Sashe 7
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*004*
*Captain*
Juyawa yayi ya kalli Magaji Abba Chindo da yake mishi dariya, idan ya sake suka yi faɗa. Tow yau ba zai iya samun nutsuwa ba, don haka ya saki dan ƙaramin murmushi ya ce mishi. "Sai a ka yi rashin dace, ni mata-maza, bana haɗa jikina da yan maza, musamman waɗanda basu dauki aikata sabo illa ba." Daga haka ya juya abinshi, shiru wurin ya ɗauka, abin ya bawa Magaji Abba Chindo dariya, amma da ya nutsu sai ya fahimci da gaske Captain magana ya gaya mishi. Mikewa yayi zuwa ciki jirgin don da suna daga waje ne.
"Kai magana ka gaya min?"
Murmushi Captain ya yi sannan ya ce mishi.
"Kaga ni bana son tashin hankali, kayi hakuri ba magana na gaya maka ba." Kurawa juna ido suka yi, sannan ya fauce Map din hannun Captain ya yaga gida biyu.
"Naga yadda...!" Kafin ya rufe baki Captain ya zabga mishi marin da sai da ya daina gani. D'ago shi yayi ya ce mishi. "Kada ka sake wani yaji wannan labarin domin zai maka dariya, kada ka kuma aikata abin da kayi. Ni idan kaci zarafina zan yafe maka. Amma idan ka taba aikina zan baka sakamakon da yafi haka. " Wato marin nan, ya shiga Magaji domin kuwa hakorin shi na wannan bangaren har yana girgiza.
Sauran matuka jirgin duk hankalinsu na kan aikinsu, babu ruwan su kuma haka da Captain yayi shi ne zaman lafiya, don haka, A hankali ya juya tare da fita daga dakin, Captain ya gyara takardan, bayan Mr Oke ya mika mishi salatep, ya gyara suna hira sama sama.
Lokacin sallah yana yi suka fita baki ɗaya, musamman Domin a yi sallah wanda Captain ne ya jasu, sannan aka ɗauko abinci da wasu daga cikin sojojin suka dafa, mika mishi aka yi ya kalli agogon ya ce musu. " Na koshi!" Haka suka kyale shi, ya tashi tare da ɗaukar abin hango wasu abubuwan, yana me duba gabansu.
Komawa ciki yayi ya dauki wata waya,ya shiga duba sakon.
_Sir mutanen nan basa gudanar da kome sai dare yayi,hankalin kowa ya koma tsoron dare. Kada ku shigo da rana domin zasu gudu_ mai da wayar yayi ya ajiye, taya zai yi facing Commodore? Haka ya daure ya fita ya zauna a gabanshi.
"Yallabai!" Cikin wani irin yanayi Commodore yake kallon Captain kamar ya shake dan banza amma yanzu ya fahimci gayen ya wuce tunaninshi. Mari daya yayi mishi, hakorinshi yake girgiza ina kuma da sun daku, tow kuwa kareraya shi zai yi ya tara dan iska a gefe kenan? "Meye?" "Inda zamu shiga basa kome da rana, sai dare."
"Tow me kake so nayi?" Ya faɗa yana nad'e hannunshi a kirji. "Ina ga a tsaya nan, sai mu duba nisan kafar ruwan, idan nisan ba yawa sai muyi musu shigar dare."
"A matsayinka na wa?" A hankali yayi kasa da kanshi kafin ya ce. "A matsayina na soja, kuma shugaban rukunin sojojin da suke aikin sirri, mataimakin ka. Na bada shawara kuma na fita." Ya faɗa yana me mikewa daga gaban Magaji ya nufi dakin iko. Jikin Magaji ne yayi sanyi, kudirinshi shine a kashe Captain a wannan lokacin, kuma ba zai fasa ba.
