya shiga damuwa, musamman ni da na san yadda nayi na sulale a falon.
"Ai yanzu kan sai kayi hakuri,amma zama da kurma ba sauki kana maganar sirri na waje na jin ka, idan kuma ka samu lafiya kana da halin kara aure."
" Ke me yasa naki mijin da zai kara aure baki yi hakurin zama ba? Alhamdulillahi ita ko yanzu yakara aure ba zai samu mace irin Zahra ba, ba karya ba ne mu abin a cikin jininmu na Fulani yake, hakurinmu da kawaici yasa duk buzaye suka kanenaye rayuwarmu, don sun fahimci baya gamu babu wata mace me iya shanye ƙaddarar mijinta." Inji Benazir, ta mike tare da nufar hanyar da Zahrah ta bi. "Allah ya kyauta, ana sara ana duban bakin gatari." Inji Maimuna. Ta bi bayan Benazir, ina zaune a bakin gadona naga Benazir ta shigo. Kallonta nayi ina murmushi. Zama tayi tana kallona. "Kiyi hakuri!" Murmushi nayi ina faɗin. "Kai ba kome jarabawa ta ce"
"Koma dai me nene kiyi hakuri." Ta rike hannuna tana faɗin. "kin yi nasarar, zama a zuciyarshi babu macen da zata samu gurbin zama a ranshi bayan ke, amma kada laifin wasu ya shafe shi."
Shigowar Maimuna yasa ni kallonta. Itama aka baje hirar a kitchen dina nayi musu girki ko nace muka yi, baki daya. Sakin baki Maimuna take ita da Beenazir, "Kin shiga makarantar koyan girki ne?"
Dariya nayi tare da faɗin. "mun yi sana'ar tuwo -tuwo." Na juye denderun kazar da muka yi, jollop din taliya ce sai tuwon semo miyar kuka, aka yi ta fita da shi. Miyar kukan da taji namar rago da kayan kamshi.
Kunun aya da tsumi da yaji kayan kamshi, haka muka yi ta fita da shi, ana gamawa muka shiga daki, na samu sun ciro min kayan da zan saka. Nayi wanka na fito Beenazir ta gyara min fuska da kwalliya light, sannan na shirya suma na cire musu sababin kayan aurena, musamman abayar. Suka saka bayan sun shirya muka fito tare, muka samu yar iskar mara kunya tana tsaye Hajiya ta hanata tab'a kayan abincin don shegiya sai ta ce zata tab'a.
Haka muka yi serving din kowa sai lokacin na fahimci baya falon, "Zahrah ki zuba mishi zuwa dakinshi." Inji Dean ɗinmu, kunya ce ta kama ni Maimunari ta hada kome ta mika min, na haura sama. Na kai mishi ya fito wanka yana goge gashin kanshi ga Alfah akan gadon shi tana wasa da tap ɗin shi. Kallonta nayi na ajiye kayan na dauke ta tare da kunna mata wakar Bunny. Na ce mata. "Love maza kaiwa hajiya da Nana su kunna miki."
"Da intafi!"
Kallonmu yayi ina jiran naji me zai ce sai zuwa yayi daidai bayana, ya ce mata." Ki je ina zuwa!" Da gudu ta fita, kasa d'agowa nayi. Yana kuma tsaye a hankali na d'ago bayana yana gogan nashi, yarrrrr naji abu yana yawo a jikina. Jin hannunshi nayi a saman cikina tare da cewa. "Ayi hakuri!" Haɗiye yawu nayi, tare da janye jikina ina rarraba idanu.
"Ga abincinka nan!" Na fada xan fita, riko hannuna yayi tare da dawo dani ya rungume ni. "Ki kalle ni mana."
A hankali na zame jikina na bar shi tsaye, a wurin cike da tarin mamaki na, na dawo dakina. Zama nayi hawaye na zuba min me zafi har wani lokaci kafin na tashi zan shiga ban daki ya shigo, kallon juna muka yi.
Ajiye abincin yayi yazo ya zauna kusa dani. "Yunwa nake ji." Ya faɗa yana kallon yadda nake ƙoƙarin kauda kaina. "Baki yi farincikin dawowata ba ko?" Shiru nayi ban ce kome ba, sa ke magana yayi na kalli bakinshi kafin na juya da kunnen da nake ji na ce mishi "ka faɗa min me kace?" Na fada da karfi. Juyawa nayi naga yana kallona Idanunshi jajjur. "Zahrah baki ji ne da kunne ɗaya." Murmushi nayi ina wasa da yatsun hannuna. Abin da nake son ya fahimta kenan kuma ya fahimta, fita yayi daga dakin na bishi da idanun, ban kuma futa ba sai da su Maimuna suka zo min sallama, muka fita na raka su bayan na sake diba musu kaya a cikin laida, Mami sai fada take min bakya gajiya ne ga sabon abayar ga kaya kuma, murmushi nayi nace mata. "Idan ba naka ba waye zaka yiwa hidima baka gaji ba ai sai naka."
"Allah ya zaunar da ku lafiya!"
Murmushi nayi ina faɗin "Amin" bayan tafiyarsu na koma cikin gida muka baje dasu Baraka muka ci abinci. "Maman Amirah, ina son zuwa gida Zainabu ta haihu." "Me ta samu?" "mace yarinyar nan ta cika haihuwa, fisabilillahi Aunty tasan." Dakuwa nayi mata, ina faɗin. "Kaniyarki kema baki fi karfin Allah ya jarabce ki ba, don ta haihu sai ta zama me laifi."
Tura baki tayi tana faɗin. "Allah laifina kike gani kawai."
Girgiza kai nayi ina kallonta, Baraka ta zame min wata sanyin idaniyar, a duk lokacin da na kalleta sai naji ina kara kaunarta, shi yasa nake burin Yazid ya aure ta ita da iyayenta su fita a rayuwar da suke ciki duk da suna da rufin asiri, Baban yana aiki a kamfanin Mahdi mijin Munaisah.

Bayan sati guda baki ta ko ina sai zuwa suke har da Zaytoona da yaranta biyu, Ummi da ta kusan aure itama tazo, Munaisah da nata Yaron, Zuzu na ma haka farinciki iya farin ciki. Muna cikin wannan farin cikin Mutumin da xai auri Ummi ya kira ya gaya mata ya fasa yaji ance ta tab'a karuwanci a baya, tayi kuka nayi kuka dukkanmu mun yi kuka,, shi yasa nace ta zauna da mu anan babu amfanin zuwa Nigeria kada ta zama abin nunawa.

Addah yadda zuzu take gaya min, ta koma kamar wata halitta. Amma bakinta yana nan radau kamar ba ita bace a nad'e. Zuwan Malamijo da Alhaji Abubakar Abzin, yasa gidan ya kara cika. Allah yaso tunda ya dawo babu abinda ya tab'a hadamu zuwan dattawan nan da Ya Babangida,aka sake daura aurena da Majid, tunda a shari'ance yana kasar kuma yana sane da ya sake ni ne da sauki amma Nima ban yi wani auren ba, wanda ba a san inda yake bane da ya shekara hudu babu aure, amma yana raye ina raye kuma yana kusa damu a Muslunce wata hudu ya dace a kashe auren. Daura auren ya yayyafa wutar da yake cin ran Mama sannan kiri-kiri ta saka ni a gaba muka bar nijar, wai ta tafi yi min jinya ai shima da ya tsallaka ya tafi bai yi tunanina ba.
Chapter 134 · 0% Book details