← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 138

Sashe 103

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Can nake ji kamar ana min rad'a, ga wani kararrawan da nake jin yana bugawa a kaina. Bude idanu nayi ina kokarin tashi na ga Yazid da Chairman ne, kamar zasu cinye juna. A hankali jina ya dawo daidai. "Kai baka isa ba" inji Yazid, "Na isa domin aiki za a mata." Inji Chairman. "Waye zai ayiwa aikin?" Na fada a hankali, kallona suka yi ganin ina kallonsu. "Zahrah!!!" Suka kira suna na lokaci guda. "Kin farka." Yazid ya faɗa, kokarin tashi nake amma Chairman ya ce min. "Koma ki kwanta na duba ki." "Ya zaka ce haka, ta farka zata tashi." Inji Yazid, "A kan aikina nake, idan ka shiga rayuwarta ce a hatsari, daga farkawar ta ba a bukatar ta zauna sai mun duba lafiyarta."
A hankali yake aikin shi yana tambayata ina bashi amsa, kafin ya zare na'urar da suke kaina, ya ce min. "Kanki yana miki ciwo?" "A'a da dai dazun na ji kan kamar ana buga min kararrawa?"
"Ok yanzu fa?"
"Babu?" A hankali ya wuce ya bude min labule da window ɗinkin iska me dad'i da sanyi ya shigo dakin. "Ki kula da kanki, za a kawo abinci da magani ki sha akan lokaci." Fita yayi daga dakin. "Ya jikin naki?""Da sauki," na fada dama can Umaima tunda suka fara ta bar dakin tayi tayi su rabu sun ki.
Abinci aka kawo min na ci a hankali, na sha magani, sannan nurse biyu da Aunty Umaimah suka taimaka min nayi wanka da sallah.
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB255
Alhamdulilahi sauki yana ta samuwa, domin kuwa har asibitin sau biyu Nana tana zuwa, idan tazo babu abin da take bani sai labarin Rayuwar Majid da Hajiya, ni dai ban tambaye ta ba, kuma bana jin akwai wani abu da yake tsakaninmu da ya wuce aikin kamfani. Amaan a asibitin yake wuni haka ma Aryan yana zuwa akai-akai don kawai muyi hira, haka Hajiya tazo ita da Zaytoonah. Sai dai daga yadda take min kallon kamar taga abin kyama yasa ni fahimtar saboda mazan gidansu ne, ba laifi Hajiya tayi min alkhairi kuma a duk zuwanta sai tazo min da abinci, haka yasa nake jin dadin haka. Sai dai kuma akwai wani abu da nake fahimta daga gare ta. Wanda iya fahimta ta ce ban san me ye ba, sai bayan da aka sallame ni mutane sun yi sauki tazo har gidan.
Ni da Baraka muka yi ta mata hidima, kafin ta ce min. "Ya isa haka." Dawowa nayi na zauna, tana murmushi ta ce min. "Wani abu nake so na sani."
"Akwai alaƙar soyayya ne a tsakaninku da Abdul Majid?" Girgixa mata kai nayi, ajiyar zuciya na sauke, kafin na ce mata. "Babu!"
"Kece kika haifi Amirah?" A wannan karon tambayar tayi min tsauri, bakiɗaya sai na rud'e, bakina yana rawa na ce mata. "Eh...a!" "Eh ko a'a!" Yadda ta tsare ni da idanun na samu kaina da cewa. "Eh!" "Waye ubanta? Ko Majid ne?" Wani irin rawa jikina ya dauka, na kasa bata wannan amsar. "Umaima ta gaya mana, cewa Majid ya kai ki wurinta tayi miki jinya?"
"Waye Majid Hajiya?" Na tambaye ta ina daura hannuna a baki. "Barikin sojan sama na Fatakwal sojan da ya dauke ki awannan daren Majid ne ko?" Kamar an buga min guduma haka naji kalaman Hajiya, sake rudewa nayi kamar xan tashi zaune na ce mata. "Chairman Majid shine sojan....."