Don haka ya mike tare da fito da sabon tsarin da ya sauya, a ka'idar zuwansu nan. Shi ne shi zai jagoranci wasu daga cikin Yaranshi su isa har inda ake zaton abin, amma son zuciya irin nashi, sai ya kalli Captain ya ce mishi. "Kai da team dinka zaku tafi inda ake badakalar, ni da team dina zamu zauna a nan. Domin ba za a rasa wanda zai iya kawo farmaki ba, idan kuma ba a samu ba kunyi nasara, ga fireworks sai ku sanar da mu."
"Amma Sir wannan abin babu tsari, taya kana shugaban sojojin kuma kace Captain zai jagoranci wasu daga cikin mu, kuma mutumin da bai tab'a rike bindiga ba, aikinshi kawai sanin meke faruwa."
"Shi namiji ne, idan har ya cika namiji ya jagorancin tafiyar."
"Na amince " ya faɗa tare da ware wasu daga team ɗinshi. "Zamu tafi in sha Allah hakkina ne, na bawa rayuwarku kariya,ku yarda da ni in sha Allah zan mai daku cikin iyalanku lafiya."
"Mun amince " suka fada, sannan ya shiga musu bayani tare da tara su a cikin wurin tukin jirgin, yana nuna musu yadda tafiyar zata kasance.
***
Addah
Kallon Addah mutumin yayi ya ce mata. "Ki kula da zuciyarki kada ki aikata abin da zai dame ki, ita yarinyar babu ruwanta." Kasa magana tayi can ta daure ta ce mishi.
"Yanzu haka 'yata zata kasance? Babu wani cigaban rayuwa sai ta karuwanci? Karshenta."
"Ba farinciki da nutsuwa ake nima ba?" Ya tambayeta yana gyara zaman wandonshi, domin yana matukar jin dadi Adda tana cikin mata na musamman da yake mu'amala da su. Murmushi yayi yana faɗin, " A gaskiya bakya tsufa " dauke kai tayi ta gyara jikinta, sannan ta dauki jakarta ta bar dakin, tana fita waje ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wata iriyar tsanar Zahra. Duk inda zata aiki akan zahrah sai ta bada kanta bata san me yasa haka ba, yarinyar ta shiga ruyuwarta ita da take tutiyar ta samu hannun jari, ashe bala'i ta daukowa kanta.
Hadiye bakinciki tayi ta shiga kasuwa tayi sayayya. Sannan ta dawo gida ta mikawa Ummi wata leda, ta ce mata. "Ki girka mata wake da hantar mu kai mata asibiti!" "Tow ai basu bamu kati ba" "eh idan kuka isa ku kira Zulaihah."
"Hmmm!" Inji Munaisah, ta cigaba da gyaran farcenta, domin tana son zuwa saloon a mata fixing farce. "ina son zuwa saloon dai, domin farce na da kaina yayi datti." Da Ace Munaisah ta san halin da Adda take ciki ba zata fara fadar ita zata saloon ba, dauke idanun tai kanta ta wuce ɗakinta. Sai da tayi wanka ta cire roban condom din mata ta wurga cikin masai din, sannan ta wanke gabanta tass. Sannan ta gyara ta fito, Adda ta san darajar gyaran jiki, shi yasa take gyara jikinta. Duk da abin da take yi be dace ba, amma kuma ita ta dauki haka a matsayin wata hanya ta samun kudi cikin sauki,
Aiki take amma a zahirin gaskiya gangan jikinta ke jagorantar aikin, amma zuciyarta da kwakwalwarta basa bata haɗin kai, baki daya ta kashe rayuwarta domin yau ta samu riba, tana son ace yau ta zama wata hamshakiya, amma wani ikon Allah rayuwarta da na Yarta ne a lalace, wanda take ganin ta maida ita baya an gaya mata ba zata iya kome da ƙaddarar ta ba, "hmmm!" Ta fada tana kallon tilin kayan da ta sauke daga wardrobe ɗinta, tana mamakin me yasa meta da wannan aikin? Lallai ya kamata ta mike wannan lamarin sai kace an saka mata hannu. Jin muryar yan matan da suke mata aikin abinci suka shigo gidan yasakata mikewa