"Eh soja ne, kafin ya ajiye aikinsa ya rike kamfanin mu. Meye alakarku? Amirah yar shi ce?" Wasu irin hawaye ne ya shiga zuba min ina jin kamar na haɗiye zuciyata na huta. "Yar shi ce ko." "Ba yarshi ba ce." Na bata amsa cikin wani irin kuka. "Zata kuma magana nayi maza na ce mata. "Hajiya ya isa haka, babu wani alaka a tsakanina da shi sai na aiki bayan nan ban san kome akan shi ba, idan akwai bukatar na ajiye aikin kamfahinku ma zan ajiye amma don Allah kada haka yasa ku sheganta min Yarinyata." Daga haka na bar falon zuwa dakina, har bakin kofar ta iso. "Ba zan sheganta miki Y'a ba Zahra amma ina son sanin wacece ke? Sannan meye alakarku da Yazid, ni uwa ce da take kokarin tsayawa d'anta, nazo nan ne domin nima Majid soyayyarki ba nazo na cutar dake ba ne, amma kiyi hakuri. Ban san yadda zuri'ata zata yi alfahari dani ba, amma macen da aka ciyota a caca bata cancanci tayi farinciki ba ne? Ko macen da aka samota a bariki bata dace da farinciki ba ne. Bana son tarihi ya maimaita kanshi ne." Ni dai ina dakin a bakin gado, kuka nake mara sauti Hajiya kuwa tana ta magana ne, har na daina jin maganarta na fito na samu ta ajiye min karamar takarda.
_Kiyi hakuri amma ina son kiyi farinciki ne bana son daga baya kiyi kuka da ni. Ina tsoron kada shigowar ki zuriyarta a sake samun wata victim._
Yaga takardan nayi abuna, lokacin da Yazid ya zo ya so ya gano wani abu amma naki, kwanan shi goma sha daya ya koma garinsu. Nima sai da nayi sati Uku na koma wurin aikina.
A lokacin dayawa sun min ya jiki,wani abu da na kara fahimta, shine kusancina da Chairman. Yanzu ba karamin kulawa yake ba ni ba, ina zaune zai min odar abinci. Wani lokaci kuma zai Ajiye aikin ya ce min. "Zo muje wani aikin." Muna fita gidan cin abinci ne, tun kafin mu shiga zai saka a sallame kowa. Haka yasa bakiɗaya nake jina a takure.
A wannan takin ne akazo aka yi ta kama wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin ana sallamarsu. Koda yake zan iya cewa ta wani fuskar da sauki wasu abubuwan.
Ranar da ya ishe ni da kinibibi ne, ina aiki kawai ya fito da keyn mota. "Zo ki raka ni?"
"Babu inda zani ina aiki." "Ba jimawa zamu yi ba." "Na ce ba xan je ba Please." "Na mana odar abinci?" "Bana bukata!" Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Ok me kike so?" Ajiye aikin nayi kafin na ce mishi. "Don Allah ka rabu da ni." Kamar haka bai mishi dad'i ba ya ce min. "Na bata miki rai ne?"
"Nace maka don Allah."
"Tow shi kenan " ya faɗa tare da fita, bayan kamar minti ashirin, sai ga shi ma'aikata na ta fita, "lafiya dan Larai." "Wai yau an dakatar da aiki ne sai gobe."
Tashi nayi ina ajiye aikin, na fita nima tare da jakata. Ina jin wani irin dadi da nutsuwa. "Zamu iya fita yanzu?" Ganin mutane basu gama barin kamfanin ba, yasa ban tsinka shi a gabansu ba. Don haka na yi banza da shi muka fito na shiga motar. "Gida zaka kai ni." "Ok Madame Zahrah." Daga haka muka wuce zuwa gidan, sai so yake ya min magana amma naki, muna isa gida na wuce ciki shi ma ya biyo ni. Daki na wuce na zauna tare da ɗaukar wayata, kiran Sk Lamido na gani na dauka muka fara magana da shi, kafin na fito na samu yana wasa da Amirah, mika mata waya nayi. "Ga Daady!" ai kuwa ta amsa tana murna. Kallon shi nayi ina faɗin. "Me yasa baka tafi ba?"
"Ina jiranki ne ki bani abinci."
"Ni ce xan baka abinci na baka guba? Ko ka manta irin kallon da kake min ne?" Na tambaye shi ina tsare gida, "eh ko yanzu a bani gubar zan ci. Idan na mutu a hannunki ba zan yi bakinciki ba tunda nasan a wurin Khamila na mutu." Sake hade rai nayi kafin nace mishi. "Gobe kace muna da tafiya zuwa damagaram ko? Amma meye ya kawo wannan abin kuma?" Mikewa yayi yana faɗin. "Tow Allah ya kai mu goben."
Dauke kai nayi tare da wuce shi har zai fita na ce mishi. "Idan ka kuma zuwa gidana ka zauna ba da iznina ba, zamu samu matsala."
Murmushi yayi ya fita yana faɗin. "Tow Ma!" Ya fita, babban burin shi ganinta cikin farinciki yafi komai yi mi shi dadi, yarinyar da ya jima yana fatan gani ashe ita ce yake ta zubawa tijara..
Chapter 103 · 0% Book details